Sashe 28
My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aunty Yolash ta cigaba da cewa "duk da nasan ke kike da laifi Amma ai yanzu kin shiryu kuma kinyi alƙawarin bazaki ƙara maimaita kuskuren ba, ya kamata Chief ya dubi halin da kike ciki yayi haƙuri amma tinda bashida yafiya sai ki sharar da shi, dan Allah Kilishi ki zamo mai kamun kai, ki daina bibiyansa haka, ni duk abinda kike so ki ƙira wayata zaki same ni zan dauke miki duk ɗawainiyar ki kar ki damu, ki cigaba da addu'a komai mai wucewa ne, ki kwantar da hankalinki, ni yanzu zan koma bauchi domin ayyukana na bari nazo gurin da aka wulakanta ni, na tafi saina ji ki..."
Daga nan Aunty Yolash ta koma Bauchi, ita kuwa Hajiya Kilishi a ranar ko rintsawa bata yi tsabar kuka, ba ƙaramin shiga damuwa tayi ba, ga yanzu ba halin ganin ƴaƴanta balle taji sanyi a ranta, idan taje yanda suke kuma Sojoji hanata shiga ciki suke sakamakon bin umarnin Abbah, ya sanar musu cewa idan suka ƙara barin Kilishi ta shiga masa gida duk saiya hora su...
Ummy uwar masu gida itama ba ƙaramin shiga damuwa tayi ba na rashin ganin mahaifiyar ta tsawon shekara guda, ta samu Abbah akan tana son zuwa yanda take amma yaƙi barin ta, hakan yasa yanzu ko zuwa wurin da Abbah yake bata yi kullum a cikin kuke take, ga yanzu kwana biyun nan ta ƙi saka komai a cikin ta haka take zaune ba ci ba sha, ganin halin da Ummy take ciki ne yasa itama ƴar tinny ciki damuwa, yanzu a ɗakin Ummy take bata zuwa wurin Ammy ma balle shi kan shi Abbah, duk sun ƙaurace masa,
Ammy ta yi magana wa Abbah yabar yaran su je suga mahaifiyar su amma Abbah ya dakatar da ita akan cewa babu ruwanta kada ta ƙara shiga cikin maganar,
Roshan ganin halin da Ummy da Æ´ar tinny suke shima ya samu Abbah, yana faÉ—in "Abbah ka bari na kaisu idan sun gana da juna saina dawo da su..."
Nan ma Abbah ya ce "bai yarda ba sai dai su mutu..."
Kowa har yayi ya gaji.
Wata rana Ummy ta fito falo kana ganinta kasan bata da lafiya ga duk ta rame tsabar jikinta babu ƙwari haka ta yanki jiki ta faɗi sumammiya, Ammy dake shirya abinci akan dinning tana hangota ta tafo da gudu tana ƙiran sunanta, dai dai lokacin da Abbah ya shugo, ganin Uwar masu gida a cikin wannan halin yasa yayo kanta a ruɗe, haka yasa hannu ya ɗago ta yayi waje da ita sai asibiti...
Ummy Saida ta sha ledar jini da ruwa domin ba ƙaramin wahala take sha ba, sai da suka kwana tukun ta farfaɗo tana kuka tare da faɗin "ni ku kaini wurin mommy, nasan tana cikin mawuyancin halin, bana so na mutu ban ganta ba dan Allah, mommy na an rabani da ita kenan? ba zan taɓa yafe wa duk wanda ya rabani da Mahaifiyata ba wallahi...."
tana kaiwa ƙarshe ta fashe da matsanancin kuka...
Abbah yana tsaye yana jin duk maganganun da take faÉ—i ga kuma Ammy a zaune a gefen gadon da take sai Baiwar ALLAH itama tazo duba ta.
Suna cikin wannan halin sai ga Doctor ya shugo Abbah ne ya ce "shin za'a iya sallame mu yanzu?..."
Doctor ya ce "eh duk abubuwan da ya kamata ayi mata munyi yanzu komai normal..."
Abbah ya ce "good, kinga uwar masu gida tashi muje ki shirya na kai ku wurin uwatta kun tinda kun fi sonta akan Ni..."
ya kalli Ammy ya ce "ina Auta ta?..."
Ammy ta ce "ta fita da Roshan ina tunanin gida suka nufa..."
Ya ce "Okay zan kai su amma bazan bar yarana a hannunta ba domin da mutuncin su..."
Ammy ta ce "kenam kana nufin kace ita uwar tasun batada mutuncin ne?..."
Abbah ya ce "ko kaÉ—an babu..."
Ammy shuru tayi tana gudun kar ta fusata shi domin yanzun ma a dole zai kai su ba dan yana so ba...
Haka Abbah ya riƙo hannun Ummy ya ɗago da ita duk suka tashi suka fice,
Bayan sun koma gida duk shirya wa sukayi har Æ´ar tinny Ammy ta shiryata, sai a lokacin hankalin Ummy ya dawo jikinta domin a halin yanzu tana muradin sanya mahaifiyar ta a idonta, kuma taji labarin tana shan wahalar rayuwa kowa ya guje ta..
Abbah shi da kansa zai kai su har garin Suleja...
★★★★★★★
Baiwar ALLAH ce a É—akin Roshan tana gyara masa gadon kwanciyar sa, yanzu kwana biyun nan ita take masa komai, kullum sai ta je part É—insa ta gyara tare da wanke masa bathroom ta feffeshe ko ina da turare, sannan tayi girki ta shirya su akan dinning su ci tare, a baya kuwa sai dai ta É—auki nata ta shiga room É—inta ta ci acan shi kuma ya zauna a dinning ya ci shi kaÉ—ai, yanzu kuwa zama take su ci tare,
Abun ba ƙaramin mamaki yake bashi ba, a ransa yake faɗin "shin mai take nufi ne?..."
A yanzun ma ta gama gyara masa gado ta juya zata fita kwatsam ta gà nshi yana tsaye a bakin ƙofa ya goya hannayensa saman ƙirjinsa yana mata wani irin kallo na rashin fahimta,
Itama tsaya kallonsa take daga bisani ya ƙarasa shugo wa ya zauna a bakin gado sannan ya kalle ta ya ce "ki zauna mana..."
Itama taje ta zauna a wurin da ya nuna mata a kusa da shi,
zama tayi jiki a sanyaye..
Roshan idonsa na kallon gabansa ya ce "naga kwana biyun nan kin canza shin meye a cikin zuciyar ki? tsawon shekara muna zaune ko da wasa baki taɓa zuwa part ɗina ba amma yanzu a kwana biyun nan meyasa? kinsan dole zan yi tunanin wani abu a raina, domin duk wanda ya ce baya sonka da safe babu wanda za'ayi da daddare ya komo yace yana sonka wannan ƙarya ne, saboda haka tin a baya kin nuna bakya sona ɗan uwana kike so kuma nasan har yanzu hakane a cikin zuciyar ki, kiyi haƙuri nasan na cutar da ke dana riƙe ki har zuwa tsawon wannan lokacin kinyi haƙurin zama dani a gida ɗaya, inda ace tin farko baki nuna cewa zaki zauna dani ba da yanzu kinada yaron ki jinin ɗan uwana Razhdeen domin a lokacin ya nuna ya amince kika kwabsa, gashi muna zaune zaman ba daɗi Ni ba ɗa kema haka ko kusantar junan mu bamu taɓa yi ba wai hakan muna zaman Aure,
Insha Allahu sauran ɗan watanni kaɗan Razhdeen ya dawo da zaran ya dawo zan damƙa masa ke domin yanzu haka takardar sakin ki na nan a ajiye lokaci kawai nake jira...."
ya ƙarasa maganar yana sharar hawayen da ya zubo masa,
Itama Baiwar ALLAH kukan take jin maganganun da yake faÉ—a mata kuma alhalin yanzu ba haka bane a cikin zuciyarta,
Cigaba da cewa yayi "zan roƙe ki wata alfarma shin zaki iya mun?..."
Yayi maganar yana kallonta, itama kallonsa take tare da É—aga masa kai,
Jinjina kai yayi sannan ya ce "inaso ki daina shugo mun room, ki tsaya a yanda kike a baya, girki ne idan kika yi zan ci idan kina so zamu zauna a dinning muci kamar yanda muke yanzu, amma fake wa wuri ɗaya ne banaso domin nasan kaina banida juriya, kina cuta na sosai idan naga mun fake Ni kuma bazan iya aikata komai dake ba saboda nasan wata rana ke matar twins ɗina ne, bana so ya karɓi saura na, nafi so ya ɓare ki sabuwa a leda zan fi jin daɗin haka sosai, inaso idan na kusanci mace to ya zamana har ƙarshen rayuwata ita zan rinƙa kusan ta, saboda haka kiyi nesa da abinda zai sa mu fake wuri ɗaya, zan cigaba da shan lemon tsami na har Allah yasa mu rabu,
Da fatan dai ban ɓata miki rai ba ko?..."
Baiwar ALLAH ganin bazata iya juran kalaman Roshan ba yasa ta tashi tare da fashewa da matsanancin kuka ta bar É—akin da gudu, kai tsaye part É—inta ta nufa.
Shima Roshan bai san lokacin da hawaye ya fara masa go slow ba domin ba ƙaramin ƙaunar Baiwar ALLAH yake ba, ya kasa cire ta a ransa kodan yana ganinta koda yaushe ne...
★★★★★★
Bayan isar su Abbah garin Suleja gidan da aka masa kwatance nan yayi parking a ƙofar gidan, gidan ne kana gani kasan gidan haya ne amma kowa da part ɗinsa,
Har Ummy ta sauƙa daga cikin motar tayi gaba zata kutsa ciki Abbah yayi saurin riƙo ta yana faɗin "baki da hankali ne? daga ganin gida zaki shiga idan ba nan ne gidan kuma fa?..."
Ummy tsayawa tayi domin a halin yanzu bata da wani buri da ya wuce taga mahaifiyarta..
Wani magidanci ne ya fito daga gidan da duk kan alamu shima a gidan yake da iyalansa, Abbah ne yayi masa magana yana faÉ—in
"Dan ALLAH bawan Allah nan ne gidan da Kilishi take?..."
Mutumin ya ce "eh dake part-part ne gidan ban san a wani ƙofa take ba, kuma akwai mata da yawa a gidan duk bansan sunayen su ba..."
Abbah ya ce "okay matan duk bazaware ne ko matan Aure?..."
Mutumin ya ce "duk matan Aure ne bazawara ɗaya ce ɓangarenta daban ita kaɗai..."
Abbah ya ce "okay to wurin bazawarar muka zo..."
Mutumin ya ce "nasan ƙofar da take muje na kai ku..."
Abbah ya ce "a'ah kayi mana sallama da ita muna waje daga nan zamu wuce ne..."
Mutumin ya ce "okay..." Sannan ya shige ciki, can ya fito ya sanar da cewa "tana fito wa..."