← Book details Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 76

Sashe 29

Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Babu yanda Muftahu baiyiba dan ya sarrafa agogon hannunsa amma hakan ya gagara, Dan bak'aramin d'auri ya shaba.
Kusan gab da magriba Wanda ke kawo masa abinci ya shigo, ajiye kular abincin yayi sannan ya matsa kusada muftahu zai kwanceshi, cikin murya k'asa-k'asa kamar mai rad'a yace “yalla6ai inhar zaka biyani wlhy zan ku6tar dakai”.
Kallonsa Muftahu yayi sosai nawasu mintuna, “ka tabbatar?”.
“wlhy Oga da gaske nakeyi, Dan wannan matar da kake gani bata wasa bace, duk abinda ta fad'a zata iya aikatashi wlhy”.
Murmushi Muftahu yayi, yace, “nawa kake buk'atar Na baka?”.
“tab aini Oga dubu 100 ma ta wadatar”.
Muftahu yakuma Murmusawa, “zan baka 200”.
Da sauri yaron yaja baya cikin razana, “oga dubu 200 fa? Yo ai sai a d'auka nafara yankan kaine”.
Sosai abin yabama Muftahu dariya, Dan haka ya dara, yo dubu 200 a wajensa ai bata wuce ta siyen agogo ko takalma ba, amma shine shi yake ganin 200k a matsayin wasu kud'in da har za'a iya d'auka yayi yankan kai.
Kallonsa yayi yana murmushi, “karka damu to, amaimakon nabaka kud'in a hannu a zargeka mizai hana Na bud'e maka wata Sana'a da zakabar wannan aikin da kakeyi yanzu”.
“to ai Oga karkaje kasa a kamani wataran, nikuma inhar zan samu Sana'a to zan nutsu”.
“haba abokina, ya zakamin rana nikuma Na maka dare, karka damu kaidai ka aminta dani kawai”.
“to Na amince, yau sai k'arfe 11 zan kawo maka abincin dare, a time d'in sauran sun fita club, insha ALLAH nikuma zan dawo baya nace Na manta da abincinka, daga nan saina ku6tar dakai, sukuma na sanar dasu Na dawo ban gankaba”.
“shikenan babu damuwa, idan zaka dawo kazo da account number, dana koma zan maka transfer insha ALLAH”.
“to Oga Na gode sosai”. Ya fad'a cike da d'oki.
Murmushi kawai Muftahu yayi.
“yauwa Oga bara Na kwanceka kaci abincin to”.
Girgiza kai Muftahu yayi, yace, “a'a ka barsa kawai, banajin ci, in kanaso d'auka kaci kawai”..
“amma Oga ai.......”.
Kai Muftahu ya girgiza masa alamar karyace komai.
Shiru yaron yayi ya d'auki kular ya fice kawai, Muftahu kuma ya bishi da kallo.

**************************

Har akayi isha'i Galadima yana birnin gayu, saida aka kira sallar magriba ne yafita zuwa massalacin dake plaza d'in yay salla tare da ma'aikatan wajen masu salla, daga nan ya gaggaisa da makwaftan wajen dakan zo masallacin yin salla suma, bai fitoba saida akayi sallar isha'i. daga nan yacema saleem yaje dasu Aryaan su za6i dukkan abinda sukeso ya mik'a mass ATM d'insa, shikuma ya kuma shiga office ya kulle kansa ya d'ora tunaninsa daga inda ya tsaya.
Ya dad'e yana zagaye office d'in, yayinda zuciyarsa ke k'ulawa da kwancewa, agogon hannunsa ya kalla, ganin time yayi nisa yasashi furzar da huci, kayansa ya tattaro ya fito, dogaransa duk suka mik'e, suna gaisheshi, amsawa ya shigayi tamkar baya so.
d'aya aciki yace, “zamu tafine ranka ya dad'e?”.
Kansa ya jinjina masa alamar eh, sannan yace “ama saleem magana”.
Da sauri suka amsa da to.
Ficewa yayi, sauran dogaran sukabi bayansa. Mota aka bud'e masa ya shiga, za'a rufe murfin ya hana, idonsa akan k'ofar plaza d'in harsu Aiyaan suka fito tare da saleem, dogarai biyu d'auke da manyan ledoji.
Suna hangoshi suka k'arasa da gudu, murmushi yayi ya d'aukesu d'ai-d'ai da kansa ya saka a motar, sannan aka rufe musu k'ofar.
Sudai dogaransa sai mamakin yanda yake sakema su Aryaan sukeyi.
Har sun fara tafiya ya fad'ama sarkin mota suje zasu taho da Munaya.
A ladabce sarkin mota ya amsa da to.

*****************

Muna tsaka da hirarmu aka kira wayata, sharewa nayi tamkar bazan amsaba, Munubiya ta harareni, ramawa nayi nima sannan Na d'aga.
Ciki-ciki nayi sallama, ya amsa daga can, mamaki ya kamani danjin muryar Galadima, katseni yayi da fad'in “ki fito”. Bai jira cewata ba ya yanke wayar.
Kamar zanyi kuka haka naji, Yaa Marwan ya fito daga d'aki yana saka rigarsa, kallona yayi yana fad'in “k ba jiranki akeba ne?”.
Sai da Na kumbura baki sannan Na mik'e. shikuma ya fice.
Da taimakon feena Na had'a komaina, har abubuwan da mama Rabi'a ta bani, sannan suka rakoni. Mun iske Yaa marwan tsaye jikin motan ya dafa k'ofar suna magana da Galadima dake ciki bai fitoba.
Dogari d'aya ya zagaya ya bud'emin, ido muka had'a da Galadima Na janye da sauri, shima janyewa yay ya maida hankalinsa ga Yaa marwan dake masa magana.
Mamaki ya kamani ganin su Aiyaan, suma cikeda d'oki suka fad'amin a jiki suna dariya da fad'in “Auntynmu!”.
Juyowa Galadima yay yana kallonmu, shima Yaa marwan yay dariya kawai, sannan ya rufe mana murfin yanama Galadima sai da safe.
Su Aryaan sun kacame da bani labari, yayinda nikuma naketa musu dariya da biye musu, mamaki ya kama Galadima, bai ta6a tunanin ina magana hakaba, ya lafe jikin seat yana kallonmu cikeda birgewa.
Nikam nama manta ko gaisheshi banyiba, saida yay gyaran murya sannan Na d'ago Na kallesa, murmushi namasa ina fad'in “yalla6ai barka da dare”.
Shima wani miskilin murmushi ya min yana d'agamin hannu batareda yayi magana ba.
Aiyaan yay saurin fad'a “auntynmu bafa yalla6ai sunansa ba, sunansa Uncle”.
Kamar zan harari yaron sai kuma nad'an murmusa ina kallon Galadima dake kallonmu shima. janye idona nayi daga gareshi Na cema Aryaan to naji zanke fad'a.

Har muka kai gida basu barmu mun hutaba, sai surutu suke da bani labarin abinda yafaru a gida bana nan, danaji zasu kauce hanya kuma sainai saurin waskewa.

★★*★*★★*★*★★

Sarkin mota yana ajiye su munaya ya duba gefen seat d'in data zauna, takarda ya gani ya d'auka, dan sanda zasu shige tamasa wata inkiya da hannu.
Dubawa yay yaga mita rubuta. Sallama yayma sauran 'yan uwansa sallama akan zai shiga gida.
Daga nan ba gidan ya shigaba, saiyay dabarar da yabar masarautar gaba d'aya.
Sun had'u da Saleem a inda suka shirya, saleem Ya bama sarkin mota handkerchief d'in da zasu shak'ama Muftahu.
Sarkin mota ma yaje ya bama Ameer ne, daga nan ya dawo k'ofar fada amma k'aramar k'ofa tacan baya inda keda k'arancin tsaro.
Agaban idonsa su Ameer suka sauke Muftahu a mashin yana cikin yanayin barci saboda abinda suka shak'a masa, saida ya tabbatar sunbar wajen sannan shima ya koma ciki.

Yau dai kam ni kad'ai Na kwanta a d'akina, Galadima ko lek'e bai lek'oba, yana can tare da su Aiyaan a d'akinsa.
Nima kawai saina kira Momma mukasha hirarmu, tana bani labarin yanda jikin Abie yaketa k'yau a tsakaninnan, dukda kar yanzu maganar bata fita amma yakanyi bamai tsawoba, naji dad'i sosai, na masa addau'a mai tsawo tareda fatan alkairi, daga nan muka cigaba da tattaunawa akan maganar Abbana, da zancen su innarmu dasuka k'i yarda su zauna a gidan, innarmu ta dage bazata zaunaba tunda muma anan muke, saida Momma ta saka baki da mata bayanin da zata gamsu sannan ta amince zata zauna. Nasha dariya, dan dama nasan za'ayi hakan, innarmu kawai kunya da kawaici.
Daga nan har muka dawo kan ta Muftahu, dayake tasan komai a kai, da taimakonta nima nake samun k'arfin gwuywa.
Itama tasha mamakin jin Harun a lamarin, ta dad'e tana jinjina maganar nan. ta bama Samha muka d'ora da hira, saida naga time yaja ga zazza6in fama ya rufeni, sallama mukayi nai addu'a Na kwanta.
Masu iya magana since sabo tirken wawa, saina kasa barcin, naji kawai ina kewar Galadima.

Shima kansa yanacan sai juye-juye yakeyi, yakasa barci, bayan sun gama hirarsu dasu Aryaan yay musu shirin barci da kansa suka kwanta, aiki yad'an ta6a yana Neman dabaru akan binciko Muftahu, baiwani dad'eba ya kwanta shima, amma saiya kasa barci, juye-juye yaytayi agadon, ganindai da gaske ya kasa barcinne saiya mik'e yana jan guntun tsaki, kwanciya ya gyarama su Aryaan ya lullu6esu da bargo sannan ya fito da nufin wai zai duba munaya 🤣😜.

Jin shigowarsa yasani k'ara lafewa tamkar nayi barci, ya kunna fitilar d'akin yana kallona, yaja wani dogon lokaci sannan ya kashe ya tako zuwa gadon, “nasan idonki biyu ai, dama kin tashi kinbar wani kumshe-kumshe”.
Shiru nayi nakumak'i motsawa.
Kwanciya yayi a gefena, yaja bargon shima ya lullu6a, tareda juyamin baya, yace “miya hanaki barcine?”.
“farkawa nayi”. Na fad'a batareda ba kalleshi ba.
Murmushi yayi yana fad'inn “ Hummm”.
Daga nan duk mukayi shiru nawani lokaci, kamar an matse bakina nace “yalla6ai na tambayeka please? ”.
Yace, “Uhmm”.
Juyowa nayi ina fuskantar bayansa, a nutse nace, “wai dan ALLAH ina sauran matan Abie yanzu?”.
Da sauri naga ya juyo gareni, ni harma tsoro ya kamani nai baya da sauri, nazata makeni zaiyi, amma sainaji ba hakaba, yace “Munaya mi kika sani a kaina ne?”.
“yalla6ai kamarya mina sani a kanka? daga tambaya?”.
Yace, “Humm yana matsowa gareni, zan matsa ya rik'o hannuna................✍🏼

Kuyi manage da wannan please🤦🏻‍♀

*_ALLAH ya gafartama mahaifanmu😭🙏🏻_*
[7/3, 9:59 AM] Aysha Galadima: *_typing📲_*

💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*

*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

~Book 2~ 👉🏻1⃣4⃣
Chapter 29 · 0% Book details