← Book details Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 76

Sashe 62

Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk Wanda yake a wannan masarauta yau hankalinsa a matuk'ar tashe yake, saifa kallon kallo da hasashen juna ake a zuciya, kowa yana zargin Wanda ya raina.
Hankalin Abie a matuk'ar tashe ya nemi ganin Galadima, koda sarkin k'ofa yazo yana knocking Galadima bai amsaba, kuma yana kallonsa ta CCTV.
d'an aike ya koma ya sanar Galadima ya kulle kansa a d'aki yak'i bud'e k'ofa.
Papi inno ya kira, yace maza taje sashen Galadima taga mike faruwa.
Ko kuyangi inno batajira sun mata rakkiyaba, hasalima babu Wanda yaga fitowarta a sashen mama Fulani, dan kowa a rikice yake da wannam bak'on lamari na satar yara.
Galadima daya ga sarkin k'ofa yabar wajen ya mik'e shima daga gaban kayayyakin da yake aikin, shaddar jikinsa ya cire yasaka bak'in wando da t-shirt, ya kawo bak'ar jacket mai k'yalli kamar rigar sanyi ya ajiye gefe, a bakin gadon ya zauna yana d'aura takalminsa yana cigaba damasu Sauban da Nuren bayanin hanya, a dai-dai lokacinne Inno ta iso sashen nasa, da hanzari Sarkin k'ofa ya bud'e mata k'ofar, bata jira wani isoba ko masa sallama ta turo k'ofar falonsa ta shigo, babu kowa a falon, komai ma a kashe yake. Bedroom d'insa ta nufa, nandai saida tayi knocking kam, saidai kafin yay yunk'urin tasowa ya bud'e mata ta turo k'ofar ta shigo, mik'ewa yay yana kallonta da d'aukar jacket d'insa zai saka.
Ajiyar zuciya inno ta sauke, saboda ganinsa normal.
“Ranki ya dad'e da kanki? lafiya dai ko?”.
“Inafa lafiya Muhammad? takawa ya aiko a kiraka ance ka kulle kanka, gashi baka sanar mana halinda yarinyar nan take cikiba”.
Galadima yace, ba kulle kaina nayiba, bansan kuma d'an aiken daga papi yakeba” ya juya yana kallon Munaya da cigaba da fad'in, “itama ta farfad'o, amma sun mata allurar barci”. ‘ya k'are maganar da daidaita zaman kwalar rigar jacket d'insa’.
Ajiyar zuciya inno ta kuma saukewa, tace, “to Alhmdllh. ina kuma zaka naga kana shiri?”.
Wani murmushin takaici yayi zuciyarsa dake gudun daya wuce kima da suya ya dafe, Inno dai ta zuba masa ido, takowa yay inda take ya kama hannunta ya rankwafo (dan yafita tsaho) ya d'ora bisa kansa, cikin murya mai nuna tsananin karsashi da alwashi yace, “kisamin albarka inno, zanje farautane”.
Da sauri ta janye hannunta daga kansa tana matsawa baya, “Muhammad mikake nufine? kana ganin tashin hankalin da muke ciki shine zaka k'irk'iro mana wani kuma? kana tunanin wad'annan mutanen zasu barkane? dama kai suke fako, shiyyasa sukayi tarko da bayin ALLAHn dabasu ji ba basu gani ba, su takawa cikin k'ok'arin d'aukar mataki suke, yanzu haka naga IG da kansa gashican ya iso bisa umarnin kiransu”.
Galadima dake tattara abinda zai amfani dashi yana zubawa a aljihu, yace, “inno Muhammad Sameer d'inku ba ragon namiji bane da zai zauna jiran Police d'in da suka gaza gano wad'anda suka durk'usar masa da mahaifi tsawon shekaru a yanzu kuma nayi tunanin zasu iya dawomin da gudan jinina har uku, ba sune sukamin tarko ba nine namusu tarko, idan tsoron na mutu kuke, Ku cire inno, ko babusu mutuwa tabbataccen abune rubutacce a kundina, kimin addu'a saina saina dawo”..
Biyosa inno tayi har babban falo tana Kiransa amma yak'i dakatawa, saima d'aga mata hannu da yakeyi, yana gab da zai fita ya juyo yana fad'in “karki d'aga murya da yawa ranki ya dad'e, dan kunnen magauta a bud'e yake”.

Yana fitowa Sarkin mota ya taso, dan suna zaune jigum-jigum a rumfar bunun dake sashen na Galadima, duk gaisuwar da suke masa babu ta wacce ya amsa, yau kam ko d'aga hannun basu samuba ma.
Basu damuba dan dolene kowa yamasa uziri.
Da kansa ya bud'e mota ya shiga mazaunin driver, Sarkin mota daya k'araso yace, “ranka ya dad'e ka gafarceni gani”.
Da hannu yamasa nuni da gefen mai zaman banza batareda yace uffan ba.
Sarkin mota bashida za6in daya wuce zagayowa ya shiga.
A 360 Galadima ya ja motar, kamarma ya manta yana cikin masarautane, saida suka fito gaba d'aya sannan ya bud'e baki da k'yar yace, “ka dinga kallon bayanmu, dan nasan dole za'a samu masu binmu”.
Da “to” sarkin mota ya amsa cike da girmamawa.
Sarkin mota yace, “tabbas ranka ya dad'e ana binmu”.
Cije lips Galadima yayi, ya canja hanya, cikin salon iya taku suka 6acema su Harun dake bin su tundaga masarauta.
Hankalin Harun ya tashi kwarai da gaske, dan bai shirya fito na fito da Galadima ba yanzu, saiya cimma burinsa, daga nan komai ta fanjama fanjam, iya zagaye-zagayensu baiga ko motar datai kama data Galadima ba.

Shima yana 6ace musu ya dawo kan titi sosai, Maps d'in GPS ne yazama jagoran Nuna masa hanya, da taimakon Sarkin mota kuma dayasan gari. Danshi Galadima ba tuk'i yakeba idan yazo 9ja, saidai idan ta kama tilas babu yanda zaiyi kamar irin haka.
Sunyi tafiya mai tsawo, yayinda yake Communication dasu Nuren dasu Saleem. A haka ya iso inda suke, duk fitowa sukayi daga motocin, shima Galadima ya fito, idonsa akan agogon hannunsa, yad'an kallesu sannan ya koma kan waya yana fad'in, “maps d'in ya nuna suna a wajennan, kunga kenan tsakanin gidajennan guda hud'une dake kallon juna?”.
“kwarai da gaske suna nan”. cewar Muftahu yana furzar da iska.
Galadima yace, “Sauban da Saleem zaku cigaba da Control namu”. ‘yay maganar yana ciro agogon hannunsa ya mik'a musu, “ga wannan kuci gaba da using dashi”.
Suka amsa da “to” suna kar6a. ya mak'ala abinda zai taimaka masa yaji magana, suma su Nuren duk yabasu suka saka.
Har zasu bar wajen ya dakatar dasu ta hanyar d'aga musu hannu, takawa yay gaban k'ofar gidan farko ya haska gaban gate d'in da fitilar wayarsa, babu abinda yake nema, ya matsa na biyu ma haka, komawa yay d'ayan 6angaren, yana haskawa saiga sawun tayar mota data shiga gidan, duk'awa yay ya d'iba k'asar wajen ya shinshina, ya d'ago ido ya kalli gidan yana jizar lips, saiya zubar da k'asar daya d'iba ya mik'e, da hannu yayma Nuren da Muftahu nuni nan ne.
Tahowa sukai garesa, Aunty Salamah datun d'azun suna daga cikin mota suna kallonsu suma suka fito ita da su Ameer.
A tare suka rissina suna gaida Galadima ya amsa yana bin su da kallon mamaki.
Da yake su Saleem sun sanar dasu Muftahu su Aunty Salamah d'in sai Nuren ya kuma yima Galadima bayani.
Aunty Salamah tace, “ka gafarcemu ranka ya dad'e, nasan zakayi mamkin mun shigo abinda ba'a gayyacemu ba, insha ALLAH zakaji dalilin shigowar tamu nan gaba. game da shiga gidan nan mungama komai, maza 5 ne da mata biyu, wad'anda shigarsu ta tabbatar min suna cikin hadiman masarauta su matan kenan”.
Kai kawai Galadima ya iya jinjina masa. daga nan yaymata nuni da zasu iya farawa.
Da taimakon su Ameer suka shiga gidan.

★★*★★★*★★★*★★

Fitar Galadima da kusan awanni hud'u, around 2am Munaya ta farka a firgice, Inno dake zaune akan Sofa, mom da Aunty Mimi kuma a gefen gadon suka kalleta, tashi Mom tayi da sauri ta nufeta tana rik'eta, itama Aunty Mimi ta taso.
Kuka munaya ta sanya tana fad'in “Mom sun mutu ko? Nasan dama kashesu zasuyi, Aunty Mimi dan ALLAH miye laifinsu su? kwanansu 7 fa kacal yau a duniya, mi suka sani game da abinda ake tuhumarsu? An durk'usar musu da kakansu, an hana mahaifinsu nutsuwar zuciya data rayuwa, shin wannan tabon bai Isa a barsu su taso da shiba a rayuwarsu? Har sai an had'a da salwantar dasu kenan?”. ta fashe da kuka maiban tausayi.
Tasowa inno tayi ta zauna a bakin gadon itama, kamo hannun Munaya tayi ta kwantar da ita a jikinta tana shafa kanta, yayinda itama kwallar kebin nata kumatun.
Aunty Mimi da mom ma duk hawayen sukeyi, kalaman Munaya sun ta6a zukatansu.
Lallashinta da magana mai dad'i suka shiga fad'a mata, sai sauke ajiyar zuciya takeyi, ga jikinta yayi ringim da zazza6i saboda nononta sun mata hak'e-hak'e, rabonsu da shansa tunda rana, tausayinsu ya kuma kamata, tasan yunwa da k'ishi ma kawai sun Isa su k'arar da numfashinsu, hawaye masu d'umi suka kuma gangaro mata a kumatu suna sauka jikin inno dake shafa kanta.

Shayi Aunty Mimi ta had'o mata, amma fir tace ta k'oshi, da k'yar inno ta samu ta lalla6ata tasha Quarter d'in kofin.
Mom tace, “wannan nono kid'an matsesu kozasu rage miki nauyi, dan shine yakawo wannan zazza6in”.
Bata musaba aka kawo k'aramin bowl ta matse aciki, Aunty Mimi ta zubar a bayi”..
Tanason tambayar ina Galadima tanajin kunya, sukuma babu Wanda ya sanar mata komai, kodan gudun k'ara tada hankalinta.
Magani suka bata tasha takoma ta kwanta, yayinda sukuma suka mik'e duk suka d'aura Alwala suna mik'ama Ubangiji kukansu, danshi masanin sirrin 6oyene, yana kallon komai, kuma shine zai kawo iyakar komai d'in.

★★★★★★★

Duk wannan abun dake faruwa su Momma babu Wanda ya sanar musu, saidai sukaji a jikinsu tamkar akwai matsala, sunta kiran numbers amma daga wadda zasu samu a kashe sai wadda network zai hanata shiga.
Sai suka d'aura ko shagalin sunan ne yakawo hakan.

*******************

Tunda Munubiya suka koma gidan kuka takeyi, ko kad'an tak'i sauraren yaran da keta tsula kuka suma, balle tabasu nono.
Ba itaba hatta su Ayusher dasu feena kukan sukeyi, hakama Samha harda shid'ewa, dan itama su tabi bata koma masarauta ba, Yaa marwan da mama Rabi'a ne kawai ke k'ok'arin danne nasu suna lallashinsu.
Yayinda dare yay nisa duk sai suka d'aura alwala suka zo suna mik'ama Ubangijin talikai kukansu da k'ok'on barar bama wad'annan k'anan alhaki kariya da fatan ku6ta.

A 6angaren gidan su Munaya kam duk hassadarsu yau dai sun tausayama gudan jininsu da yaranta, sundawo gidane kowa yana sharar kwalla da addu'ar ku6tar yaran.
Ita innarsu Munaya ma ai ba'a magana, ALLAH kad'aine yasan halin datake ciki, ta shige d'aki ta rufe kanta tana jera nafilfili, dan wannance kawai gudunmawar dazata iya bayarwa a garesu akan wannan lamari mai sark'ak'iya da yawa.

Abban su munaya ma yau harda hawayensa, dukda bashi da tabbas akan hasashensa yasan komai zasu iya, saboda SD yanada kusanci da wannan masarautar sosai, duk abinda ke hannunsa da bayanan daya ajiye ya shiga tattarasu waje d'aya...............✍🏻

😿Duk nisan jifa dai k'asa zai fad'o, kwana 99 na 6arawo, 1 kuma tak namai kaya.👎🏻
Chapter 62 · 0% Book details