Sashe 7
Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da k'yar Galadima yad'anci abincin, danma tuwone, yanason tuwo sosai, maganin Nuren ya 6alla yabashi yasha, sannan suka nufi massallaci dan gabatar da sallar azhur.
'*****'*********'*******'*******'
Sauban ya sama musu tickets d'in tahowa Nigeria, Momma bata bari Munaya ta d'ebo wasu kayaba, tunda tanada kayanta anan, d'an abinda ba'a rasaba kawai ta d'akko, sunje asibiti sukaima Abie sallama sannan khumar yakawosu airport shida Samha da Khaleel dasuka musu rakkiya.
Sunyi zama nakusan 1hour sannan jirginsu yasamu tasowa......................✍🏼
*_ALLAH ya gafartama mahaifanmu😭🤚🏻✋🏻_*
[7/3, 9:54 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*
*_Haske writer's asso...._*💡
*_♦RAINA KAMA......♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻
~Book 2~ 👉🏻3⃣
............Shiru kawai yayi yana kallon fuskarta ta cikin d'an hasken mai kalar jaa, sai fuskar tabada wata kala data k'ara mata k'yau. yaune ranar farko dazaice yamata kallon k'urilla irin haka, yadad'e yana kallonta kafin ya janye idanunsa dake cike da barci. hannu ya mik'a ya kunna ainahin fitilar, haske ya gauraye d'akin, cikin dabara yafara yunk'urin janye jikinsa, amma tak'i yarda, saima farkawa datayi, tabud'e idanunta dasukai nauyin barci a hankali, kad'an take kallon face nashi, ta lumshe idon tasake bud'ewa.
“wannan d'aurin goronfa?”. ‘galadima yay maganar a hankali cikin muryar barci, yanabin hannun munaya da ta zagaye cikinsa da kallo’.
Sosai Munaya ta waro idonta yanzun, ganinta a jikinsa kwance, gashi tawani dabaibayesa saita sakeshi da sauri tana matsawa baya da waige-waigen inda take kwance. gabanta ne ya fad'i, dan ita harga ALLAH tama mance ta hau masa gado, tayi saurin rik'e kanta dake sara mata tana tashi zaune.
Shima saiya tashi yana binta da kallo, a mugun sanyin murya yace “bakida lafiya ne?”.
Hawaye suka wanke mata fuska, muryarta na rawa tace “kaina kamar zai tsage”.
Saida yaja 1minute kafin yad'an matso kad'an, yatsunsa biyu ya d'ora gefen wuyanta, saiyaji jikin zau da zafi, ya janye ya d'aura zuwa gefen kanta, jijiyar wajen sai motsi takeyi d'ass d'ass d'ass d'ass, alamaun kan namata ciwo sosai. hannun ya janye tareda sakkowa daga gadon gaba d'aya.
Ya zagayo 6ari da take, hannu yasa ya zame nata hannun data tallafe kanta dashi, ta tad'ago idanunta dake cike da barci, sunyi d'anja sun k'ara girma, idonsa a kanta, Dan haka ta janye nata ta maida k'asa tana cigaba da hawayenta.
Kad'an yad'an furzo iskar bakinsa, kafin a hankali yace “mike miki ciwo bayan kan?”.
Saida takuma matso wasu hawayen sannan tace, “duk jikina”.
“kin fad'ine?”.
Kanta kawai ta iya girgiza masa, ya cigaba da tsura mata idanu batare da yace komaiba, ganin tana hawaye duk sai yaji babu dad'i, koba komai itad'in Friend nashice ai, kamar yanda yafad'a tun farko. yad'an sauke ajiyar zuciya mai sauti kafin ya mik'e, bayi yashiga, mintuna kad'an yafito, tana a inda ya barta dafe da kanta, yace “taso kid'an watsa ruwa, ko jikin zai huce”.
d'agowa tayi ta kallesa, sai taga ya tsatstsareta da mayun idanun nan nasa, tayi saurin janye nata, amma takasa tashi. matsowa yayi kusada ita, ya mik'a mata hannunsa, alamar takama ta tashi, ta d'ago ta kallesa ya d'aga mata kansa yana mai lumshe idanunsa alamun tabbatarwa.
Hannunta ta saka a cikin nasa, ya had'e waje guda sannan ya taimaka mata ta tashi tsaye, kallo d'aya yamata ya kauda kai, dukda kayan nata masu kaurine saida yaji wani Abu daban, dansu fidda surarta sosai. Har wajen wankan yakaita, sannan yafito batare da ya ce uffanba. da kallo tabi bayansa, a ranta tana mamakin sauk'in kai irin nasa, ada kallon mutum mai girman kai take masa, amma tunda suka fara rayuwa a tare saita fara fahimtar ba haka baneba, kawai dai shi mutumne dabai cika hayaniya da surutu ba, shiyyasa inbaka gama saninsaba saika dunga masa kallon mai girman kai.
Koda ya fito saiya had'a mata tea, shi dama baya rabo dasu a d'akinsa, magani ya d'akko shima ya ajiye, yakoma bakin gadon ya zauna yana tsumayen fitowarta.
Kusan mituna 10 tagama watsama jikinta ruwan, lallai naji dad'i sosai, saidai kuma bazan iya maida kayan dana cireba, inajin kunyarsa, kuma jinsu nake sun d'auki zafi, towel naja Na d'aura, saidai bashida girma, bazan iya fita a haka dashiba Galadima yana d'akin, kad'an nabud'e k'ofar Na lek'oda kaina, yad'an juyama k'ofar bathroom d'in baya kad'an, a hankali cikin muryata mai nuna alamun banida lafiya nace “please yalla6ai ka taimakeni da hijjab”.
Waiwayowa yayi ya kalleni, alamun baijiba sosai, Na turo baki kad'an sannan nace “please yalla6ai hijjab”.
Baice komaiba ya mik'e, inda nake ajiye hijjab d'in yaje ya d'ako, yazo inda nake ya d'oramin akan hannuna dana mik'o, kallon ido cikin ido mukaima juna, kowa ya janye cikeda basarwa.
Bayan nasaka hijjab d'in nafito kamar wata muna fuka, sai k'asa nakeyi da idanu nakasa kallonsa, shima idonsa a lumshe ya jingina da fuskar gadon, wucewa nayi wajen akwatina Na d'akko wasu kayan barcin, bayi nakoma Na saka, saina yafo k'aramin Vail Na cire hijjab d'in.
Yabud'e idanu kad'an a kaina, batare da yayi magana ba ya nunamin mug d'in daya had'a tea a ciki. nad'an yatsine fuska da marairaice murya tamkar xanyi kuka, “ALLAH yalla6ai banajin yunwa”.
Shiru yay kamar bazai tankaba, saida yaja kusan 2minutes sannan yatashi zaune sosai, batare da yayi magana ba ya d'auki mug d'in da drug's d'in ya taso inda nake zaune a kan sofa, saman k'aramin table d'in gaban kujerar ya zauna yana fuskantata, d'an gaf d'in daya bari tsakanina dashi bai wuce tafin hannuba, Dan har inajin saukar numfashinsa, baya nad'anja kad'an Na jingina da jikin kujerar, amma hakan bai hana kusanci sosai tsakanina da shiba. babu magana babu komai naji dirar cup a bakina, d'ago ido nayi tamkar zan fasa kuka, danni wlhy banajin shan shayinan, yamin hararar data saka 'yan cikina harmutsawa, babu shiri nabud'e baki na kar6a, ya had'e girar sama da k'asa, baibar ko k'aramar k'ofar dazan kawo masa wargiba, haka naita kar6a ina hawaye, saida yaga Na shanye tas sannan ya barni yana hararata, nidai yau babu k'arfin mayarwa, yabani maganin, shikam babu musu Na kar6a nasha. ganin yanda naketa hawaye saiya zubamin ido kawai yana kallon ikon ALLAH, nikam banida niyyar daina kukan nawa, kuma nima bansan dalilin kukanba, kawai dai jinake hawayen Na tahowa.
Ya zuba tagumi abunsa yana kallona kamar yasamu television. kallon dayake min saiya k'ara tunzurani, nafara kuka mai sauti harda shashsheka.
Tagumin yacire yana wani k'asaitaccen murmushi, ya mik'e tseye yakoma kan gadon, filolin dasuke k'asa ya d'auka ya jera a tsakkiyar gadon kamar d'azun. nidai duk ina kallonsa, saida ya lullu6ama k'afafunsa bargo zuwa cikinsa sannan yace, “taso ki kwanta sarkin arhan hawaye”.
Harara Na zuba masa batare da Na shiryaba, sai kawai ya ta6e bakinsa yay kwanciyarsa ya barni, tareda kashe fitilar ya maida ta barci.
Kusan mintuna 4 Na zame Na kwanta a kujerar, amma sainaji duk babu dad'i, saboda maganin bai fara tasirin da jikina zai bar ciwonba, tashi nayi nakuma zama, kusan 5munutes sannan natashi sad'af-sad'af tamkar munafuka na haye gadon. Ni duk tunanina yayi barci. Ashe duk abinda nake yanajina da kallona. murmushi yayi kawai yana lumshe idonsa, a ransa yana jinjina irin rashin wayona.
Ajiyar zuciya Na sauke a hankali, sannan naja bargon dayake babbane Na lullu6a, mintuna kad'an nafara zufa, alamar zazza6in ya sauka. Bargon na janye don insha isaka, bansan sanda barci ya saceni ba.
Juyowa yayi ya kalleni, yaga ina sauke numfashi a hankali alamar nasamu barci, k'aramar ajiyar zuciya ya sauke kafin yasake addu'a shima ya gyara kwanciyar sa.
★★★★★★★
Yau gidanmu sun tashi cikin tashin hankali, Abbah yay Accident yayin dawowa gida daga wajen aikinsa, innarmu Na kwance ciwon kai dukya isheta, tunda ta tashi da safe dashi ta tashi, gasu Aryaan sun isheta da ihun fad'ansu, sai mugun wasa sukeyi suna guje-guje a falon, amma takasa d'aga kai ta tsawatar musu.
Zuciyarta cike da kewar su Munubiya, inda suna nan da yanzu suke bata taimako, koyaya tace batajin dad'i zasu rud'e, amma gashi yau ko wanke-wanke tama rasa mai matashi, sai Zainab maman fauziyya tasaka tayi mata, amma 6angarenta ko shara bai samuba yau, kuma tun d'azun tafara jin mamansu yaa hameed tana k'ananun magana akan tak'i fitowa ta aza musu girki, maimakon sunga shiru su lek'o suji ko lafiya? A'a su babu ruwansu, kawai a dafa abasu suci da 'ya'yansu...
Wayarta dake ring ta katse mata tunani, ta kalli su Aiyaan dake danbe Aryaan Na kuka saboda dukansa da Aiyaan yayi a baki. “wani cikinku ya d'akkomin wayata saman freight”.
Cikin kuka Aryaan yace “Innarmu kingafa ya dokarmin baki”.
“kukuka Sani, nidai nace wani ya d'akkon waya acikinku, idan kuma kuka bari Na tashi sai jikinku yagaya muku”.
Aryaan ya d'akko mata wayar ya kawo mata, lokacin harta tsinke, ganin Abbanmu ne yasata bin kiran, bugu biyu aka d'aga, ko gaisuwa bai bari sunyiba, yace mai wayarne yayi Accident, yanzu haka suna general hospital.
“innalillahi wa'inna'illaihirraji'un” innarmu tafad'a tana mik'ewa zumbur, ga wata zufa Na karyo mata, batasan tayo waje tana kwalama matan gidan kiraba.
Kowacce tafito jiki Na 6ari, azatonsu wata acikinmu aka sako, musamman ma ni dasuke kiran aurena auren d'ori d'afini.
tana hawaye ta sanar musu da abinda yafaru. Nanfa gidan ya rikice, yara suka garzaya suka sanarma innaro.
Ko takalmi babu haka tanufo gidanmu tana shar6ar majinar kuka da kiran tashiga uku, Awwalu zai mutu ya barta. wannan kwakwazon natane ya ankarar da jama'ar anguwarmu.
A rikice baba k'arami da Dady suka nufi asibitin, Dan matan gidanmu sun kira suma sun sanar musu abinda ke faruwa.
Kafin wani lokaci jama'ar gidanmu sun gama cika asibitin, sai koke-koke sukeyi suna son ganin Abba, amma an hanasu, Dan bak'aramin buguwa yayiba.
______________________________