← Book details My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 39

Sashe 20

My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abbah ya ce "whattt? to amma ya akayi hakan ta faru, bata sonka kuma akayi Auren? shin waye a ranta har ta kasa karɓar soyayyarka kuma ta kasa baka haɗin kai...".

ÆŠago wa yayi daga kwancen da yake akan Abbah, da rinannun eyes É—insa yake kallon Abbah sannan ya ce "Razhdeen ne a cikin zuciyar ta, shi take so kuma take muradin ya zamo mijinta uban Æ´aÆ´anta..."
ya ƙarasa maganar yana sakin ƙayataccen murmushin baƙin ciki da kuma farin ciki...

Abbah gaba ɗaya ya gama ruɗe wa, cike da mamaki ya ce "amma shi Razhdeen bai taɓa sanar mun wannan maganar ba, ko a bakin wani ban taɓa jin Razhdeen da Daughter suna soyayya ba...

Roshan ya ce "Abbah ka gane zancen mana, ba soyayya suke ba ita ce take sonsa amma ta kasa nasar masa, ta kasa fitar da abinda yake cikin cikinta da haka har aka É—aura mana Aure, shi kan shi Razhdeen bai san tana son sa ba..."

Ajiyar zuciya Abbah ya sauƙar yana jinjina kai daga bisani ya ce "Roshan!.."

Roshan ya amsa masa cikin sassanyar murya.

Abbah ya cigaba da cewa "shin wani hukunci kake son É—auka?..."

Roshan ya ce "Abbah ni na yanke shawarar rabuwa da ita, in yaso sai a Aura mata Razhdeen duk da nasan da wuya ya yarda da hakan, amma zan lallame shi akan ya yarda ya Aure ta, ina son farin cikin ta sosai, a halin yanzu ita É—in marainiya ce bata da kowa sai mu..."

Jinjina kai Abbah ya yi daga bisani ya ce "shikenam duk yanda ka yanke shine dai-dai, hakan na nufin zakayi sadaukar da soyayyar ka wa ɗan uwanka domin ka sama mata farin ciki, kai baka damu da naka farin ciki ba, shikenam inaso a yanzu kowa ya hallara a babban falon cikin gida, kaje ka ƙira matar takan, nima yanzu zan ƙira Razhdeen yazo yanzun nan..."

Roshan tashi yayi da ƙer yana jan ƙafa da haka ya fice, shima Abbah wayar sa ya ɗau ya danna ƙiran number Razhdeen cikin sa'a kuwa lokacin wayar tana hannunsa ya ɗauka da sallama a bakin sa..

Abbah zuciyarsa a hargutse ya ce "kana ina Razhdeen?..."

Razhdeen ya ce "ina gidana..."

Abbah ya ce "okay I want to see you right now..."

In other side Razhdeen ya ce "but what happen Dad?..."
Abbah ya ce "kar ka damu idan kazo zaka ga komai a idonka..."

Razhdeen amsa masa yayi tare da faɗin "Okay..." ya katse ƙira yana mamakin ƙiran gaggawar da akayi masa kuma da safe yaje ya gaishe da su Abbah, babu yanda ya iya haka ya bar duk abinda yake ya ɗauki key ɗin motar sa zai fita,
A falo ya tarar da Ƴar Amana dake yau ba school ranar hutu ne, ta zuba wa plasman ido tana kallo kai kace ba kurmiya ba ce, bata ankara ba taji an manna mata kiss akan goshi da sauri ta ɗago tana bin sa da kallo, murmushi ya sakar mata tare da faɗin "take care my Beb, I'll be back..."
Itama murmushi ta sau idonta akan sa, ga gashin kanta yanda ya bazu akan gadon bayan ta...

Kaɗa mata key yayi sannan yasa hannu zai buɗe ƙofa ya fice ya ji Madam Blessing tana faɗin "sai ka dawo Major..."

Ba tare da ya juya ya kalle ta ba ya ce "thank you..."
daga nan ya yi tafiyar sa.

Kowa ya hallaru a babban falon gidan Abbah duk da yanzu basu da yawa a gidan, daga Abbah ne sai Ammy sai uwar masu gida da Ƴar tinny itama yau ba school ga Roshan shima a zaune gefe guda, waɗanda ake jira Razhdeen ne sai Baiwar ALLAH wacce aka ƙira ta tin ɗazu bata samu damar zuwa ba,
Abbah ne ya kalli Roshan sannan ya ce "Roshan kaje ka taho mun da Daughter ina tunanin tasan ƙiran akan maganar ta ne shiyasa ta ƙi zuwa..."

Roshan ya ce "okay tam..." ya tashi zai bar falon.

Razhdeen parking ya yi a gurguje ya buɗe murfin motar sa ya fito dai-dai lokacin da Baiwar ALLAH itama ta iso part ɗin, bakin get ta nufa idonta akan Razhdeen wanda shima wurin ya nufo shima ita yake kallo yana saƙe-saƙe a ransa, a gaba da baya suke ita tana gaban sa a yayin da shi kuma yake ta bayan ta baifi nan da ɗan rata kaɗan ba ya iso ta, tafiya take ba tare da ganin gaban ta ba, idonta akan sa bata san ta iso bakin get ɗin mashigar compound ɗin gidan ba, kawar da kansa yayi daga ganinta yasan ta iso bakin get ɗin amma bai dakatar da ita daga ganin sa ba domin ya daɗe da tabbatar da cewa Baiwar ALLAH taɓaɓɓiya ce ta fara haukacewa tin lokacin da ya kaita hospital.

Kan ta ne yayi wani irin mungun buguwa da ƙofar get mai ƙarfin gaske, wani irin gigitaccen ƙara tayi tare da yo wa baya zata faɗi har ta saddaƙar kwatsam taji an riƙo ta, idonta a ƙarƙame a matuƙar tsorace ta cakume shi sosai jikinta har wani ɓari yake tana sauƙar da numfashi da ƙer,
kallonta ya tsaya yi yana kallon kalar riƙon da yayi mata, caɗaf ya ɗaga ta yayi mata ɗaukar jaririya wanda shima kansa bai san yayi mata irin wannan ɗaukar ba, domin a yanda tayo baya zata faɗi inda bai yi saurin ɗaukar ta ba sai dai a ɗauke ta sumammiya, a hankali take buɗe eyes ɗinta tana so taga a hannun wa take, idanuwanta ne suka sauƙa akan kyakkyawan fuskar Roshan mai ɗauke da ƙayataccen murmushi, zaro ido waje tayi ganin a hannun Roshan take, ƙoƙarin sauƙa daga ɗaukar da yayi mata take, a hankali ya sauƙar da ita, waiwaye ta soma yi tana duba yanda Razhdeen yake domin tasan shine a wurin.

Roshan da ya fahimci Razhdeen take duba wa ya ce "tin tinin ya yi wuce war sa, domin inda Allah bai kawo ni da wuri ba ina tunanin yau sai dai kiyi kwanan hospital...

Abunda ya faru shine a lokacin da ta bugu da get tayi baya a ruɗe zata faɗi ƙasi shi da kansa Razhdeen ya kauce mata ko sauraronta bai yi ba balle ya yi gaggawar riƙo ta, kafin faruwar haka kuwa Roshan daman ya fito bakin get ɗin ganin yanda take ta kallon Razhdeen ne yasa ya tsaya cakk yana binsu da kallo, ganin tana shirin kaiwa ƙasi ne yasa ya taho da gudu yayi mata ɗaukar luɗa kafin taje ƙasi, shi kuma Razhdeen ko kallon yanda suke bai tsaya yi ba ya buɗe get ya shige ciki...

Baiwar ALLAH tsaya wa tayi tana tariyo abinda ya faru, bayan da tayi zata faɗi da akan Razhdeen zata faɗa shi kuwa yayi saurin kauce mata yabi ta gefen ta, tabbas in ba dan Roshan ba Razhdeen bazai taɓa tallafa mata ba,
rufe eyes É—inta tayi sosai tsananin kunya ne ya ishe ta, sai yanzu ta fara jin ciwon kai sakamakon buguwar da tayi, kama kanta tayi tana faÉ—in "wayyo kai na..."

Roshan ne ya ce "na É—auke ki ne?..."

ta ce "no I have leg, I'll walk by myself..."

Murmushi ya yi tare da faÉ—in "okay fine..."

Tayi gaba yana binta a baya da haka suka shige, a falo suka tarar da su Abbah da Razhdeen yana zaune sai pressing phone É—in sa yake,
Roshan ne shima ya zaune dab da Razhdeen, itama Baiwar ALLAH zama tayi a kusa da Uwar masu gida...

Abbah ne ya soma magana yana faɗin "ba komai ne yasa duk na tara ku ba sai dan na sama wa iyalai na Dawwamammiyar farin ciki na har abada, akwai wani labari da naji wanda yayi matuƙar ƙona mun rai ya kuma saka ni cikin ƙunci, na shiga tashin hankali matuƙa dana ji kalar rayuwar da ma'aurata biyu suke yi na rashin wanzuwar farin ciki da zaman lafiya..."

Ƙirjin Baiwar ALLAH ne ya yi wani irin bugawa da ƙarfin gaske jin wannan batun tasan da su Abbah yake,
Uwar masu gida ne ta kalli Baiwar ALLAH domin ta fahimci babu zaman lafiya a tsakaninta da Yaya Roshan kuma tasan Roshan bashi da damuwa sai dai matsalar daga wurin ta ya fito...

Razhdeen dai yana zaune ya kasa fahimtar komai game da abinda Abbah yake faÉ—i..

Abbah ne ya kalli Baiwar ALLAH sannan ya ce "Daughter Roshan ya sanar mun duk halin da kuke ciki, ya buƙaci rabuwa da ke domin ya sama miki farin cikin da kike nema..."
Nan Abbah ya kwashe duk maganganun da Roshan ya sanar masa ya faɗe su yana kallon Baiwar ALLAH ya ƙarisa maganar da cewa "Shin duk maganar da ya faɗa gaskiya ne?..."

Zaro ido Baiwar ALLAH tayi tana ƙoƙarin haɗiye ranta tsabar tsananin fargaba da tsoro ga yanda Abbah ya fito mata da sirrin da take ɓoye wa a gaban mutanen gidan...

Razhdeen wani irin ƙololuwar baƙin ciki ne ya ziyarci cikin zuciyar sa jin yanda Baiwar ALLAH take wulaƙanta masa twins sannan har take furta cewa bata son shi, jin yanda ta furta wa Roshan cewa shi take so yasa gaba ɗaya yaji ya tsani yarinyar, sai kuma ya tuno da maganganun da take ta furtawa a gadon asibiti...

Abbah ne ya ce "bazan takura miki akan dole sai kin zauna da Roshan ba amma ina mai sanar miki cewa duk wanda ya nuna yana sonki tsakani da ALLAH to shine Abokin rayuwa, amma indai ke kike so kuma ba'a son ki to rayuwarki tana yawo a tsalallakun gajumare ne,
yanzu ina so ki furta da bakin ki kina son Razhdeen..."

Da sauri ta É—ago tana kallon Abbah ido sunyi jawur tsabar kuka, ta kalli Roshan taga shima kallon ta yake sannan ta maida idonta kan Razhdeen a yayin da shi kuma Razhdeen idonsa suke kan Abbah jin tambayar da yake mata...

Abbah ne ya sake maimaita wa da cewa "kina son Razhdeen ne kamar yanda kika faÉ—a ko kuma?..."

Girgiza kai tayi tana shaƙar numfashi da ƙer cikin kuka ta ce "zan cigaba da zama a gidan mijina..."
Chapter 20 · 0% Book details