← Book details Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 76

Sashe 54

Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

“hakane ai saidai hak'uri ranki ya dad'e, dama wasu idan sun haihu sukanyi k'am baki, amma a hankali zai canja”.
Badan munaya tasoba ta zauna, laraba tabata kunu mai k'yau da aka dama don ita, sai k'amshin kayan yaji yakeyi, sai farfesu.
Kallon abincin kawai Munaya keyi, amma ko kad'an batajin sha'awar ci, ta tuna kwanakin baya da idan taga abinci jikinta har rawa yakeyi wajen son ci, hikimar ubangiji daban ce, ta d'ago ido suka kalli juna itada Galadima dake kallonta tun d'azu, a zuciyarsa yana tuna kwanaki uku rak dasuka shige, yanda ta maida abinci, murmushi yamata ta d'auke idonta ta maida ga abincin.
A haka Mom ta shigo ta iskesu, zama tayi tana fad'in “yanaga bakici komaiba?”.
Idon Munaya cike da kwalla tace, “ALLAH mom banajin d'and'ano”.
Zama mom tai kusada ita, tace laraba taje itama ta karya. Kunun ta d'auka ta tsiyaya a Kofi ta d'iba mata farfesun, “kar6a maza runtse ido ki shanye kunun nan d'iyata”.
Kunyar Mom ta sakata k'ar6a tana had'iye kwallarta, tafara sha badan tanajin dad'inba, sai dan tsatstsareta da ido da Galadima yayi shida Mom. ahaka dai tasamu tasha yafi rabi, dama yunwar takeji, dad'in bakinne kawai bataji, shima farfesun tad'anci, dandanan tafara zufa. tace,
“Mom dan ALLAH bara na kunna AC”.
“a ina?”. ‘galadima ya fad'a yana tashi zaune da sauri’.
Ita mom ma dariya ya bata, yawani had'e fuska yana harar Munaya, “malama babu wani AC da zaki sakama mutane anan, kina ganin yara duk da mura sukazo duniya saboda rashin jin maganarki.....”
Mom ta katseshi da fad'in “ai bama zai yuwuba, itada ke jego ko fankace a d'akinnan ai saidai kallo kuma, yanzu ruwan sha ma sai mai zafi”.
Galadima ya sakko daga gadon yana fad'in “hakan ai shine dai-dai wlhy, remote d'in AC d'in ya d'auka a lokan gefen gadon ya masa yanda bazata iya control d'insa bama gaba d'aya, sannan yafice abinsa yana murmushin mugunta.
Mom ta girgiza kai kawai, a ranta tana mamaki canjawar Sameer......
Maganarsa ce ta katse mata tunani, harya fita ya dawo baya, “mom ga maganinta nan tasha, kuma yaranan yunwa sukeji”. ‘yak'are maganar cikin marairaicewa’.
Dakuwa mom tamasa, “Sameer kaci kidanku, wai yaushe kama fetsare hakane ban saniba?”.
Fita yayi yana dariya, ta kirashi da sauri. Kuma dawowa yayi, tace, “kasandai Doctor tace a nemi madara, naga kuma bama kada niyyar hakan”.
Gaba d'aya fara'ar fuskarsa ta d'auke, yad'an shafi girarsa da d'anyatsa d'aya yana fad'in “Mom wai wace madara ga abincinsu?, ALLAH dai ai shiya haliccesu, kuma shine zai wadatasu da abincin nasu, amma kawai sai a kama wani danna musu wata madara? dan ALLAH mu ajiye zancen madarar nan ma gefe mom”.
Numfashi mom ta sauke, tasan murd'ad'd'en halin Galadima da dagewa akan ra'ayinsa, cikin kwantar da murya tace, “na yarda da maganarka, amma ita za'a tausaya mawa, shayar da yara uku bafa abune mai sauk'iba Sameer, wasuma d'ayane idan suna da fargabar shayarwa kaga duksun k'are sun lalace, koda dai sau d'ayane sai a ringa basu madarar a rana, tunda ALLAH dai baya hanaka yanda zakayi bane”.
Tashi Munaya tayi tana hawaye, taje ta hau gadon kawai tayi kwanciyarta, ta kula Galadima yacika son kansa, tanaga saita tuna masa da matsayin auren nasu da alfarmar yarda ta haifa masa y'ay'an dayake neman nuna mata mulki a kansu, aidai abin shayarwar a jikinta yake, sai kuma yanda taso tayi da kayanta, dolene ta takama wannan homar tasa birki.
Daga Mom har Galadima da kallo suka bita, yaja guntun tsaki yana juyawa zai fita.
Mom tace, “zaka siyo d'in?”.
A k'ufule yace, “zan duba”. Yay ficewarsa. shifa ya lura yarinyarnan ma batason yarannan, shin bak'in ciki take ALLAH yamasa k'yautar abinda kud'i baya sayane ko me? ALLAH zaiyi maganinta kuwa.

🤣🤣ho Galadima, uwa ta ta6a k'in d'antane🤦🏻‍♀.

★★★★★★★★★★★★

Mama Fulani dai yau tagaza gane kanta, duk yanda taso danne zuciyarta tayi murnar koda ganin idone ta kasa, shiyyasa ko zuwa wajen tarbarsu batayiba.
Takuma hana dukkanin bayinta da kuyangi shiga inda take.

Abinda bata saniba idon Galadima fes yake akan dukkan Wanda ya tayashi murna da samun k'yautar ALLAH, wad'anda bama su fitoba sun shiga black lists, kuma d'aya bayan d'aya saiya kartama kowa rashin m acikinsu.

★★★★★★★★★

Innaro kuwa dai saita hau tsiya dataji labarin su Munaya kowa mijinta ya d'auketa zuwa gidanta, tahau zazzaga masifa anmata ba daidaiba, babu Wanda ya kulata, dan masu zugatan suma hassada ta ishesu, basuda kuzarin taya 6era 6ari😂..
Haka tagama jarabarta takoma gida tana huci, Abba yasha dariya, danshi lamarin mahaifiyar tasu yanzu kallon rikicin tsufa kawai yake masa, inba rikicin tsufaba miye abin tada jijiyar wuya anan? Sunada damar hana yaran komawa gidajen mazajen sune?.
Shikam baba k'arami ma lokacin da take jarabar zuwa yay ya ra6a ta gefenta ya fice daga gidan.

Ai lamarin innaro sai ita🤣🤦🏻‍♀.

******************

A 6angaren Munubiya ma Alhmdllh, dukkan wata kulawa mama rabi'a tana tsaye akan 'yarta da jikokinta, sai zuba mata gata akeyi da k'yak'yk'yawar kulawa mai ban sha'awa.

Suruka ta gari dadi alkur'an💃🏻💃🏻😘😘.

★★★★★★★★★★★★

Mom dai da k'yar suka lalla6a Munaya itada Aunty Mimi ta amince ta shayar da yaran, suna sha tana kukan zafi kuma😹, sunsan zataji zafi tunda Na farkone, ga yaran a buk'ace suke dama, amma kukan datake yawuce Na zafi kad'ai, (basusan harda haushi Galadima bane😂🤭).
Mom data fahimci hakan saita fara lallashin da nuna mata muhimmanci hak'uri, su maza komai zasu iyayi akan y'ay'ansu, musamman ma shi da yake tsaka da d'okinsu yanzu, karma tabari irin wad'annam abubuwan su dameta, shima yafad'ane kawai amma zai sayo madaran”.
Itadai Munaya kai kawai take d'agawa amma batace uffanba, dan tagama Sanin Galadima da halinsa Na kafiyar tsiya da dagiya akan ra'ayinsa.
Bayan duk sunsha sun k'oshi Aunty Mimi tace ta kwanta ta huta kafin time d'in walimar yayi. ALLAH ya taimaketa maganin yasata barci kuwa, yaran Na gefenta suma suna nasu barcin, kowa cikinsa ya cika kenan😘.

Ajiyar zuciya Aunty Mimi ta sauke tana murmushi, tace, “Mom d'an nan naki bazai canja ba dai ashe? lamarin Sameer saishi wlhy, koda bayaso susha madarar saiya fad'a da harshe mai dad'i ba fad'aba”.
“Humm, kibari kawai, nifa harna fara murnar ya canja, Ashe yana nan yanda nasan kayana, yarinyar tanada hak'uri kuma wlhy, dan zama da mai halin Sameer saika daure, muma iyayen idan mun k'ureshi ba iya mana kawaici yakeba”.
Aunty Mimi tayi dariya, “papi ne mai tankwarashi kobai soba ai, idan yak'i bari abasu madaran dashi kawai za'a had'ashi, komin wadatar nono shayar da yara uku ba sauk'i ne dashiba, balle ita farin Shiga ma”..
Mom tace, “hakanma shine kawai mafita ai”.

***************************

*_8:15pm_*

Liyafar cin abinci tafara gudana a babban d'akin taro Na masarautar gagara badau, Munaya da y'an uku duk sunsha k'yau, hakama uban gayya Baban y'an uku Galadima, duk d'insu sunci kwalliyane cikin ainahin kayan sarauta, yaranma an nad'esu cikin k'ananun alk'yabbu. (Gado kenan🥰)
Kwai da kwarkwata Na gidan nan zaka sameshi a wajen, saidai marasa lafiya da wad'anda basa nan, mai martaba ma yana wajen, dan shine da Kansa ya shirya liyafar domin taya d'ansa murnar k'aruwa da kar6ar bak'uncin jarirai, yaran duk suna kusa dashi cikin d'an gadon da aka ajiyesu a ciki.
Kowa anan yake zuwa ya lek'asu, yamusu addu'a.
Yara sunsha addu'oi da k'yaututtuka ga iyaye da kakanni, abin zakkyau da birgewa.
Ita kanta Munaya tasha nata k'yautar.

( k'yauta da bajinta kan saka zama isashe a gidan sarauta, wannan babbar al'adace tamasu mulki a masarautun k'asar hausa, shiyyasa suke ado da ita akowanne motsinsu🤩👍🏻).

Tsakanin Munaya da Galadima babu uhum babu um-um, sai y'ar wullama juna harara (🤣nifa dariya suke ban), banga abin jin haushin junaba, duk da Na lura ita dama Munaya akwai haushi kaine ka jamin shan wahala😂, kaikuma Galadima k'asaita da jinkai ya sa kakasa fahimta balle kayi lallashi da kwantar dakai aji da y'an jariranka🤣.
To maji dai maga yanda za'a kwashe😹.

Sai 11 dai-dai taro ya tashi lafiya kowa ya kama gabansa.
Chapter 54 · 0% Book details