← Book details Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 76

Sashe 76

Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Misalin 8:30 na dare Galadima ke shiri bayan ya dawo daga sallar isha'i, yagama tsaf cikin k'ananun kaya da jacket d'insa wadda takai masa har gwiwa, ya saka safa har a hannunsa, cikin takunnan nasa na gwarzantaka ya fito, sashen Munaya ya nufa, sukaci karo a k'ofar d'aki zata fito a rikice, sauri tareta yayi ta fad'o jikinsa saboda kad'an yarage ta fad'i, k'amshin turarensa ya sakata shaida shine, ta share hawayenta tana kallonsa a rikice, shima kallonta yakeyi, Muryarta na rawa saboda kuka tace, “yalla6ai Abdurrahman sai kuka yakeyi, jikinsa ya d'auki zafi”.
Baice komaiba ya kama hannunta suka koma cikin d'akin, laraba da aunty Mimi na zaune, aunty Mimi tana zarema Abdurrahman kayan jikinsa za'a watsa masa ruwan d'umi kozaiyi shiru.
Zama yayi ya kar6e sa daga hannun Aunty mimi, ya fiddo wani kwali k'arami daga aljihun jacket d'insa ya bud'e, k'aramar kwalbar dake cikeda magani ya fiddo, ya d'iba maganin cikin tsinken da ake bama yara magani ya zubama yaran a bak'i, dak'yar ya shanyeshi.
Sudai sunyi jugum-jugum suna kallonsa.
Yunk'urin amai da yaron keyi yasaka Galadima d'agashi daga jikinsa dan kar yay masa, baimayi amanba, hakanne yasaka Galadima sauke ajiyar zuciya ya mannashi da k'irjinsa yana hura cikin kunnen yaron a hankali.
Tun yana kukan kad'an-kad'an ya koma ajiyar zuciya, sai gashi yayi barci. Kwantar dashi yayi kusada y'an uwansa ya lullu6esa.
Ya kalli aunty Mimi yana mik'ewa, “insha ALLAH zai sauka zaza6in”..
Yanda Aunty Mimi kebinsa da kallon tuhuma saiya janye idonsa yakama hanyar fita, da sauri tamik'e tabi bayansa a fusace. Dan Sauban ya sanar mata Galadima ya sashi kai yaron sashen mai martaba d'azun.
“Dakata Sameer”.
Cak ya tsaya yanajan hular rigar bisa kansa, amma bai juyoba.
“Sameer wai mike damun kankane haka? da zaka ringa wasa da rayuwar yaranka da kanka?”.
Lips d'insa ya ciza, ya juyo yana kallonta, amma ita bata ganin idanunsa saboda hular ta rufe, murmushin takaici yayi, yace, “Ni ba wasa da rayuwarsu nakeba aunty Mimi, komai kikaga nayi nasan abinda nakeyi, zuwa nangaba kad'an kuma zaku fahimci komai”.
“ALLAH yasa to, amma ni yanzu na zone muyi maganar komawar Munaya gida kafin mu wuce goben, tunda jirgin rana zamubi”.
Agogon hannunsa ya kalla, yace, “yanzu kam inada uzirin fita?”.
“fita? Inakuma zakaje a wannan daren?”.
Batareda ya tanka mataba yajuya yakama hanyar fita, saida yaje bakin k'ofa sannan yace, “Farauta”. yay ficewarsa.

Kasa motsi aunty Mimi tayi a wajen, sai maimaita Sunan Galadima kawai takeyi akan la66anta.

******

Tacan baya yabi shikam, hanyar akwai k'arancin mutane sosai, yana zuwa ta wani waje yagamu da wani Wanda ke sanye da irin kayan hadiman masarautar, rissinawa yay yabashi keys d'in mota. ya kar6a batareda sunma juna maganaba ya wuce.
Can sashen su Harun naga ya nufa, dukda tazarar dake tsakaninsu baiji tafiyarba, motar dake fake a wajen ya bud'e ya shiga ya zauna, zamansa da mintuna uku Harun yafito ad'an hanzarce, motar yabud'e seat d'in baya ya shiga ya zauna, cikin bada Umarni yace, lawandi muje, kasan d'an bala'innan yanada securitys dake kaimasa rahoto”.
Murmuahin gefen baki Galadima yayi yatada motar yafice daga masarautar................✍🏻

“Hummmm! Reader's harna sauke numfashi, babbar magana, yau dai ga Galadima ga Harun, sauran abinda zai faru kuma sai a buk 3 na raina kama”.
Miya faru da Abdurrahman lokacin da Sauban ya kaisa sashen gimbiya zulfah ne🤔? Yaya batun kama SD?, wad'anne sarakuna ne Galadima yake zargi? Kodai dama can Galadima yasan wanene Harun yabashi damane kawai?🤔, Yaya batun warkewar Abie da Auren Contract tsakanin Galadima da Munaya?, mi suke shiryawa itada Momma da suka damu da zuwanta wankan gida? Ko Galadima zai amince?”.

Yaya batun gano asalin innarsu Munaya? Da ita Munayar ta d'auki alwashi?.

Tofa wannan amsar dai duk zatazo a littafi na 3 kuma na k'arshe da izinin ubangiji, dukkan wasu tambayoyinku amsarku na cikinsa, zan had'a muku da albishirin zan dingayi a weekend rana 1, kodai asabar ko lahadi, kowacce rana nasamu dama aciki, dan buk 3 inason kammalashi ne a gaggauce saboda uzirin danake dashi insha ALLAH.

Ngd sosai da had'in kan da kuke bani, muje zuwa my guys⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀🥰🥰🥰🥰🥰🥰😍😍😍😍😍😍❤❤❤.

Barkanku da juma'a🙋🏻.

Musha weekend lafiya⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏼
Chapter 76 · 0% Book details