← Book details Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 76

Sashe 1

Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[7/3, 9:54 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*

*_Haske writer's asso...._*💡

*_♦RAINA KAMA......♦_*
_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻

____________________________

*_Dolene page d'in farko yazama sadaukarwa agareki MAMAN JUNIOR😭, ALLAH ya gafarta miki, ya raya abinda kika bari, ALLAH ya k'addara bazakiga k'arshen wannan littafiba. (Masoyan Raina kama kusaka wannan baiwa a addu'arku, ta rasu cikin azumi, kusanma k'arshe, member ce a group d'in raina kama, ALLAY ya yafe mata🙏🏻😭._*

_INA fata kunyi salla lafiya gaba d'ayanku, ALLAH ya kar6i ibadunmu. Ya yafe mana, yasa kar6a66iyar ibada mukayi🙏🏻😭._
Sai dai banci naman salla ba sosai, gashi banida d'inkin dallah🤦🏻‍♀🤥.

______________________________

~Book 2~ 👉🏻1⃣

.............Tunda mukayi maganar nan dashi banyi k'asa a gyuwa ba wajen dagewa da addu'oi wa mahaifinsa, ina buk'atar ruwan zam-zam, dan haka yau nashirya fad'a masa ya nemomin. tunda safe ya fice, dan haka bamuga juna ba.
Yauma dai haka Na tashi banida wata isashshiyar lafiya, Na tak'ark'ara nayi gyaran d'akin har zuwa falo, sannan Na had'a ruwa mai zafi nayi wanka dashi.
Ina cikin shiri najiyo sallamar Samha a k'ofar falon, rigar dana fara sakawa Na k'arasa, sannan nace ta shigo.
“humm Aunty gimbiya kina kallon kanki a mirror kuwa?”.
Cikeda mamaki Na kalleta sannan Na kalli jikina, nace, “kamarya?”.
Zama tayi a sofa tana 'yar dariya, sannan tace, “wlhy kinyi k'iba, sati uku kacal da zuwanmu India kin koma wata madam”.
Nad'an fiddo idanu waje, sannan Na harareta, “lallai Samha nagode da zagi to”.
“tab wlhy babu wani zagi gaskiya Na fad'a, halan Uncle Sam bai ta6a fad'a mi ki ba........”
Ta k'arasa Maganarta da d'ai-d'ai saboda shigowarasa d'akin da sallama ciki-ciki.
Suna had'a idanu ya watsa mata harara, hakan ya tabbatar mana da yaji maganar tata, da sauri tamik'e ta fita, Nikuma najawo gyalena na yafa sannan Na kallesa.
Saman sofar ya zauna ya dafe kai, kallo d'aya zaka masa ka karanci damuwar dake shimfid'e bisa fuskarsa.
“yalla6ai lafiya kuwa?”. ‘nafad'a cikin tausayawa’.
Shiru bai amsaniba, banyi zuciyaba nataka a hankali zuwa gabansa, durk'usawa nayi a gaban nasa, a d'arare nasa hannu Na najanye nasa dayay tagumi dashi.
Ya d'ago idanunsa da sukai jaa yana kallona. kasa jurar kallon cikin idonsa nayi, Na janye nawa gefe, cikin dakiyar zuciya nakuma fad'in “bakada lafiya yalla6ai?”.
Yanda nayi maganar a marairaice saiyaji yakamata ya fad'amin, kodan nuna damuwar danayi akansa......
Ganin yamin shiru nikuma saina yink'ura natashi ina fad'in “kayi hak'uri idan nashiga hurumin daba nawab......”
Bankai k'arshen maganarba naji tattausan tafin hannunsa cikin nawa.
Rintse idanuna nayi, saboda wani yarrr da tsigar jikina tayi, shima agaresa saiya lumshe idanu kawai. najuyo danufin zare hannun kawai ya fisgoni na fad'a saman kujerar, rabin jikinna duk yana a jikinsa, yayinda sauran rabin nake a kan kujera.
Bansan nawani lumshe idanuba saboda daddad'an k'amshin turarensa d'aya ratsa hancina zuwa magudanar jinina. shikuma ya sauk'e 6oyayyiyar ajiyar zuciya.
Ya karkato da fuskarsa inda tawa take a gefen kafad'arsa har inajin saukar numfashinsa saman face d'ina, mayun idanun nan nasa suka kuma shiga cikin nawa, na janye da sauri, sannan nafara k'ok'arin cire kannawa daga kafad'arsa.
Hannunsa na dama da nake jiki ya sak'alo ta bayana, ya maida kai na ya kwantar a kafad'ar tasa, cikin muryarnan tasa mai kama da anmasa tilas yace, “jikin Abie ne ya motsa, Ashe tun jiya basuyi barciba gaba d'aya, da safennan Akash yakirani yake sanarmin, nakasa kallon halin da mahaifina yake ciki Munaaya! Abie na yana cikin mawuyacin hali..” ‘yak'are maganar cikin zirarowar kwallar data cika masa idanu tunda yafara maganar’.
Wani matsanancin tausayinsa ne ya ratsani, duk jarumtar Galadima kaga yana kuka ai kasan lamari ya 6aci gaskiya, nima hawayen suka fara gudun fanfalak'e a kumatuna, tashi nayi zaune sosai, cikin wata jarumtar da bansan inada itaba nasaka hannu Na kamo hannunsa cikin nawa. Sai kawai naga ya zame sosai ya kwantar da Kansa bisa cinyata, tareda hard'e hannayensa a k'irji. duk da kujerar tama tsawonsa kad'an, dan ma Love's chair ce.
Kansa nafara shafawa a hankali, hawaye na zirara daga idona har yanzun.
Shikam idanunsa a lumshe suke.
Cikin tausasa harshe da tsantsar Nuna kulawa da tausayawa nace, “Yalla6ai kayi hak'uri, Abie d'inmu yana buk'ar addu'armu ne fiye da kukanmu, sannan itace jarabawarsa, wad'anda suka aikata masa hakan summa kansune, domin ALLAH bazai barsuba. idan ka amince akwai wasu addu'oi Dana Sani, Nina kakanmu ne yabama innarmu kafin yarasu, shine ta koya mana, mizai hana ka samo mana zam-zam muma mu farayima Abie su, Ubangiji gafurun rahimunne, babu abinda ya gagaresa, kuma shine yace mu rok'esa zai amsa mana”.
Tunda nafara maganar bai bud'e idonsa ba, nikuma ban fasa shafa masa kaiba. Saida nakai k'arshen zancen sannan ya bud'e lumsassun idanunsa dasuka koma launin jaa a kaina. yamotsa baki kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru.
Nima shirun nayi ban sake yink'urin yin magana ba, nadai cigaba da shafa kan nasa a hankali. ba akai 3minutes ba barci ya d'aukesa, sai numfashinsa danaji yakoma sauka a hankali.
Ajiyar zuciya na sauke kawai, na tsurama fuskarsa ido, yaune ranar farko dana ta6a nutsuwa namasa kallon tsaff, sosai yake kamanni da dukkan iyayensa, Abie da Momma, amma yafi tsananin kama da Momma gsky, duniyar tunani nafad'a batare dana fargaba, tausayin Galadima da families nashi yana cukurkud'ar ruhina, insha ALLAH nayi alk'awarin bada gudun mawa a duniyarsu har zuwa lokacin da aurenmu zai k'are.
kaina na jingina da jikin kujera, nima sai barcin ya kwasheni, dama bajin dad'in jikina nakeyiba.

********

Bayan anma Abie allurar datake temaka masa yin barci mai nauyi idan jikinsa yamotsa irin haka su Momma suka sami nutsuwa, dan yayi barci.
Sai alokacin hankalin Momma yadawo kan Neman Galadima, tabbas taga yafita hankali a tashe lokacin da Abie ke fidda numfashi a wahale, amma hankalinta bai koma kan Galadiman ba.
Aunty Mimi ta kalla tace, “Mimi ina d'an uwanki?”.
Itama aunty Mimi sai yanzu hankalinta yadawo ta farga babu Galadima d'in, hankalinta a tashe tace, “Momma inagafa ya fita, bara na duba”.
Bata jira cewar Momma ba tafito daga d'akin da sauri. ganin babu Galadima a wajen hankalinta yak'ara tashi, fitowa tayi harabar asibitin tana tambayar securitys d'in wajen.
d'aya ya sanar mata ya fita a rikice gaskiya, dan suma sun nemi su taimaka masa amma baima tanka musuba.
Innalillahi tashiga ambata. Bata koma wajen Momma ba tashiga mota tanufo gidan.
Ta iske Samha a falo kwance, ko sauraren sannun datake mata batayiba tace, “k ina Uncle d'inku?”.
Samha tace, “yana sama Mummy”.
Da sassarfa ta haye step's d'in, itadai Samha da mamaki taringa binta da kallo.
Ko knocking bata tsaya musuba ta turo k'ofar ta shigo.
Ajiyar zuciya ta sauke dan ganin Galadima kwance, kansa bisa cinyar Munaya, hannunta d'aya na bisa Kansa, yayinda shikuma yarik'o d'ayan hannun munaya ya had'e da nasa ya d'ora kan kirjinsa, suduka barci ya kwashesu a haka. cikin sand'a ta juya ta fita taja musu k'ofar tana share hawaye dayima ALLAH godiya d'aya bama d'an uwanta mace tagari wadda take kulawa dashi. inda dane kafin yayi aure shima sai ciwonsa yatashi saboda damuwar dazai saka Kansa akan motsawar jikin Abie, amma gashi yanzun yasamu mai kwantar masa da hankali, suma kuma nasu ya kwanta suji da Abie kawai.
Momma ta kira ta fad'amawa dan hankalinta itama ya kwanta.
Momma harda hawayen farinciki, tana godema ALLAH.
Aunty Mimi bata zaunaba suka koma asibitin itada Samha da tace zata bita, itama sai yanzu takejin jikin Abie ya motsa.

*************

A k'alla munyi barcin 47minute's, Galadima ne yafara farkawa, ya bud'e idanunsa a hankali, hannuna dake rik'e a nasa yafara kallo, kafin yad'ago ido zuwa kaina, yamin kallo kusan na 2minutes sannan yad'an motsa da nufin gyara kwanciya, saina bud'e idona, ido muka had'a, kowa yay saurin janyewa cikin basarwa, hannuna dake kansa na cire, sannan nazame Wanda yarik'e d'in, dan wata matsananciyar kunya ce kuma takamani.
Shima sai ya tashi zaune sosai, a hankali yacemin “thanks”.
Daba kusa dashi nakeba ma bazanjiba. Bance komaiba, shima bai sake cewa komaiba yamik'e tsaye. takalmansa kawai yacire ya d'auki jallabiya a wardrobe d'insa yashige bayi.
A hankali na sauke ajiyar zuciya, tareda janye idona daga k'ofar bayin, komai banceba nakuma zamewa saman kujerar na kwanta.

Ya d'auki adadin wasu mintuna masu tsawo kafin yafito sanye da jallabiya ruwan toka, da alama wanka yayi, kallona yayi batareda yayi magana ba ya nunamin agogon dake ajiye a drowan gefen gadon alamar time d'in salla yayi.
Kaina kawai na girgiza na mik'e, zuciya ta na mamakin hali irinna Galadima.
Shikam turare kawai ya d'auka ya fesa yafice salla.

★★★ ((★))(())((★)) ★★★

A gidanmu kam hankalin mamansu yaa hameed da Zarah a tashe yake, dan babu Sa'eed babu labarinsa, kira Zarah tamasa yafi 50 amma yak'i d'agawa, ta tura massages babu reply, bata aikin komai sai kuka, ga ciki.
Abbanmu kuma jin sanadin sawowar tata gida yace bazai kira Alhaji halliru ba har sai Zarah tafad'i ainahin gaskiya, danshi bai yarda ba itace ta d'auki kud'inba..
Innarmu dai dasuke zagi suna kallonta mak'iyarsu batakai komaiba itace tashiga lalla6a Abba damasa magiya.
Itama da farko buris yay da ita, saida yaga tanace sannan yace, “wai kekam Ai'sha miyasa kika damu kankine? kinbi kin damu da lamarin wad'anda basu damu dakeba, na tabbatar da Munaya ko Munubiya ke cikin wannan halin su murna zasuyi a gidannan”.
Murmushi innarmu tayi, cikin kwantar da murya tace, “Alhaji ai daga Zarah harsu munubiya duk d'ayane a wajena, domin kaine mahaifin Zarah, dukkan abinda kuma yakasance naka ina kaunarsa fiye da zatonka, a duba lamarin yarinyar kodan abinda ke gabanta, ba'a son mace mai ciki da shiga tashin hankali, muyima tufk'ar hanci tun munada sauran dama, basai Abu yayi tsamariba kuma muce zamu nemo mafita, hannunka baya ru6ewa ka yanke kayar alhaji, dan ALLAH kayi hak'uri kaji”.
Jawota yayi jikinsa ya rungume yanamai saka mata albarka da aminta da buk'atarta na kiran senator halluru da safe insha ALLAH.
Innarmu tamasa godiya itama.

**********
Chapter 1 · 0% Book details