← Book details Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 25

Sashe 13

Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaya Use tana ri
e gam da hannun Baffa suka fito a mota, Inno, da Yaya karime suma suka fito, sai nima na fito.

Na bu
e gidan muka shiga.

Inno sai washe bakinta take yi, na bu
ofar falon nasu muka shiga baki
aya.

Inno Baffa ku zauna ga kujerunan.

Yaya Use kinga gidan yayi ko?" Sai da ta zaunar da Baffa tukunna tace.

"Masha Allah Tubarkallah.

Gida yayi kyau Tani Allah ya saka miki da aikhairi.

Kamar yanda kiketa
ari a kanmu Tani Allah yasa
anki su zame miki ni'ima a rayuwarki.

Inno, Baffa wannan gidane da Tani ta da
e tana yin asusu dan ganin ta siya musamman domin ku.

Allah yau ya cika mata burinta gaku a gidan da Tani ta siya muku." Tana kaiwa nan ai sai dukkanmu kowa ya soma sharar
walla, harda Baffa da Inno wanda mamaki, ko farin ciki suka hana su cewa uffan.

Yaya Karime tace.

"Gaskiya Tani kinyi namijij
ari sosai.

Ji rayuwa kamar ba zata kai miki ba, amman ji beki yanzu kin zama tauraruwa a cikin dangi.

Allah yai ma zuriya albarka.' Baffa ne ya amsa da cewa.

"Tani Ubangiji Allah yai ma rayuwarki da rayuwar iyalanki albarka.

Yau Tani kece kika ciremu a
angin da muka tsinci kanmu.

Kinga uwarku gata saudiyya take son tafiya ta barni yawon bara.

Dan taga
arfina ya
are.

Ni da duk inda zani nake ri
e hannunta muje, amman ita tsallakewa zata yi ta barni.

Yawon bara har kwatano munje, a can akai cikin Karime, lokacin Use na hannu." Inno ta doka mishi harara tace.

"Ana zancen farin ciki zaka dagula mana zukata Baffa.

Tani mun gode Allah yai miki albarka.

Kiyi ha
uri da tsangwamarki, da
yamatarki da muka dingayi a baya, lokacin da gidan aure yaki yi miki dadi.
atanki ya ta
a mu ainun, ni dai dashi nake kwana nake tashi.

Da tafiya naga tanata tafiya na fidda rai da ganawarmu na zaci sai a darussalam"
Babu komai Inno.

Wannan abunda nayi muku shine ka
ai abinda zan iya muku hankalina ya kwanta.

Bana
aunar ganinku a kwararo, cikin zafi, ruwa, da iska kuna bara.

Lokaci yayi da zaku zauna ku nutsu waje guda ku bautama Allah yanda ya dace.

Zan
aukar muku malama da zata dinga zuwa tana koyar daku addini har gida.

Dan akwai gyara a alwalarku, sallarku, da karatun sallar kanshi.

A irin wannan shekarun hutu kuke bu
ata ba wata wahala ba.

Inno babu maganar zuwa saudiyya bara." Dariya mu ka yi dukkanmu.

"Sai abinda kika ce yarinyar kirki" Dariya muka sake kwashewa dashi.

Muna cikin haka sai muka jiyo sallamar su Goggo Ige, su Goggo marka, Goggo mai riga, Da su kawu Junaidu.

Da
an uwan Inno, su Goggo Azumi, da su Kawu Mati.

Bus guda su ka yo.

Ni na fita na sallami mai Bus
in.

Kuma munyi dashi da yamma zai dawo ya mayar dasu.

Yaya Use ce ta yi musu bayanin na siya ma su Inno gida ne.

Kai Alhamdulillah Wallahi ranar an shi mun arbarka fiye da tunanin masu karatu.

Ige tace.

"Naroro bara ya
are.

Muma in Shanono ta
au zafi sai mu zo mu huta anan." Inno tace.

"Ke da ba miji ba Ige dama zamanmu mu ka yi na samu abokiyar ta
i ai ko?" Nan fa kowa ya
auka da cewa.

"Kuma wallahi hakan yayi" Kawu mati yace.

"Gaskiya Tani kinyi kokari sosai, Allah ka
ai yasan irin ladan da kika samu.

Kinga su Yusuf kai tsaye sun san inda Baffa yake a matsayinshi na babba.

Duk wata matsala za'a kawo mishi gabanshi.

Allah yayi albarka.

Su Inno yawo ya
are, har aka gama yawon bara banga wani abun da kuka tara ba.

Mu kuma ana ce mana mabarata ku
ine dasu." Baffa cikin karfin murya irin na makafi yace.

"Wata gigitacciyar sata akayi mana a wata anguwa a legas mai suna agege unguwace ta hausawa.

A funfata sai da
arayinnan suka samu million biyar.

Inno kuma million uku ne cib a lalitarta cikin leda, duk suka yashemu.

Wadannan ku
e mun da
e muna tarasu amman
arayinnan suka dur
usar damu" Baffa sai kuka shi da Inno.

Duk lokacin da suka tuno da wannan satar to fa sai sun zubar da hawayensu, nima rana ce da bazan manta da'ita ba abadan.

Ana cikin rarrashin su Inno wayata tayi kuka, Sani ne yake kira
ila sun shigo Kano ne.

Ina
agawa kuwa ya sanar dani shigowarsu Kano kenan.

Da tambaya ana nuna musu hanya har suka iso
ofar gida.

Ina tsakiyar dangina yarana suka shigo da sallama.

Cike tab idanuna yake da hawaye na kura musu idanuna.

Amina da su Shafi'i sai murna da ihu.

Hauwana da Salis
ina kuwa basu gane ni ba sam.

Dauda gefe ya koma ya fashe da kuka.

Ya zama saurayi sosai harda
asumba ya ajjiye.

Kyawun yarana ya fito sosai, kowa ya girma gasu cikin kyawun shiga da kamala.

Bani ka
ai naji sha'awar wannan yara ba.

Kab falon babu wanda bai yaba dasu ba.

Dauda kuwa sukaita mamakin girmanshi ya zama babban mutum.

Gefena duk suka zauna, na
aura Salis a kafata.

Dauda sai kallona yake yi.

In suka ha
a ido da Sani sai inga ya banka mishi harara.

Rahama tayi ma masu abinci jaroranci suka shiga shigo da abinci.

Masa nasa akayi, da jallof
in shinkafa wacce taji kayan lambu da tsokar nama, sai abun sha, da ruwa.

A wannan rana zukata cike suke da farin ciki marar yankewa.

Sai yamma lis mai Bus
in daya kawo su Kawu yazo ya kwashesu, bayan na bibbi kowa da dubu biyar biyar, na rakasu har bakin motar ni da Sani da Dauda da suka ma
ale mun.

"Tani tunda Dauda gashi a Kano, ki daure ki rakashi ya duba dangin mahaifinshi su ganshi shima.

A daure ai komai ya wuce, kune a sama kin yi ma Narani tazara mai yawa.

Yanzu kam aurenki ai sai wanda ya shirya.

Murmushi nayi nace.

"To Goggo Ige in na
an rarrage aiyukana zan je in sha Allah in rakashi ya gaishesu.

Amman ba wannan zuwan ba, sabida jigilar asibitin Baffa ban je aiki ba, aiki ya tarumun a office " A haka muka rabu dasu kamar ba zamu rabu ba.

Hannun yarana na ja muka koma ciki, ina zama yaran duk suka dawo kusa dani.

Yaya Use kinga Salis, da Hauwa sun mance dani fa" Sulaiman yace.

"Da Salis da Hauwa kullum sai sun yi kukanki Ummanmu.

Gaskiya ummanmu muna sonki, duk munyi kewarki.

Babanmu yace in mun zo mu gaisheki sosai." Amina tayi zaraf tace.

"Ya ba da sako ma yace in baki hannu da hannu Umma.

Umma mu fa ba zamu koma ba, dake zamu zauna" Ni dan tsantsar farin ciki ma duk wanda na kalla sai inji kamar nafi son shi.

Su Baffa sai nan nan suke da su Sulaiman.

Abun gwanin ban
awa.

A gidan dai muka kwana baki
aya, washe gari kuma ya kasance asabar ne, in monday tayi sati na biyu rabona da wajan aiki, komai nawa ya tsaya cak.

Da sassafe sai ga Rahama tazo ganin yara, Mai hula ma Rahama bata jima da shigowa ba sai gata.

Kai wannan sammako haka, sai kace kun tashi dani a mafarkinku?" Da zolaya nake maganar.

Mai Hula tace.

"Ni tun daren jiya da kika fa
a mun yaranki sunzo ganinki, ba da ban mai gidan bazai barni in fito ba wallahi da a daren zaki ganni.

Ga yara Tubarakalla, kyawawa dasu, ashe kina da samari manya ma, Shanono ke fa ba ta yau bace kyan jikine dake." Dariya nayi mata kawai.

Kajita yarane fa tsayin dai kafane dasu.

Rahama ta harareni tace.

"Wadannan samarin da zasu iya ma mace ciki kike kira da yara Shanono?

A gaisheki, gaskiya kin kyauta da kika dawo da iyayenki kusa dake, gida yayi kyau sosai." Yaya Use ce ta fito musu da abincin karyawar da nasa su Dauda suka fita suka siyo mana.

"Shanono wannan itace Yaya Use ko, me yawan kiranki in kina office?" Dariya muka saka ni da Rahama.

"Itace, ai Yaya Use akwaita da kiran waya." Itama Yaya Usen dariya tayi kawai ta koma ciki.

Su Mai Hula suna tafiya muka fita cefane, ni da Yaya Use da Yaya Karime, da Sani da Dauda.

Kayan masarufi muka siyo ma su Inno da duk abinda nasan zasu bu
ata, hatta tukwane sababbi na sai musu dal.

Bamu muka shigo ba sai bayan la'asar, a tsakar gida muka samu su Baffa da yaran.

Amina na bashi magungunanshi, Sulaiman na rike da kofin kunun Baffa, dan da kunu yake iya ha
iyar maganin.

Bayan mun yi sallah kuma muka shiga jera musu abinci da kayan aiki a kitchen, dan naga su Amina sun gyare gidan tas, ko ina fes.

"Tani amman zamu koma Jos
ebo kayanmu ko?

Dan inada ajjiyar ku
e a cikin tsummokarai" Cewar Inno kenan, Yaya Karime tace.

"Ni da Yaya Use zamu tattare muku duk abinda ya dace Inno, Yaya Use zata zo ta kawo muku kayanku, ku
enku ba za su yi ciwon kai ba" Da yamma na
ebi yarana muka je gidana dan mu ke
e in basu lokaci sosai.

Na shiga kitchen nayi musu girki mai da
i, na shige tsakiyarsu muka ci tare muna suturu gwanin da
i.

Bayan sallar Isha muna zaune a falo ni da su Dauda yana bani labarin damuwar da suka shiga bayan rashina, da yanda ya kammala karatunshi, da garin da yaje bautar
asa, sai ga Amina da wata
aramar jakar kwali fara sol ta mi
o mun.

"Umma ga sa
on da Baba yace a Baki, da muka je mishi sallama" Sani ya fisge jakar a hannun Amina yana mata muzurai, harda mikewa kamar zai daketa wai dan me yasa ta kar
o daya bata.

Sai da Dauda yace ya zauna kana ya zauna.

Ita kuwa duk ta firgita da Sani.

Turarene a cikin jakar, da wata wasi
a.

Kekketa wasi
ar yayi, turaren ya sa a aljihun jallabiyarshi.
Chapter 13 · 0% Book details