← Book details Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 25

Sashe 22

Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da suka kama hanyar Kano Kaila ya samu salama."
Barrister Shanono:.

Tun sassafe na shirya tsab cikin shigar aiki, yau ina da sabuwar shari'a mai zafin gaske.

Sani ne ya dafa mana tea ya soya mana wainar
wai.

A gurguje naci, nai musu sallama na fita.

Sai da na shiga gidan su Inno muka gaisa kafin na nufi chamba.

Ina shiga na tarar ana shirye_shiryen meeting.

Misalin
arfe takwas na safe duk muka hallara a meeting holl, duk muka doka wayoyinmu a silent dan gudun kar a kira ana tsakiyar tattaunawa.

Oga Rashid ya soma magana.

"Am ma
asudin wannan taron, na taraku ne domin mu tattauna akan wasu matsaloli da suka shigo mana wannan Chamba.

Tun farko dana bu
e Chambata, na bu
etane domin in tallafi
ananun baristoci da suka gama karatunsu na low suna yawon neman aiki.

Gaskiya dokin
arfe na kafata ne domin gaskiya da gaskiya.

A cikin baristocin da ni nake dasu, an samu wa
anda ake ha
a baki dasu ana mur
e ma masu hakki hakkinsu, akan abun duniyar da bai taka kara ya karyaba.

Ni tsohon lauyane nasan yanda harkar take, nasan yanda ake mana tayin kudi, nasan yanda ake mana barazana da ranmu.

Akwai wara shari'a dana gabatar shekaru talatin baya, wallahi sanadiyyar wannan shari'ar har makaranta akabi mai
akina aka saceta, tun duniyarma na kwance.

Akace in ban
aryata duk hujjojin dana kafa ba wallahi sai sun kasheta.

A lokacin na shiga tsaka mai wuyar fita, gashi
angaren dana ri
a rauni garesu ni suka ri
e a matsayin sandar jagoransu.

Da dabara dai aka sako mun matata, nai musu al
awarin zan
aryata kaina.

Bayan sun sakota aka gama shari'ar ba tare da na yi abinda su suke so ba.

Amman har biyoni su kai a titi suka harbeni a hannu.

Banda motoci, ko gida da za'aima tayinsu.

In muka ce zamu ru
u da irin wannan tayin wallahi zamu cutar da kanmu ne.

Sannan kun rage
wazo da himma akan aiyukanku.

Barista Shanono, da Barister mai Hula ne suka fi kowa mayar da hankali akan aiyukansu.

Kuma in suka nace ma kes sai sun yi nasara.

Sannan suna da hanyayo da salon bincike sosai, ina bibiyar aiyukan kowa.

Wannan shine ma
asudin taron namu.

Kuma akwai sammaci da muka yanka ma mutum 6, zan rarraba muku aikin in sha Allah.

In da me magana sai yayi" Mun fi awa uku muna abu
aya, daga bisani ya Sallamemu taron ya watse.

Da zan fita Oga Rashid yace in na rarrage ayyukana in zo in sameshi zamu yi magana.

Ina zama a teburina wayata ta shiga haske dake a silent take.

Sabuwar number na gani.
agawa nayi na kara a kunnena.

Sai naji muryar mijin Habiba Bala.

"Barista shine jiya kika gudu ko sallama babu ko?" Ajjiyar zuchiya na sauke da naji muryar tashi washar da'ita.

Na yi tunanin Jega ya kira mun ruwane.

Ango da kanshi, barka da safiya ya kwanan Amaryar?" Da dariya yace.

"Gata ita tace in kirawoki ma" Mi
a mata wayar Yayi.

"Shine kika gudu ko Shanono dan wula
anci, su Sabira sai nemanki suke yi."
Yi hakuri kira na samu na gaggawa
awata kuma nasan in dai nace miki zan tafi ba lallai ki amince ba.

Ya kin tashi lafiya?" Dariya kawai tayi mun tace.

"Zaki zo ne in kin baro office akwai labari fa" Nima dariyar na mayar mata nace.

To zan yi kokarin hakan.

Yaranki fa sun dawo hannuna, jiya ma Kaila ya kira ta inda yake shiga ba tanan yake shiga ba.

In nazo ma za
a musu makarantar da kika ga ta dace dasu, sai nazo, Sabira sun koma ne?"
"Tun yaushe, taje ma gida ta dubo su Inno.

Tasan kin tara aiki a office ne shi yasa ma bata bi ta kanki ba, sun kusa shiga Jos ma ai yanzu" Sallama nayi mata, ina sauke wayar kiran Sani ya shigo.

Sani ya akayi?"
"Umma su Babane suka zo, suna cikin gidan su Inno, Baffa ne yace in kira ki, in ba wani abun kike yi ki zo yanzu." Gabana ya yanke ya fa
i ras a sanyaye nace.

To ganinan zuwa yanzu Sani.

Har zan kashe wayar yace.

"Umman kin mun al
awarin ba zaki koma hannun Babanmu ba, kar ki manta da wannan.

Ni bazan ta
a yarda ki koma mishi ba umma" murmushi nayi dan in kwantar mishi da hankali.

Babu ma wannan zancan Sani, kaji ko kasha kuruminka ganinan zuwa" Wayar na kashe Mai Hula ta kalleni tace.

"Wata matsalarce?"
E yarane nasa aka kwaso mun suka dawo hannuna, shine Babansu ya biyo sahu.

Baffa ne yace yanason ganina.

Bari in je sai na dawo" Fita nayi zuwa ofishin Oga Rashid.

Kwankwasawa nayi ya bani izinin shiga.
was_
was_kwas na shiga, kujera ya nuna mini yana murmushi.

Nagode sosai Sir.

"Ai ya zame mun wajibi in baki waje zama ni fa na gayyaceki" Katseshi nayi.

Dama a gidane mahaifina yake nemana akwai abun da ya taso ne, shine nake neman izininka" Da mamaki ya kalleni yace.

"Dama tare kike da mahaifanki a garinnan?"
A'a dawowa dai su ka yi, da Bama tare sir" Murmushi yayi yace.

"Allah sarki, to a gurguje nima bari in yi amfani da wannan damar domin in fallasa miki asirin zuchiyata, tunda kin
i ki fahimci inda na dosa sam.

Kaina nayi sauri na sunkuyar gabana ya shiga harbawa Fat_fat_fat.........

Team Kaila #
Team JEGA #
Team Oga Rashid #
Ku futo.

A ganinku wa ya fi cancanta Shanono ta mi
a ma zuchiyarta a karo na shida ?.....NA FA
O DAGA BENE.....

NA ZARCE RIJIYA
BOOK 2
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN
AMSHI
GAWURTATTU UKU
LAMBA TA 14
"Barista na jima sosai ina rainon jaririn sonki a zuchiyata har yayi girman da nake kasa mallakar kaina.

A mafiya yawan lokuta, zagaye da nake yi zuwa ofishoshin ma'aikata, ina yine domin in ganki in ji sanyi.

Ina sonki Shanono, Allah yasa babu wanda ya rigani, dan ni tun ina matashi bana iya ha
a soyayyar mata biyu.

In kuma naje wajen mace na ganta tana kula wani saurayin to jaye jikina nake yi.

Dan ni in inaso ban iya so ba, haka in abu ya fitar mun akai ma haka nake.

Da fatan zaki bani lokaci in zo in sameki a gida mu
arashe maganar?" Ni dai tunda ya soma jawabi gabana ke aikin bugawa, abun wani iri nake jinshi, duk da nasan Oga Rashid ya jima yana tattalin sona, amman ni fa ba auren da zanyi magana ta gaskiya"
Nagode Sir, inaso ka bani lokaci zanyi nazari akai" Da murmushi ya dubeni yana wani numshe idanu yace.

"Zuwa yaushe kenan?

Kar ki sakani cikin zulumin tare
da taraddadin me zai fito bakin ki.

Domin rashin amincewarki zai iya jefa ni cikin wani hali mawuyaci.

Na da
e ina rainon sanki, yayi girman da rasaki zai iya kassara kuzarina" Ru
ani na shiga mai girman gaske, nama rasa bakin magana, bance komai ba har ya sake magana.

"Zuwa yaushe zan jira amsar taki Barista, ba zaki tausaya mun zuwa ko gobe bane in zo gida in sameki mu tattauna ba?

Ai mun wannan alfarmar, ban ta
a neman alfarmarki ba, yau
aya na ro
a aimun dan Allah "
aureni da jijiyoyin jikina yayi tamau, Oga Rashid tabbas mutumin kirki ne, lokacin da nazo neman aiki, ma'aikata sun cika Chambarshi, amman da yaga macece ni mai rauni, a hakan ya nema mun ofishin da zan zauna, ya
aukeni aiki.

Tunda dai ya nemi alfarma ya kamata in mishi.

Amman bazai iya samun soyayya ba, dan in na fa
a mishi ina sonshi na zalunceshi, na zalunci kaina.

Babu wani wanda da
in bakinshi zai sa in iya sonshi sam an riga da an sha ni na warke.

To shikenan Sir Allah ya kaimu gobe." Ajjiyar zuchiya ya sauke, ya mi
o mun wayarshi.

"Saka mun number wayarki da hatimin amincewa in kira wayar a ko da yaushe." Kar
ar wayar nayi nasa mishi number, kana nace.

Baka samu hatimin amincewa da kira ko yaushe ba.

Kira in ya wuce taran dare wayata ma bata kunne, domin kullum ina zama in yi karatu domin nazari"
"To shikenan sai yanda kikace ai.

Muje in taka miki" Nayi nayi dashi ya barshi, amman fur ya
i, sai da ya kaini har bakin mota.

"Kina da shari'a yaune?"
E inada ita, a kotun bayan gidan sarki,
arfe hu
u zamu yi zaman.
ila daga gida can zan wuce" Murmushi yayi kawai baice mun komai ba, naja motata na tafi na barshi a wajen.

Ina tu
i sambatun Oga Rashid suna yawo a kaina.

Wayata ce tayi ruri, da sauri na duba ko Sani ne.

Amman sai naga sabuwar number.
agawa nayi na saka a kunnena.

"Amincin Allah ya tabbata a gareki Amaryar Jega da fatan kin tashi cikin
oshin lafiya, yaya gajiyar biki?" Saida kaina ya sara mun,
it na kashe wayar ma baki
ayanta, hawaye ya soma zuba a idona.

Mahaukaciya ma suke shirin mayar dani na lura, soyayya dai_ soyayya dai a aureka daka kwana biyu kashi ya fika daraja.

Ina bazan iya bama kowa damar shiga rayuwata ba sam." Da wannan surutan na isa gida.

Ina shiga gidan na hango takalman maza biyu a
ofar
akinmu.

Yaran duk suna tsakar gida, Sani na ganina ya kamo hannayena muka shiga ciki tare.

Idanu muka ha
a da Kaila.

Ya zuba mun idanu yana kallona.

Nima shi nake kallo, ina hango murmushin muguntar da yayi mun sanda zamu je zaman firzin.

Ige ce tace.

"Shigo Tani.

Kai kuma Sani shikata ka koma ka jira waje." Kallon Sani nayi nace.

Ka jirani, ku tafi can gidan bazan da
e ba kaji Sani na?" Jayayya yaso ni na hanashi, yana hawaye ya fita, ni kuma na shiga na nemi waje na zauna.

Sai
aremun kallo Kaila yake yi.

Ban yi yin
urin gaishe da kowa ba, Baffa yace.

"Tani, Kaila ne yazo tafiya da yara.

Yace shi bai yarda yaranshi su zauna a hannunki ba.

Yanason ha
e kan iyalanshi waje guda.

Dan haka ke me kikace, tunda kema yarannan naki ne?"
Baffa yara dai sun dawo hannuna kenan.
Chapter 22 · 0% Book details