← Book details My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 39

Sashe 9

My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Chief yace "Aure ai ke kika hana kanki, Allah ya baki damammaki da dama amma kin ƙi amfani dashi, nawa ne mazajen Aure suka zo nemanki amma duk kin ƙisu, kuma dan anyi miki gori sai kiji haushi?
Ai gorin haihuwa yafi na Aure ciwo, har yanzu damarki bai wuce ba, akwai waɗanda suke zuwa neman Aurenki, aciki akwai Governor Kaduna da Governor Bauchi ga Alhaji Tafidan Bauchi ga manya-manyan shuwagabannin nan Abuja da dai sauransu idan kuma kince a'ah TOH saiki cigaba da toshe kunnuwanki da jin duk wasu ƙananun maganganu akan ki,
Ku tashi ku ban wuri...."

Dasauri Aunty Yolash ta miƙe ta fice tana kuka,
Hajiya Maamie kuwa zaro idanuwa ta fara yi jin manya-manyan mutanen da suke neman Aunty Yolash da Aure, da hassada acikin zuciyarta tabar falon Chief,
Ita kuwa Tsohuwa zama tayi ta cigaba da tattaunawa da Chief akan yanda bikin zai kasance gashi É—aurin Auren har da nashi....

Aunty Yolash tana shiga babban falonsu kai tsaye room É—inta ta wuce ta danna sakata,
Mutanen da suke falo babu yawa duk sun kutsa kai ɗakin da Amarya take itama Baiwar ALLAH ta kulle kanta a cikin Bathroom taƙi buɗewa, sunyi da ita akan ta buɗe amma taƙi, gashi har lokacin dinner yayi, sauran yaran gidan ma ko wacce tana ɗakinta cikin damuwa ganin yanda Abbah ya wulakanta Mommynsu kuma sannan sunji labarin shima zaiyi Aure,
Angwaye sun jira har sun gaji basu ga ko mutum É—aya ba acikin matan gidan balle suga idon Amarya,
Da haka har lokaci ya ƙure aka bantsar da hidimar Dinner, amma ba ƙaramin takaici suka shaƙa ba kaf Abokanan Ango da shi kanshi Angon,
Daman Aunty Yolash ce kawai zata iya tsawatar wa Baiwar ALLAH akan ta buÉ—e TOH itama ga a halin da take ciki itama ta kulle kan natan, Ummy ma wacce itace Yakamata ta rarrasheta itama ta zama uwar É—aki....

🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️

Razhdeen shi da Mohandas layin mabarata suka nufa da isar su tsayar da motar sukayi a dai-dain layin suna baza idanu ko zasu hango Ƴar Amana, a wannan lokacin ma sun yi rashin Sa'a basu ganta ba, ɗan tsuka Razhdeen yaja tare da jan mota zai bar wurin Mohandas yayi saurin dakatar dashi tare da faɗin "wait Major! Bayan barin ka Nigeria nasha zuwa nan duba yarinyar nan amma bata nan, banyi tunanin sauƙa daga motar zuwa tambayarsu ita ba amma a wannan lokacin dole zamu je mu tambayesu ita, ina tunanin rashin zamanta anan ba lafiya ba..."

Dasauri Razhdeen ya juyo yana kallonsa cikin yanayin damuwa, ƙirjinsa ba ƙaramin bugawa yayi ba jin abinda Marshall ya faɗa..."

Mohandas yace "let me go and check her, stay inside the car..."
yana kaiwa nan ya fice kai tsaye wurin tsofin ya nufa, shi kuwa Razhdeen yana daga ciki yana kallon wurin da take yawan zama...
Mohandas tsugunawa yayi a gaban tsohuwar da Ƴar Amana take suka gaisa sannan yake tambayarta labarin Ƴar Amana,
Nan tsohuwa ta fashe da kuka tana faÉ—in "Allah sarki kurmiyar Allah, Amanar Allah sun É—auke ta..."
Mohandas cike da mamaki ya furta cewa "daman kurmiya ce?..."
Tsohuwa tace "ey kurmiya ce, ɓarayi ne suka sace ta..."

Dasauri Mohandas ya miƙe tsaye tare da faɗin "whattttt!!!!...."

Juyawa yayi da gudu ya nufi motarsu, buÉ—ewa yayi ya shiga yana jan numfashi ido a zazzare,
Razhdeen ganinsa ba ƙaramin tsorita yayi ba ganin halinda ya kasance, tsoronsa kar wani mummunan abu ya faru da ita..

A É—an ruÉ—e Razhdeen yace "what's wrong?..."
shuru Mohandas bai bashi amsa ba,
A tsawace Razhdeen yace "ina maka magana ka bani amsa mana ..."
Razhdeen bai taɓa buɗe murya yayi magana kamar yanzu ba, cike da mamaki Mohandas ya juya yana kallonsa ganin yanda ya rikice lokaci guda,
a É—an tsorace Mohandas yace "someone kidnap her..."

Razhdeen cikin go slow ya juyo yana ƙarewa Mohandas kallo ido a zazzare,
Jin bai gamsu da maganar Mohandas ba yasa ya buÉ—e murfin motar ya fice, kai tsaye wurin tsofaffin ya nufa yana zuwa ya tsaya yana binsu da kallo, a tsawace ya fara magana yana faÉ—in "Who kidnap her?,
tell me please who come and kidnap my sarah?..."

Duk tsaya kallonsa suke domin babu wacce tasan mai yake faÉ—i domin da turanci yake maganar,
tsohuwar ƴar Amana ce tace "kayi haƙuri yaro Bama jin Yaren nan..."

Razhdeen hannu bibbiyu yasa a cikin sumar gashinsa yana cakurkuÉ—awa cikin zafin rai yace "nace waye ya sace mun Sarah? ..."

Anan duk suka sanar masa duk yanda akayi da cewar suma basu ga fuskarsu ba domin baƙar hula ce akan su...."
tsohuwar ta miƙa masa jitar Ƴar Amana...

Razhdeen kamar zai dungura haka ya nufi motar yana shiga ya finciki motar a É—ari suka bar wurin,

A wannan ranar Razhdeen da Mohandas ba yanda basu shiga ba neman Ƴar Amana amma babu ɗuriyarta, duk yanda suka san ƙungiyoyin Dabanci Saida suka je amma basu samu labarinta ba, Saida suka yiwa wasu ƴan Daba dukan tsiya ganin zasu raina musu wayo,
yanzu misalin ƙarfe 2 na dare suna hanya, Mohandas gaba ɗaya ya gama gajiya daƙer ya lallami Razhdeen suka koma gida akan washe gari zasu ƙara fitowa nemanta......

asmeetah writer ✍️

*MY ENEMY _*

🫦 مقىينا 🫦

Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳

Asmeetah (giaÉ—e writer)

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

STEP TWO
👇
*11_ TŌ _12*

Misalin ƙarfe uku na dare, agogo ne yake harbawa a hankali ƙit-ƙitt-ƙittt a yayin da Razhdeen yake kwance saman katafaren gadonsa, yana rufe da mayafi sai iya fuskar sa ne a waje yana kallon ceilling, kashe hasken ɗakin yayi sai ɗan hasken lamp da ya bari mai launin green,
A daren yau Razhdeen bai samu yin bacci ba sakamakon abin da yasa a ran sa, ɓatar Ƴar Amana ba ƙaramin girgiza shi yayi ba domin a halin yanzu bai san a wani hali take ciki ba, gashi an bayyanar masa cewa zuwa akayi har wurin da take aka ɗauke ta, duk yanda akayi sun haɗa mata tarko ne,
Tunani ne barkatai acikin kwakwalwar sa, mafita yake nema yanda zai samu yarinyar nan domin a halin yanzu ita ce raunin sa!...

Washe garin ranar ɗaurin Auren Roshan da Baiwar ALLAH, kowa ya hallaru baƙi ne a gidan Chief kamar basa mutuwa tsabar yawan family, misalin ƙarfe 12 na rana Ango da Abokan sa kowa yayi shirin zuwa ɗaurin Aure dake can babban masallaci, Abbah shima da abokansa waɗanda suka zo ɗaurin Aure sun sha manya-manyan kaya, kowa ya hallaru sai fita ake da wasu manya-manyan motoci ga motocin sojoji suma zasu yi rakiya, kowa ya tafi sai iya Ango ne kawai ya rage shima yasha farar gizner da babbar gariya sai shining giznar take, ga wani irin ƙamshin da yake fitarwa kai kace wanka yayi da zallar turare,
Roshan ba ƙaramin kyau yayi ba, ga hular kalar kayan, sai wasu Abokansa guda uku motar su ce kawai ta rage basu tafi ba, ganin Roshan yaƙi tafiya yasa suma suka ƙi tafiya domin saboda Angon za'aje wurin ɗaurin Auren shi kuma bai tafi ba, Roshan ba kowa yake jira ba illa twins ɗinsa Razhdeen, duk taron mutanen da akayi babu Razhdeen a ciki, kowa sai tambayar sa yake, domin shine twins ɗinsa kuma babban Abokin Ango, an ƙira wayarsa switch up, anje gidansa baya nan babu wanda yasan yanda yake hatta Mohandas shima ya halarci wurin ɗaurin Auren Roshan,
Ganin shuru babu labarinsa yasa Abokanan Roshan suka ja shi cikin motar nan da nan kamar walƙiya suka bar gidan domin iya su kawai ake jira a wurin taron ɗaurin Aure...

Baiwar ALLAH tana bedroom ɗinta tare da masu kula da ita ba abinda take sai kuka, gaba ɗaya fuskar nan tayi jawur tsabar kuka kamar ba Amarya ba, ji take kamar ta sanar cewa bata son Auren Roshan amma sai dai idan tayi hakan tayi butulci sannan aikin gama ya gama tinda an tafi ɗauro Auren, har cikin ranta bata cire son Razhdeen acikin zuciyar ta ba kuma gani take bazata taɓa cire soyayyarsa ba, kulle kanta da tayi a bathroom tayi niyar tasha poison ta kashe kanta amma tayi tunanin kashe kai ba abu ne mai sauƙi ba, tana ciki Abbah ya shugo domin a lokacin har anje an gayo masa dake tana jin shakkar Abbah,
tana zaune a bakin bed tunanin samawa kanta mafita take, amma zuciyarta na sanar mata cewa "kiyi haƙuri ki zauna da mijinki haka ƙaddarar ki tazo miki, a duk yanda kika tsinci kanki to ki gode wa ALLAH..."
Sauƙe numfashi tayi domin tayi na'am da shawarar da zuciyarta ta bata, a hankali take ɗago da kanta tana bin mutanen ɗakin da kallo, ganin kowa yana cikin farin ciki yasa ta yin maganar zuci cewa "Allah sarki farin cikin ku kawai kuka sani amma baku san tawa farin cikin ba..."
tana cikin saƙe-saƙe kwatsam taji an dafa kafaɗarta, da sauri Baiwar ALLAH ta juyo tana kallon wacce ta zauna gefenta tare da ɗora mata hannu akan kafaɗa,
Ramlat ce tasau mata murmushin takaici da kuma kishi ta ce "Sannu Amarya bakya laifi, Amma fah kin ciri tuta gaskiya duk da baki da asali amma haka Yaya Roshan ya nace miki, kuma ba wani dace wa kuka yi da juna ba, kina nan kamar wata farar goÉ—iya..."

Duk mutanen É—akin ne suka juyo suna kallon su, wata daga ciki ne ta ce "toh ikon Allah duk meya kawo wannan maganar?..."

Ramlat ta kalleta sama da ƙasa sannan ta ce "bakin da Allah ya tsaga baya rasa ta cewa, don haka abin da ke raina na faɗa..."

wacce tayi maganar ce ta kuma cewa "Amma ai bai kamata kiyi irin wannan maganar a cikin mutane ba..."
Ramlat ta ce "Oh ashe dai a cikin mutane nake, ai Ni kuwa na É—auka dabbobi ne..."
Chapter 9 · 0% Book details