← Book details Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 25

Sashe 18

Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali na mi
e jikina babu laka sam.

Ina zuwa tsakiyar filin naci karo da Jega, da wani irin mayen kallo mai wuyar fassarawa ya bini.

Harara na daddage na dalla mishi, shi kuma ya sakar mun murmushi"
KAILA:
Mutuwar tsaye yayi kawai.

Ya bi Shanono da yaranta da kallo, yabi takun da shanono take yi cikin tsari da gogewa irin ta manyan mata, wayayyu wa
anda suka san ciwukan kansu.

Murmushi ya saki.

"Wacece wannan Apple da har ta
auke maka tunaninka ka mance kanka, a gabana kake ma mace mayen kallo haka, wai dama haka kake?

To da kake kallonta sakin
aya daga cikin matanka zaka yi ka maye gurbi da ita ko yaya?

Gashi naga har Sani ma ya santa, meke faruwane?" A jejjere take tuhumarshi tare da kafeshi da idanuwanta da suka koma jawur dan haushi.

Shi kuma Kaila cikin rashin mallakar kai yace.

"Gyatumar su Sani ce, uwar
anace Shanono" Ya bata amsa tare da soma tafiya,
amshin shanono yananan daram a hanyar data wuce yana gauraye da iskar da Kaila yake sha
a, sai lumshe idanu yake yi.

Salima kuma mamakine ya cikata da ganin Shanono ita a tunaninta ba haka zata ga shanono ba, domin taji jita_jitar ance iyayenta mabaratane, amman dai bata da wani labari dangane da
azantar da aka dama.

Jikin Salima yayi sanyi, dan da a tunaninta tafi ko wacce mace a idanun Kaila, ganin Shanono ya ture mata wannan tunanin kuma ta mi
a wuya cewar Shanono ta fita nesa ba kusa ba, kuma har wayewar da take ta
ama dashi Shanono ta kere mata.

Uwa uba yanda take fitar da wani irin fitnannan
amshi mai sa nutsuwar zuchiya, dan har zuwa lokacin hancinta cike yake da
amshin turaren da Shanono ta bar musu a matsayin abinda zai ta buga musu kawunansu.

Da jan
afa Kaila da Salima suka shiga cikin holl
in, tare da samun wani teburi suka zauna.

Ashe teburin dake kusa da su Sulaiman ne da su Amina.

Sai ji Kaila yayi Balaraba tace.

"Baba" Da sauri ya juya, ido hu
u yayi da Sani, yaga yaron na mishi wani irin kwarjini, da sauri ya
auke idanunshi akan nashi yana harararshi.

Ya yafito Balaraba da hannunshi.

Mi
ewa tayi tazo kusa dashi.

"Kina da number ummanki?" A kunne yake tambayarta, gya
a mishi kai tayi halamar e tana dashi.

"To shikenan zan kar
i number a wajenki, amman kar ki sake ki fa
ama kowa.

Inaso in dawo muku da ummanku ne, kuma ku zauna a wajan mamanku" Sani idanunshi a kansu yake, yana
issima yanda zai ma Balaraba.

Saketa yayi ta koma wajan zamanta, Salima ta harareshi, yayi tsam yana kallonta yama mance da shakkarta da yake ji yau sam.

Juyawar da zai yi ya hango Shanono tana sakkowa daga inda Ango da Amarya suke, sai dariya take yi.

Ganinshi yayi a tsaye kamar soja yana
arema takun Shanono kallo.

Sai da Salima ta finciko hannunshi ta dangwarar dashi a kujera, ta nuna shi da
an yatsa.

"Bari kaji nafi
arfin kai mun wula
anci wallahi, me akayi akayi ka?

Namiji sai shegen kallon matan tsiya kamar wani bunsuru.

Ji yanda kake kallonta ka mance da ni a zaune a gefenka.

Ina zaka sata to in ta amince ma zata dawo kan yaranta?" Harara ya sakar mata.

"Lallai Tanjirin.

Baki san waye Shanono a cikin rayuwata bane.

Baki san a yanda shanono ta tsinceni mu kai aurenmu na rufin asiri bane.

Wanda nayi imani da kece zaki tsinceni a irin yanayin da shanono ta tsinceni ba zaki ma yarda ki saurareni ba.

Kuma bance miki dan wani abun nake kallonta ba.

So nake mu gaisa a matsayina na wanda mu kai rayuwa tare a baya, yaranmu bakwai tare da ita.

Ai kuwa ta riga ta zama ni, na zama ita" Kallonshi ta yi ta sake mayawa.

Kana Tace.

"Zaka ga buyagin da zanyi maka wallahil azeem.

Bari in je wajan su Yaya Hama, in ka ga dama sai kaxo ku gaisa"
Sani:
Balaraba na komawa yace mata.

"Baba zai dawo mana da ummanmu ko?

Nafi kowa farin cikin hakan" Ya fa
i hakanne domin ya nuna mata gaba yake da ita, dukan cikinta yayi.

Abinka da yarinta nan ta hau
arin zance ta kwashe yanda su ka yi kab da Kaila ta fa
i ma yayyenta.

Amina ta harareta tace.

"Wawuya kinaso ummanmu ta dawo kenan Baba yaci gaba da dukanta yana zaginta a gabanmu ko?" Sani yayi carab yace.

"Umma da fa
auke ku zata yi a hannun matan Babanmu, ta mayar daku Kano wajenta cikin sabon gidanta.

Hankalinmu a kwance.

In Umma taji labarin ke kika ba Baba number ta ya kirata.

To a Kaduna zata barki wajan Umman Musa, mu kuma mu koma can.

Duk sai Balaraba tabi ta ru
e.

Dauda ya harari Sani yace.

"Wai me yasa kake yin duk wannan abunne?

Ka ba Innata dama ta kwaci kanta a wajen Baba mana, ni ina ganin wannan fa
an nasu ne.

Akwai ga
ar da zamu iya shigar mata ko ya kace?" Sani
an duniya dan yafi Dauda gogewa sosai yace..

"Ba za ka gane bane.

Ai barinsu su yi doguwar magana ka iya rushe mun
udurina.

Wallahi Allah in har sai Umma ta dawo hannun Baba misali zai ci gaba da numfashi.

Tsaiwar numfashinshi yafi mun aikhairi ni.

Umma taci wuya fa Yaya.

Ta wula
anta ta
anta sosai" Take hawaye ya soma gudu a kumatunshi, baya
aunar abinda zai tuno mishi da rayuwar ummanshi a hannun mahaifinsu.

Shanono:.

Anata sha'anin biki, ki
e_ki
e sai tashi suke yi, Amarya da ango suna zaune sai li
i ake yi musu.
awayenmu an ha
e kai seti_seti sai hira da shewa irin da duniya tai da
innan su ke yi.

Ni kuma gaba
aya maganganun Jega sai nu
usar
asan raina take yi.

Ni ba'a ta
a rainani irin na yau ba.

Ni yaro
arami haka zai nemi tsarani, ta ya yayi sake zuchiyarshi tayi wasa da tunaninshi?

Yaro yarone ko da kuwa
an giwa ne.

Ta wani bangaren in na tuno da irin ru
ewar da Kaila yayi a kaina sai inji wani farin ciki.

Ko banza ina da abinda zan iya ma Kaila
walele dashi,
walele irin na har abadan kuwa.

Dan kuwa nasan Kaila babu shi babu runtsawa a daren yau
innan.

Haka taro yaci gaba da gudana cikin farin ciki da nisha
i.

Anci ansha an goge wuya abun ba'a cewa komai.

Mun yi rabon kasko da tureren wuta, harda ashana, wanda Sabira tai mana odarsu a wajan Mrs Bukhari gidan
amshi.

Kowa ya samu, har sai da aka koma da rogowar kayan rabon, tsabaragen munyi komai a wadace sosai.

Bayan taro ya tashi Sani shi da kanshi ya zo ya fito dani daga taron, ya sani a cikin motarshi, Kaila yana tsaye yana
are mana kallo, amaryarshi kuma tana gaisawa da
awayenta ne ko
an uwanta ne ohon mata dai.

A gidan baya na zauna ina sauke ajjiyar zuchiya.

Kaila ne ya kirayi Sani yace yaje.

Su Amina kuma suka shiga motatata su da Yayansu Dauda.

Bansan dai mai Kaila yake cema Sani ba, amman koma meye nasan yana da nasaba da abinda ya faru
azu, dan naga sai fa
a yake yi kamar zai daki Sanin.

Ya dai gama borin kunyarshi Sani yazo muka bar wajen, ina ganin Kaila yanda yake bina da wani mayen kallo, naga har ha
iyar yawu yake kamsr wani tsohon maye.

Sani baice mun komai ba tunda ya shiga motar, sai gudu yake shararawa dani, ni kuma jin shi shiru sai hakan ya ta
ani, ya saba da zolayata da kuma yi mun hira dan ya faranta mun.

Bansan Sani kuka yake yi ba har sai da muka iso
ofar gidan su Habiba Bala bayan na fito.

Idanunshi sun ka
a sun yi jawur dasu, hawaye sai zuba yake yi a kumatunshi.

Take hankalina ya tashi ainun.

Sani kukan me kake yi haka, me Kailan ya fa
a maka?" Na tambayeshi a jere, dai_dai shigowar motar su Dauda.

Ka share hawayenka kar ka
aga ma
an uwanka hankali.

Sani bazan ta
a iya bama Kaila dama ko wacce iri bace.

Ba kaila ka
ai ba, ni
innan da ka ganni babu batun aure sam a gabana, ina da tarin burika masu girma da nake son ganin na gabatar.

Yanzu haka inason in ware office a cikin gidana na sauraren koken Zawarawa, da matan da suke shan wahala a gidan mazajensu.

Dan haka kama dena damun kan ka kaji ko?" Murmushi yayi mun yace.

"Nagode ummata ina alfahari da kasantuwata a matsayin
anki.

Ina kishinki umma." Dariya mu ka yi dukkanmu.

Dauda da
annenshi suka
araso.

"Wai Innata shi wannan yaron nunawa yake yi yafi kowa sonki ne?

Nifa ban yarda ba wallahi duk bugun zuchiyata da sonki yake bugawa Innata.

Sani naga yana shirin ture mun matsayina." Su Amina suma su ka ce ai suma basu yarda ba.

Tuni yarana ababen alfaharina suka
ebe mun damuwar dana shiga.

Ina dariya nace.

Dukkanku Umma tana sanku.

Kune farin cikinta kuma, Dauda kai da Sani zaku je Jos gobe su Amina su harha
o kayansu, ku kawo mun su Kano.

Zan ci gaba da ri
esu" Tsantsar murna da farin cikin da na gani a idanunsu bazai musaltuba sam.

A guje su Amina da su Sulaiman suka shige cikin gidan.

Dauda kuma ya ja Sani zuwa gidan abokinshi a ma
ota, acan zasu kwana.

Na juya zan shiga ciki kenan na ji an ambaci sunana.

"Barista Shanono" Cak na tsaya ni ban shiga ba, ni kuma ban juyo ba"
Kaila:.

Tunda suka shiga
akin hotel Salima take huhhura hanci,
iris take jira kaila yayi mata magana ta sauke mishi kwandon ruwan masifa da bala'inta.

Tunda ba raga mishi take yi ba.

Tun a mota take sa ran soma bata ha
uri gami da rarrashinta amman abun mamakin bai ce da'ita komai ba har zuwa yanzu.

Nutsuwarshi da tunaninshi ma baya tare dashi.

Sakkowa tayi daga kan gado ta ja dogon tsaki ta shige ban
aki.

Da idanu ya bita cike da karantar yanayinta.
Chapter 18 · 0% Book details