← Book details Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 25

Sashe 25

Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kiyi ha
uri karki ce a'a Bilkisa.

A taimaka ayi hakan zaifi alkhairi, dama sabida Shamwila ne kika ce ba zaki zauna ba.

To yanzu bata gidan."
"Aikina da gidana in yi Yaya dasu?" Ta jefo mishi tambaya.

"Aiki zan sama miki wani a Kaduna.

Gidan ko haya sai ki saka.

In kuma kinason in siya in caske miki ku
inki zan siya, ni nasa hayar" A ta
aice dai Kaila yaci galabar shawo kan Bilkisa, dan Allah ya yi shi da iya tsara mace, da sarrafa harshe wajen lallashinta. ta amince zata dawo Kaduna.

Amman sai ta samu aiki a Kaduna kafin ta baro Zaria, sannan gidanta da take ciki ya siya ya bata ku
inta a haka suka rabu.

Shanono:.

Kai tsaye kotu na nufa, nayi shari'ar dake gabana, amman na kasa gabatar da sheduna dukka, na ro
i alfarma a zama na gaba zan gabatar dasu.

Al
ali ya
age lokacin zaman zuwa wani lokacin.

A girguje na shige motata na bar cikin kotun.

Habiba Bala sai kiran wayata take ta faman yi.

Fur na
aga wayarta domin bansan me zance mata ba.

Ina kuma tsoron ita me zata ce mun, daga
arshe ma wayar na kashe gabaki
aya.

Ina shiga gidansu Inno na tarar da tulin kayan abinci kamar za'a bu
e shago.

Yara suka taryoni da murnarsu, Sani da Dauda basa nan sun fita.

Ige ce tai mun bayanin kayan da ku
i da Kaila ya bayar na batun karatun yara.

Kar
ar ku
in nayi kawai na shige cikin gida.

Haka nadinga yin komai sukuku babu kuzari a jikina.

Ga fa
uwar gaba da naita fama dashi.

Tunani yaimun yawa, na rasa abinda ke mun da
i sam.

A daren wannan rana saina tsinci kaina da kasa bacci sam.

Haka na wayi gari idanuna sunyi zuru_zuru.

Takwas dai_dai na shiga office.

Amman na kasa yin aikin kirki, sai in yi shiru ina tunani, haka naita faman yi.

Ko Oga Rashid sai da yasa akai mishi kirana yake tambayata meke damuna.

Nace mishi babu komai bana jin da
ine kawai.

"Muje in kai ki asibiti, ya zaki zauna da ciwo har kizo office kuma a haka, no muje asibiti daga nan sai in kai ki gida" Bani da za
i ni kaina nafi sha'awar in tafi gidan in
an kwanta, ga jiri da ciwon kai ya tasarmun, halamu Bp na ya hau.

A motata muka tafi, shi ke tu
awa ina zaune a
angaren me zaman banza, idona a lumshe.

Wani asibitin ku
i ya kaini suka dubani, gwajin farko suka fa
amun jinina ne ya hau ina bu
atar hutu, da dena yawanta tunani.

Magunguna suka bani muka fito.

Oga Rashid da kwatance ya kaini har
ofar gida..

Nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi "
"Babu komai.

Dan Allah ki sha magungunanki ki kwanta kiyi bacci.

Sannan in nazo da daddare kya bani labarin meye musabbabin wannan tashin hawan jinin.

Allah yasa ba kalaman dana furta miki na asirin zuchiyata bane ya jefaki cikin wannan yanayin ba.

In kuwa shine a shirye nake da in janye kalamina, muddin zaki zauna lafiya.

Hakan yafi mun daidai, ki shiga gida " Godiya na kuma yi mishi, muka fito tare.

Keyn motar ya mi
o mun, tare da yi mun sallama ya wuce.

Ni kuma na bu
e gidana na shiga, ina jiyo surutun su Sani da su Inno.

Ina shiga na wuce ciki na sha magani na kwanta.

Amman na kasa bacci na kuma kasa dena tunani.

Yanzu shikenan JeGa ya zubar mun da mutumcina a idan iyayenshi,
ila har a idanun Habiba Bala ma.

Dan nayi imani wannan lamarin bazai ta
a yi ma Habiba Bala da
i ba.

Domin ita kanta hakan ka iya sawa ta fuskanci matsaloli a gidan auren nata.

Wasu ma tunani zasu yi baki muka ha
a da Habiba Bala dukiyar gidan muke son handamewa.

Wadannan abubbuwan su nake tunawa in ji hankalina yayi
ololuwar tashi.

Kiran sallar azahar ne yasa na tashi nayo alwala na gabatar da salla.

Ina idarwa na koma gado na kwanta.

Ba'a jima da idar da salla a masallaci ba.

Na jiyo muryar Sani da Dauda a Falo suna kiran sunana.

Izinin shigowa na basu.

"Umma lafiya kika dawo kika kwanta.

Umma baki da lafiyane ko Babane?

Dariya nayi nace.

Baba kuma, me Babanku zaiyi mun Sani?

Aikine babu da yawa a office shi yasa na dawo.

Amman da yamma akwai inda zani." Zama yayi a bakin gadon yace.

"Umma inason gobe zan koma makaranta.

Baba yace zai yi
ari in samu tranpa karatuna ya dawo Kano.

Kinga shikenan sai mu dinga tafiya shagon
inki da Yaya nima in koya.

Nifa Umma ku
i nake so inyi sabida ke kawai.

In siya miki motoci, da gidaje, duk azumi ki je kiyi umara, in bu
e miki gidauniya.

Kinga umma ai banci ta zama ba.

Duk wata wahala umma sai ta riki
e ta koma arziki da izinin Allah.

Wa
anda suka wula
antaki sai sunci arzikin abinda kika haifa." Wannan kalami na Sani ya sani farin ciki da samun kuzari sosai.

Gaskiya Sani shi
in na dabanne a cikin yarana.

Nagode Sani.

Allah yai ma albarka ya baku abinda kuke nema, ya cika muku burukanku da Alkhairi.

Nagode sosai.

Ina su Sulaiman suke ne?" Dauda yace.

"Suna can suna koyama su Indo karatun boko.

Yanzu suka dawo makaranta.

Su Amina kuma basu da aiki sai zaulayar Baffa.

Muma muna son mu shiga gidan Umma ne mu gaisheta.
azu ma ta kira da safe tana son yin magana dake, to lokacin kin tafi wajen aiki" Duk walwalar da nake ciki sai na nemeta na rasa, gashi ban isa ince kar suje ba zasu tuhumeni.

Dole haka sukai mun sallama suka tafi.

Misalin
arfe biyar da rabi na gama kintsawa tsab na fito.

Sai da na kama hanyar Munjibir kana na bu
e wayata.

Kamar ko jira yake yi sai ga kiranshi ya shigo wayar.
agawa nayi na kara a kunnena.

"Hello ranki shi da
e ina cikin Munjibir kamar yadda mu kai al
awari.

Ina fatan baki mance ba ko?" Numfashi naja.

Ina hanya nima"
"To shikenan Allah ya tsare miki hanya ya kawo mun ke lafiya"
Ameen" Na datse wayata na ci gaba da bin santsi har zuwa Munjibir.

A wajen da aka tanada dan ajjiye motoci na ajjiye motata na suri jakata na fito.

Takawa nake yi a hankali, ina
an ware idanuna ko zan hangoshi.

Ga
an mata da samari wasu a zaune a kujeru farare, wasu a zaune a kafet, wasu ma a tsaye suke,yayin da wasu suke tafiya irina.

Yanayin garin babu rana yayi lub, sai iska sassanya da take busowa gwanin ban sha'awa.

JEGA na hango cikin shigar manyan maza.

Ba
ar shadda ce a jikinshi
inkin malum_malum, hularshi da takalminshi duk ba
ene, agogo da tabarau
in idanunshi kuma masu ruwan zaiba ya saka, kalar surrfanin dake jikin kayan nashi kenan.

A gaskiya yayi kyau sosai,
asumbarshi tasha gyara Masha Allah.

Tun daga nesa yake
aremun kallo, tare da yi mun murmushi har na iso inda yake a tsaye.

"Kinyi kyau marar musaltuwa.

Ke
in kyakkyawace, uwa uba gaki da aji, da sanin daraja,, da kimar kai.

Kar in cikaki da rashin kunya muje ga kafet na tanadar mana." Bayanshi nabi har zuwa kan kafet
in.

Waje na samu na zauna muna fuskantar juna.

JEGA bari in baka asalin cikakken tarihin rayuwata tun daga farkon soma sanin kaina izuwa yau da nake gabanka a matsayin Barista.

Wannan itace ka
ai hanyar da zai sa ka ha
ura da neman aurena kabar zuchiyata ta samu salama.

Rayuwata a cike take fal da tarin
alubale, da jarabawa wani kan wani.

Labarina ya samo asaline daga cikin
aramar hukumar shanono dake nan jihar kano.

Cikakken labarin rayuwar shanono da irin jarabawar data samu a gidajen aurenta zai zo muku a ciki book 3 da izinin Allah wanda ni kaina bansan yaushe book 3
in zan soma sakar muku shi ba.
an samu matsalar ciwon idanu, kuma an
aurani a kan magani, da izinin Allah da zaran komai ya daidaita zaku jini da book 3.

Ananne Shanono zata fe
e mana biri har wutsiya.

Shin ya hala
ar Jega da Shanono zata kasance, kuna ganin JEGA zai iya samun zuchiyar shanono kuwa?

Ko dai shanono gidan tsohon mijinta Kaila zata koma ne?

Ga Oga Rashid shima fa yana mutuwar son shanono da zafinshi yazo.

Duk zamu ji yadda zata kaya da izinin Allah.

Ki fa
i ra'ayinki dangane da littafinnan.

Kai tsaye wanne irin darasi ke kika koya a cikin littafin?

Ina jiran amsarki.

Masu karantawa a batu, kuma ina yinku sosai.

Nagode da
auna.

MRS BUKHARI taku ce a ko da yaushe.

Sai mun ha
u a book 3
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
TECNO LD7
WPS Office
Normal
Times New Roman
Times New Roman
Calibri
Calibri
!%),.:;>?]}
$([{
fc4ff4926db249a5bcabfc5eca75f088
Chapter 25 · 0% Book details