Sashe 67
Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Hankalinsa ya maida ga Galadima, “Sameer ya jikin?”.
Bud'e idonsa yayi shima, ya ajiye mug d'in hannunsa a teble d'in dake gefen damarsa, batare da yace uffanba ya sauke ajiyar zuciya yana taunar lips.
Banga alamar damuwar rashin amsawar tasaba a fuskar Harun, dan yariga ya saba da halinsa.
Saidai idonsa k'uri akan Abdurraheem dake cinyar Galadima d'in yana barci, mik'ewa yay yana fad'in, “my son zo mu gaisa ko?”.
Ganin haka nima nayi azamar mik'ewa nakai ga Galadima kafin shi ya isa, na d'auke Abdurraheem d'in ina fad'in “ai barcima yake ranka ya dad'e”.
Ba Harun ba hatta da Galadima saida yaymin kallon mamaki, nakoyi cid'in-cid'in da fuska yandama bazaice nabama Harun d'inba.
Baki ya bud'e kamar zaice wani Abu saikuma yay shiru yana kauda kansa daga kallona, nima saina ta6e baki ina barin falon da harar Harun ta gefen ido.
Gaban Harun ya fad'i, mi yarinyarnan take nufi?......
Kafin ya lalubo amsar ya tsinkayi maganar galadima yana cewa, “sorry Harun, kasan har yanzu a tsorace take, duk wani motsinsu akan idontane”.
Murmushin basarwa harun yayi, yace, “ai dolene hakan ranka ya dad'e, abinne akwai tsoratarwa, wlhy jiya tashin hankalinnan ne yasaka azababben ciwon kai rufeni, shiyyasa ko ganina ba'ayiba, yanzu police d'in ina suka samosu?”.
“humm” Galadima ya fad'a cikin tsananin taune lips da k'unar zuciya, ya bud'e baki a hankali zaiyi magana nida ke bayansu basu saniba nai saurin tareshi da fad'in “a hannun wasu munafukaine ranka ya dad'e, ai koni daza'a bani baiwar nan da aka kama da yaran wlhy saina tsoma kanta cikin drum d'in ruwa harsaita daina Numfashi zan barta, kafin sannan kuma nagamajin labarin Wanda ya sakata, amma shi my boss ai a station suka zauna har aka kawo yaran, badasu akaje farautarba”.
Tsuramin ido Galadima yayi cikin tsagwaron mamaki, miyasa to zanzo na kasa na tsare dukkan wani motsin Harun d'in? ya kula satar yaran tana Neman ta6a tunaninta takasa banbance Wanda zata zarga, ai Harun yawuce ya 6oye masa wani sirri na sashen rayuwarsa, tun da babu abinda bai saniba na baya, saidai abinda ba'a rasaba kam, danne ransa yayi ya nuna hakane, yabari har Harun d'in ya tafi sannan yaji dalilinta.
Ina kallon Sassanyar ajiyar zuciya da Harun ya sauke a 6oye, sannan yace, “ai police d'in sun cancanci Babar k'yauta, shiyyasama na shirya musu ita, sunyi aiki irinnan jaruman masu tsaro”.
“hakane wlhy ranka ya dad'e ”. Na fad'a cikin murmushi.
Dukfa yanda Harun yaso bugar cikin Galadima yaji yanda abun yake, na kafa na tsare, dayayi tambaya nike bashi amsa, saiya d'auka kodan Galadima bashida lafiyarne shiyyasa bai iya amsawa, tun da tunda ya shigo baice k'ala ba, kuma yasan yanayin ciwonsa, a baya ma shikan bashi taimako, baidai tsinci komai ba yay mana sallama ya fita, da k'udirin anjima ma zai dawo ne.
A sace na raka bayansa da harara, sannan na kalli Galadima na basar, dukda kallon tuhuma dayake jifana dashi kuwa.
Wani farfesun na sake zuba masa na mik'a masa.
Batare da ya kar6aba cikin k'ank'ance idon bala'i yace, “mikikayi haka? kinsan waye Harun a wajena?”.
Kaina na girgiza masa.
Yaja tagwayen tsaki yana hararata, “halan satar yaranki yafara shafar tunaninki ne? kina tunanin akwai abinda Harun zai iya gazaji daga sirrina?”.
Na d'an ta6e baki ina jawo teble d'in gabansa, na d'ora bowl d'in dana zuba farfesun, baki ya bud'e kamar zaiyi magana saikuma yay shiru. nima bance uffanba na ajiye masa sannan na koma k'asa Na zauna na zuba sabon kunu nahau sha.
Kwafa yayi, yace, kinma maidani d'an iska ko?”.
“Hummm” na fad'a kawai, naimasa kallo d'aya “yalla6ai wani karatun akan barsane a yanda yazo, sai idan lokacin fasaarashi yayi amasa fashin bak'i, nasan darajar alak'ata dakai batakai koda rabin tsakaninka da Harun ba, domin ni alak'ar wucin gadice ta had'amu, k'iris ma ya rage ta k'are, saidai inason nabama y'ay'ana kamar yanda ka fad'a kariya koda sau d'ayane a rayuwarsu kafin na barsu, dan haka maida wuk'arka a kube, lokacin zareta baiyiba, sometimes kalmar Mahangi da mai hange takanyi kamanceceniya, dan bakowa ke iya rarrabata wajen fasaara ba, amma kalmomine duka masu harshen damo, wani k'alubalen saida tunanin mai zurfi, wata k'oramar ruwan mutanen dake zagaye da ita sukanyi imani bazata balle harta cisu ba, saboda sun yarda sud'in masuntane da kullum suke rayuwa cikin wannan k'oramar, abin mamaki saikaga wataran an wayi gari da mutanen da muhalansu duk wannan ruwan ya had'iyesu, abinda basu ganeba bakowacce irin alak'a bace ake kulla amana da ita, wani farin idan yashiga cikin fari banbance k'arkonsa saidai ALLAH”.
Tashi nayi nai shigewata bedroom d'insa.
A fusace shima ya mik'e zai bini, kad'an yarage ya zubda farfesun dana ajiye masa, ALLAH dai ya kiyaye ya shallakesa ya wuce.
Hucin mutum kawai naji a bayana, hakan yasani waigowa da sauri, hannu ya dunk'ule zai kaimin naushi, nai azamar fad'awa saman gadon ina zaro ido waje, a lallai Abu ya girmama, nikuma miye nawa da zai sauke fushinsa a kaina? nai maganar a zuciyata.
Janye hannunsa yayi yana ciza lips d'in sa da k'arfi, idonsa dukya kuma rinewa, ya dunk'ule hannun ya daki d'ayan dashi, muryarsa har rawa take yace, “Miyasa zaki kuma hargitsan tunani ne? Minene laifin Harun shikuma? kuna nufin duk Wanda na yarda dashi shine mak'iyina? Kai impossible wlhy, Munaya wakikema aiki a kaina? ya rankwafo kaina, kaikace cinyeni d'anya zaiyi, saikace zaki yaga bandar nama, da k'arfi yace, “bazaki sanarmin ba saina k'arar da numfashinki ne waishin Ubanwa ke fad'a miki wad'annan maganganun da kike d'aureni dasu a ko yaushe?!!!”. Ya k'are maganar cikin tsananin tsawa da k'araji.