← Book details Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 76

Sashe 70

Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_“yarana kuyi hak'uri da damuwar da kuka tsinci kanku a ciki, wadda tunkafin Ku mahaifiyarku a ciki take, amma nasan watan watarana kuda ita duksai kunci ribar wannan hak'urin, karkuyi bak'inciki akan hanaku wannan auren da akayi na y'ay'an halluru, dama can sud'in ba mazajenku baneba, hasalima aurensu ba alkairi baneba”._. “A razane duk muka kallesa baki bud'e”. Yayi murmushinsu na manya, _“abin ya baku mamaki ko? Humm ba abin mamaki baneba, yau zan fad'a muku wani sirrin dabaku saniba, domin ina hango wani tarin alkairi tattare da rayuwarku, inakuma ji ajikina kune wad'anda zaku fidda mahaifinku daga wata sark'ak'iya daya Shiga a dalilin taimako tun kafin a haifeku. Alhaji halluru da wata manufa ya nema ma y'ay'ansa auren d'iyan mahaifinku, amma Shifa na fuskanci bai fahimci hakanba, sabo da ya aminta da amintar dake tsakaninsu ta tsawon shekaru. Alhaji halluru yanason shiga jikin mahaifinku ne sosai danya kar6ama iyayen gidansa wani sirri dake hannun Auwalu, ina k'yautata zaton shine kukaji wani Abu a ciki, shi kansa Auwalu baisan minene a ciki ba, domin kuwa bashi akai amana ya Isar dashi ga Wanda yadace, kuma baita6a yunk'urin ya duba ba ya barsa a yanda aka bashi. Kuyi hak'uri akwai wasu k'alubale dake tunkaro rayuwarku, kuma yanada tsananin sark'ak'iya, saidai insha ALLAH zan baku dikkan gudunmawa inhar ALLAH yabani tsawon ran kaiwa wannan lokacin, Ku dage da yawan sadaka kudai da mik'a lamuranku ga ALLAH mai kowa da da sirrin komai, ALLAH kuma ya cigaba da tsareku.”_ “duk cikin tsantsar damuwa muka amsa masa da amin, haka muka baro gidan jikinmu duk a sanyaye, dan har innarmu tata bincikarmu a lokacin, sai muka fake da ciwon mara. sati biyu da faruwar wannan lamari sai Munubiya tafara min k'orafin yawaita mafarkin wani bawan ALLAH, kullum takan gansa ne a cikin dokar daji zagaye da wasu irin halittu masu ban tsoro suna kaimasa hari zasu halakashi, yakanyi k'ok'arin kare kansa amma saiya gaza, idan yanemi taimakonta kuma bata zuwa, saboda tsoro suke bata. Duk sanda tafad'amin wannan mafarki sainace bata addu'a ne, shaid'anune kawai. haka taita jera wannan mafarki kullum dare, kuma da gari ya waye bazata fasa fad'aminba, tundai abin na damunmu har muka watsar muka cigaba da harkokinmu. Ranar kuma sai nima nayi mafarkin makamancin na Munubiya, saidai nikuma na shige ina taya wannan mutumin kare kansa ga wad'annan halittun kamar yanda ya buk'ata, na jigata sosai dan harnatashi jikina duk yayi week, nima ban 6oyema Munubiya komaiba na sanar mata, abin yabata mamaki, kuma tundaga sannan nima na cigaba da mafarkin, kullum kuma ina taimakon wannan mutumin dako fuskarsa ban ta6a ganiba, itako Munubiya takan cemin saidai ta tsaya kallonsa daga nesa yana bata tausayi, kuma yana shan nuna mata tazo ta taimakesa, amma saitak'i ta nok'e kafad'a. nikam a nawa mafarkin duk lokacin da ya nuna na taimakesa nakanje nashiga muyita fama da wad'annan halittu, ita Munubiya tana ganin fuskarsa, amma da zaran ta tashi, saita manta, niko ban ta6a ganin fuskarsa ba ko sau d'aya. Muna cikin halin wannan mafarki ne aka shiga bikin salla, tabbas randa muka had'u dakai a asibiti sainaita jin haushinka akan dalilin da ni kaina nasan bai isa daliliba, (dan kawai ina maka kallon mai girman kai bai kamata naji haushinka ba, tunda bawai hud'ace ta had'amuba, banikuma da tabbacin akanka abbanmu ke a had'ari), saidai had'uwarmu ta filin idi tasha banban data asibiti, dan a filin idi tsoro-tsoro mai gauraye da mamakinka ne suka zaunemin a zuciya, bayan kabani wayarka kabar wajen inata mamaki da juyata da tambayar kaina kaid'in wanene? Sai wata murya ta bani amsa da cewar *Galadima!* saidai koda na waigo banga kowaba sai alamar gittawar mutum mai jajayen kaya, na dad'e soaai wannan al'amiri bai bar rainaba, a haka muka shiga shagalin bikin y'an gidanmu, harda kuma su siyama, anan ne muka had'u da Fu'ad, harga ALLAH bansan wanene Fu'ad ba, bankuma San daga wace tawagar ango ya fitoba, amma amamakin kaina lokaci d'aya na aminta dashi, dukda kasancewata mutum mai masifar tsarta, cikin kwana d'aya kacal na saki jiki dashi, dukda ban amsa masa Cewar na kar6i soyayyarsa ba, daga ni harsu Ayusher bansan miya shiga kanmu ba muka yarda ya kaimu birnin gayu plaza ba, dukda kowannenmu ransa akwai fargaba, musamman ni danakeji kamar akwai wani gagarumin Abu dake tunkaro rayuwata. hardai muka shiga muka fito abinda ya faru ya faru a tsorace nake. fitowar wannan jarida a washegari yasaka dukkan wani ahalinmu a rud'ani, Wanda bansan yazan musalta makashi ka fahimtaba, lokaci d'aya da akazo bincikar wacece a cikinmu na amsa, dan jinai bazan iya bari Munubiya ta amsa laifinba, saboda tanada hak'uri, amma tanada tsauri Wanda nikad'ai da mahaifiyarmu muka San wannan tsaurin nata, dan sometimes takanyi mugunta amma tayi tamkar ba ita baceba, kai tsayema sai'a zargeni ita ba'ayi tunanin zata iyaba....” Galadima ya katseta da fad'in, “kina nufin bakece kika kusa fad'iwaba a plaza?”. Nad'an murmusa ina gyaran mayafina dake zamowa saboda kayan sunada santsi, “tabbas bani baceba yalla6ai, Munubiya ce, tausayi. Y'ar uwata yasani kar6ar laifin. Bayan wannan Abu ya faru nanma kowa yata fushi damu musamman Abbanmu, haryace saina nemo miji cikin 2weeks kacal, wannan ya d'agamin hankali, dan nikam kaf samarina babu Wanda yamin, amma sainaga kamar zan iya auren Fu'ad, wannan dalilin yasani kiransa bisa shawarar su feena, amma saiya toshe sukkan hanyar dazamu iya yin magana. bansan yazan misalta maka halin dana tsinci kaina a tsakaninba, naji natsani Fu'ad matuk'a, a wannan time d'inma na cigaba da wancan mafarkin, amma yazomin dawani sabon salo, sannan ita kuma Munubiya ta daina, mafarkin ya canjane zuwa salon da mutumin kanyi yunk'urin ta6ani, amma nakan hanashi damar hakan ta hanyar ja baya da masa gargad'i, shikuma saiya ringa rok'ona da cemin karna masa haka, ni fitilarsa ce. Har sannan kuma still bana ganin fuskarsa, abubuwa da yawa sun had'u sun dagulemin, dukna fige na fice hayyacina. A lokacin da baba mai kanwa yaje dubani asibiti bayan maganar aurenmu da haidar ta rushe saiyake magana cikin murmushi, k'asa-k'asa kuma ta yanda wani bazai jimu ba”. _“Ki kwantar da hankalinki Hussaina, har yanzu dai mijinki bai kai ga zuwaba, kuma bayan wannan ko 10 zasu k'ara zuwa saisun barki, dan akwai k'alubale a gabanki kafin kisamu nutsatstsiyar rayuwa._” “Da mamaki na kallesa, amma saiyak'i bani damar neman k'arin bayanin komai a wajemsa. Bayan na warke nadawo gida kuka saka aka saceni kaida Muftahu, na koma gida mangariba ta rufa a ranar, ashe wai baba mai kanwa yaga sanda na shiga gida a firgice, sai'a washe gari ya aiko a kirani, innarmu da Munubiya sunyi mamakin kiran, dan cayay Hussaina taje, (shi dama baya kiranmu Munubiya da Munaya, sai Hassana da Hussaina). Haka na saka hijjab naje, a yau baiyi wasan daya sabayi da niba, kai tsaye yafara maganarsa”. _“Hussaina jiya daga ina kika dawo a firgice?”._ “A tsorace na kallesa, dan lallai tsohonnan yafara bani tsoro, dama tun muna yara mukanji ana cewa tsoronsa akeji, saidai bamusan manufar tsoronba, murmushi yayi yana gyara zama da cigaba da gyaran wasu takarsu Dana tarar yanayi, yace___”. _“karkiji tsoro, nimai taimakonki ne gwargwadon abinda ALLAH yabani ikon sani, dan haka ki fad'amin gaskiya_”. “dak'yar na iya had'iye yawu, sannan na fad'a masa abinda yafaru tsakanina daku. Murmuahi yay mai matuk'ar sauti, wanda ya bayyana fararen hak'oransa da basu wuce goma sha ba da suka rage, wad'anda a kullum zaka sameshi da ashuwaki yana d'abbak'a sunna, yace___”. _“Hussaina ni bazance ki amince ko karki aminceba, saidai nabaki dama kije ki duk'ufa rok'on ALLAH, a cikin kwana ki biyu rak ALLAH zai nuna miki mafita da abinda zai zama alkairi a gareki, sannan karki sanarma Hasaanar ki, danna kula bazata amince ba tacikin sauk'i, tashi kije”._ “A wannan ranarma haka baba mai kanwa ya sakani cikin rud'ani, nazo dukna hana kaina nutsuwa da kwanciyar hankali, saidai nabi shawararsa ta mik'a kukana ga Ubangijin al'arshi, dan shine gatana kuma fitilata, a kwana na biyu kuwa saiga dalilin dayasani amincewa da buk'atarka ya faru, na amince maka badan hankali na ya kwantaba. tunda kuma lokacin baba mai kanwa bai kuma min maganar data shafi auren ba, harma na d'auka duk mafarki nayi, har maganar da mukayi d'in dakai. Saida ana gobe d'aurin aurenmu da safe na fita yin wani Abu na gamu da baba mai kanwa, shine yace na biyoshi gida. Mun Isa gida a d'akin zaurensa, yabani wasu abubuwa dabansan mineneba na sha, sannan yabani turare kashi biyu, yace ni 1 Munubiya 1, yace____” _“Hussaina kimin wata alfarma mana?”._ “A sanyaye nace kabani Umarni akwai baba. Yay murmushi da fad'in___”. _“ALLAH ya yimiki Albarka Hussaina, ina tausayinki ta wani fannin, ta wani fannin kuma murna nake tayaki, duk abinda nake hasashe a kanki nasan zaki iya, dan kinfi y'ar uwarki wayo, ni dake zamu had'a kaine wajen fidda mahaifinku a sark'ak'iya, su a gangancinsu sun tozarta kune domin tunzura mahaifinku da karyar masa da zuciya, amma basusan Ubangiji mai hikima baneba, yafisu sanin akan abinda su bai basu damar saniba, kiyi hak'uri inata miki magana a cirkud'e, zaki fahimci komai anan gaba kema, alfarmar da zakimin shine dukkan abinda kikaci karo dashi a rayuwar aurenki ki sanar min shi, insha ALLAH Zan miki fashin bak'i gwargwadon abinda na fahimtar nikuma, maganar zaman aurenku da yanda kuka ginashi kuma ya rage naku bayan warwarewar komai, wannan ba hurumina baneba, tashi kije, daga nan dai zamu dinga tayaku da du'ai”._ “Dukda banida tabbacin mijin dazan aura wannan magana tashi tamin nauyi da wahalar fasaara, da y'an gidanku suka kai lefena kuma saina kuma tsintar kaina a rud'ani da firgici, ban kuma fita daga wannan firgicinba har aka kawoni wannan masarautar. Saka pills da Muftahu yayi mana shine k'alubale na farko dana fara cin karo dashi Wanda nake k'yautata zaton baba mai kanwa ya hangomin, hakanne kuma ya sakani tada hankali nace nafasa auren, dan a zatona kun had'a bakine da Muftahu, amma sai maganar tafiya India ta datse dukkan hanzarina, ko kad'an banyi yunk'urin sanarma baba mai kanwa wannan batunba, dan aganina baya cikin abinda shima zaiso Sani. Idan baka mantaba a lokacin da ka kaini sallama gida da kuma gidansu Munubiya ka barni a can?”. Kansa ya jinjina mata idonsa a lumahe ya jingina da gado, kai kace ba
Chapter 70 · 0% Book details