Sashe 35
My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin yana shirin faɗuwa yasa Baiwar ALLAH shugowa ciki da gudu tayi saurin riƙo shi tana ambatar sunansa
"Yaya Roshan! Yaya Roshan dan ALLAH ka daina Please ka tashi bana son irin wannan wasan..."
Shi kuwa lokaci guda idanuwansa suka fara ƙaƙƙafewa yana fitar da numfashi daƙer, ga yanda yake sama da ƙasa da ƙirjinsa alamun bugawa yake sosai,
Baiwar ALLAH fashe wa tayi da matsanancin kuka tana faÉ—in "dan Allah Yaya Roshan ka tashi, wannan wani irin wasa ne haka, bana son kalar wasan nan, ni idan baka son rabuwa da ni zan cigaba da rayuwa da kai a haka, nima ba son rabuwa nake da kai ba, ka rufa mun asiri dan Allah..."
Tana cikin wannan halin yana kwance saman cinyar ta sai ga wani irin jini ya burtso masa daga cikin bakin sa..
A ruÉ—e Baiwar ALLAH ta zaro manya-manyan idanuwanta ta ce "na shiga uku Yaya Roshan..."
wani irin tari yake yana Amar da jini, eyes ɗinsa har sun chanza color sun koma green, jikinsa gaba ɗaya ya koma yellow alamun babu jini a jikinsa, yana kaiwa ƙarshen tarin sa numfashin sa ya ɗage gaba ɗaya, sai wuyansa da ya karye..."
Hannu ta ɗora aka ta zabga wani irin gigitaccen ihu tana faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un Yaya Roshan ɗina, wayyo nashiga uku Dan girman Allah ka tashi, Yaya Roshan ka taimake ni ka tashi wallahi ina sonka, ina matuƙar ƙaunar ka mijina, ina sonka mijina wallahi, bazan iya kasancewa da kowa ba inba kai ba, wallahi idan ka mutu Nima rayuwata bata da wani amfani Yaya Roshan..."
★★★
Abbah kuwa suna isowa cikin gari basu tsaya a ko ina ba sai a babban masallacin juma'a anan ya sanar da ɗaurin Auren sa da za'a gabatar a yau Jumma'at, ya ƙira manya abokansa a waya, ya sanar musu cewa yana gayyatar su zuwa masallacin juma'a, waɗanda ya gayyato basu san meye dalilin ƙiran su ba sai da suka zo tukun suke jin labarin ɗaurin Aure, za'a mayar da Auren sa da uwar ƴaƴansa Hajiya Kilishi ba tare da wasu daga cikin mutanen sa sun sani ba, sai iya waɗanda yake da kusanci da su, anan ya bayar da sadaki ya wakilci wasu a mazannin wakilai ga kuma shaidu...
Hajiya Kilishi da Æ´aÆ´anta kuwa suna cikin mota suna jiran zuwan Abbah domin ko su basu san a yanzu za'a mayar da Auren ba..
Suna zaune sai suka hango Abbah da abokansa waɗanda ya gayyato sun nufo motar, har an kammala ɗaurin Aure cikin ƙoshin lafiya,
Bayan isowar su Abokanan Abbah fatan alkhairi suka rinƙa musu tare da nasihohi da wa'azi especially Hajiya Kilishi an fi ja mata kunne kafin daga baya Abbah ya ja su suka nufi gida, amma yaso ace ammy ta sani bawai ta gani kai tsaye ba, amma babu yanda ya iya gwara ayi abu a wuce lissafinsa...
Hajiya Kilishi ta sha mamaki sosai da taji a yanzu har aka maida Auren ta, ba ƙaramin farin ciki ta shiga ba, anan ta ƙara jinjina wa ikon Allah, Addu'ar ta yayi tasiri lokaci guda Allah ya karkato mata hankalin Chief...
Suma yaran ba ƙaramin farin ciki suka shiga ba...
Wayar Abbah ne ya fara ringing ganin Razhdeen ne yasa shi sakin murmushi ya É—aga yana faÉ—in "Ogan Sojoji ya akayi ne?..."
Razhdeen cikin sassanyar murya ya ce "Dad me yake faruwa ne?.."
Abbah ya ce "me ya faru?..."
Razhdeen ya ce "gaba É—aya hankali na ya kasa kwanciya, zuciyata sai bugawa take, i think so akwai wani mummunan abu da yake shirin faruwa a gida..."
Gaban Abbah ne ya yanke ya ce "mummunan abu kuma Razhdeen? a'a babu wani abu da ya faru duk muna cikin ƙoshin lafiya..."
Razhdeen ya ce "where is my twins?..."
Abbah ya ce "na bar shi a gida cikin ƙoshin lafiya..."
Razhdeen ya ce "okay fine..." Yana kaiwa nan ya katse ƙiran.
Abbah shima hankalinsa kasa kwanciya yayi jin abinda Razhdeen ya sanar masa domin in irin haka ta faru da Razhdeen to akwai abinda ya faru ko kuma zai faru, most especially idan abun akan Roshan zai faru...
Haka Abbah ya ƙarawa motarsa gudu yana son isa yaga shin da gaske ne abinda Razhdeen ya sanar masa ko kuma! In har ya haɗu da Roshan cikin ƙoshin lafiya to sai dai akan wani nashi ne abun zai faru...
Cikin lokaci ƙanƙani Abbah ya isa gida, a rikice ya shige bayan an bubbuɗe masa gate gate ɗin da suke gidan.
Su Ummy ne suke ta tambayar sa meya faru amma Abbah ya kasa basu amsa sai ya tabbatar da idonsa..
Abbah bai tsaya a ko ina ba sai a part ɗin Roshan ko tsaya sauƙe su Hajiya Kilishi bai yi ba, yana sauƙa ya nufi cikin babban falon gidan, suma sauran haka suka bi bayansa,
suka tarar falon ba kowa, Abbah ya kalli Ummy ya ce "shiga ciki ki ƙira mun Daughter..."
Ummy ta nufi part É—in Baiwar ALLAH, can ta dawo tana faÉ—in "Abbah bata nan fa..."
Abbah ganin tsayuwar bashi da amfani yasa shi nufan room É—in Roshan domin yafi son yayi ido huÉ—u da shi,
yana zuwa ya samu ƙofar ɗakin a buɗe, ganin Baiwar ALLAH tana rungume da Roshan a ƙasin carpet yasa shi ƙarasa shiga da sauri yana faɗin "lafiya kuwa Daughter me ya faru da shi..."
ÆŠagowa tayi da jajayen idanuwan ta waÉ—anda suka kaÉ—a sukayi jawur tsabar kuka ga bakinta duk jini yanda ta haÉ—e bakinta da na Roshan tana hura masa iskar bakinta ko numfashin zai dawo...
Abbah ganin halin da Roshan yake ciki ne yasa shi firgita yayo kansa da gudu yana "faÉ—in innalillahi wa inna'ilaihi raju'un ashe gaskiyar Razhdeen, gaskiyar Razhdeen, ciwon sa ne ya tashi..."
Haka yasa hannu ya É—ago shi yana faÉ—in "Daughter taya ni É—aukar sa mu fita..."
Itama Baiwar ALLAH hannu tasa suka É—ago shi, suka fice falo da shi, su Ummy ganin halin da Roshan yake ciki ne yasa duk suka nufo su...
Ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba Abbah ko leƙa gidan sa bai yi ba haka ya ƙara shiga mota security ɗaya yaja su suka nufi hospital,
Baiwar Allah hankalin ta ba ƙaramin tashi yayi ganin haka ne yasa Abbah ya dakatar da ita suka tafi iya su biyu daga Abbah sai Roshan da kuma security,
Gaba ɗayan su kuka suka soma yi domin a halin da Roshan yake ciki ba mai cewa yana da rai, haka suka shige cikin gidan tamkar anyi musu mutuwa, duk a falo suka zazzauna Hajiya Kilishi ta zabga uwar tagumi tana tunani kala-kala a ranta, maimakon tazo ta samu kowa cikin ƙoshin lafiya sai kuma ta tarar da wani tashin hankali,
tana cikin wannan tunanin taji Pinky tana faÉ—in "ai duk kece kika jefa shi cikin wannan mun sani, wancan lokacin ma saboda ke ciwon zuciyarsa ya tashi..."
tana nuna Baiwar ALLAH cikin ɓacin rai,
Baiwar ALLAH damuwar da yake kanta ma ya ishe ta haka take zubda hawaye ba ƙaƙƙautawa...
Hajiya Kilishi idonta akan Pinky ta ce "kina ganin halin da take ciki amma kina gaya mata cewa ita ta jawo? mijinta ne fa taya zatayi sanadiyar mutuwar sa, haba Balkisu ki koyi iya magana dan ALLAH...."
Pinky ta ce "to naga bata sonsa wai Uncle Deen take so shine take son hallaka shi..."
Ummy ta ce "innalillahi wai meyasa hakane Aunty Pinky dan Allah ki bar mu da abinda yake damun mu..."
Hajiya Kilishi ta ce "muyi Addu'a Allah ya bashi lafiya shine kawai, a yanzu dai babu wanda yasan gaibu sai ALLAH..."
Suna cikin wannan halin sai ga Ammy ta fito daga part ɗinta tana sanye da hijab har ƙasi da carbi a hannunta, jin motsin mutane ne yasa ta fito domin ganin su waye ne saboda tasan gidan shuru yake ba kowa...
Ƴar tinny ganin Ammy yasa ta rufa da gudu tana faɗin "Ammy nahh..."
Ammy ta rungumi Ƴar tinny tana dariya, tayi matuƙar farin cikin ganin yaran gidan sosai.
Ta ce "Auta ki ka gudu kika barni ko..."
Ƴar tinny ta ce "Ammy wurin Mommyna naje.."
Ammy ta ce "Ayyah fatan kin samu Mommy cikin ƙoshin lafiya ko?.."
Ƴar tinny ta ce "ai tare muka zo da ita, gata can..."
ta nuna ta da yatsa.
Ammy bata yi tunanin har da uwar aka dawo ba domin bata lura da ita ba,
haɗa ido suka yi Ammy tasau murmushi tare da nufan wurin tana riƙe da hannun Ƴar tinny,
tana zuwa wurin ta durƙusa a gaban Hajiya Kilishi tana gaishe ta
Ta ce "ina wuni Aunty, fatan kin iso lafiya..."
Hajiya Kilishi fuska a sake ta ce "lafiya ƙalau Amaryar mu, nagode sosai kin riƙe mun yara cikin mutunci..."
Ammy ta ce "ba komai wallahi, ai Æ´aÆ´a na kowa ne..."
ta cigaba da cewa "ashe kun zo Ni ban san yau zaku dawo ba ai da anyi muku tanadi na musamman..."
Pinky tana farfara ido ta ce "an maida Auren Mommy da Abbah yanzu ta dawo gidan mijin ta..."
Ammy cikin nuna farin ciki ta ce "Masha Allah, Allah mun gode maka, wallahi naji daÉ—in hakan sosai, duk da bai gaya mun ba amma nayi farin ciki..."
Pinky ta ce "ai ba dole ne sai an gaya miki ba..."
Hajiya Kilishi wani irin harara ta wurga wa Pinky tana faÉ—in "bana son iskanci fa, abokiyar ki ce ko kuma dake take maganar ta..."
Pinky kawar da kanta gefe tayi tana tura baki...
Hajiya Kilishi ta kalli Ammy tana murmushi ta ce "wallahi kuwa mu ma bazata akayi mana, ban san da Auren ba sai bayan an É—aura..."
Ammy ta ce "naso ya sanar mun dawowar ku ai, da an shirya muku girke-girke na musamman..."
Hajiya Kilishi ta ce "ayya kar ki damu, mun zo mun tarar da wani tashin hankali, Roshan ba lafiya yanzu haka sun nufi hospital ciwon zuciyarsa ta tashi..."
Ammy dafe ƙirji tayi tana faɗin "subhanallahi wallahi ban sani ba..."
sai yanzu ta lura da Baiwar Allah dake ta kuka fuska tayi jawur,
Ammy tayo kanta tana faɗin "Allah sarki kiyi haƙuri Daughter Insha Allahu zai samu sauƙi..."