← Book details My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 39

Sashe 4

My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaro ido waje Roshan yayi yana kallon Mai martaba,
gaba É—aya jikinsa yayi la'asar kamar ba jini, sai ji yayi mai martaba yace
"Ni ban sanar masa komai ba, yadai gaya mun cewa tareda Minal kuka zo amma ban ce masa bakuzo da ita ba, rashin sanin abinda zan gaya masa ne yasa na katse wayar domin sai naji daga bakin ku tukun na yanke hukunci..."

wani irin sauƙe nannauyar numfashi Roshan yayi yana faɗin "thank God,
sannan yace Uncle zan sanar maka duk halin da ake ciki..."

Mai martaba yace "TOH ina sauraronka..."

Nan Roshan ya sanarwa mai martaba halin da ake ciki na Minal da kuma Mohandas..

Dogon numfashi mai martaba yaja sannan yace "TOH banda abinka Roshan meye zaka iya a wannan lamarin? kadai san halin Mahaifinku idan yace baya son abu TOH kuwa duk duniyan nan bamai sashi yayi, sannan kuma shi Mohandas so kake ya bijirewa iyayensa kenam akan mace?..."

Roshan idonsa akan mai martaba yace "Uncle ina tausaya musu ne, wallahi suna son junansu kuma shima Mohandas ya amince akan zai musulunta, nasan idan ya karɓi musulunci Abbah bazai hanashi Auren Minal ba..."

Murmushi Mai martaba yayi yace "yaro yaro ne, Roshan har yanzu da ƙuruciya akanka, kana nufin kace Abbah zai bawa Mohandas Auren Minal ba tareda iyayensa suna so ba? ko kuma Abbah zai ɗauki yarinya ya bashi ba tareda iyayensa sun sani ba?
TOH bari kaji shi Aure ya wuce yanda kake tunani, ina mai sanar maka cewa Mahaifinku bazai taɓa yadda da wannan al'amarin ba sai dai idan har iyayen Yaron suma sun Aminta nan ne za'ayi abu cikin lumana..."

Roshan Dafe goshinsa yayi yana hura iskar bakinsa tareda jinjina maganganun mai martaba,
ÆŠagowa yayi yana faÉ—in "yanzu ya zamuyi Uncle?..."

Mai martaba yace "ku sake shawara dai..."

Roshan yace "Uncle inason jin daga bakinka duk yanda kace hakan za'ayi..."

Mai martaba yace "sai dai a samu iyayensa ayi magana cikin hankali idan su bazasu musulunta ba to subar yaronsu ya musulunta inyaso sai a Aura masa yarinyar..."

Roshan jinjina kai yayi sannan yace "tabbb! Uncle ai gwara tawa shawarar zai iya yuwa, amma nasan iyayen Mohandas yanda suke riƙe da ƙarfin Addininsu bazasu taɓa yadda ba wallahi...."

Mai martaba ne ya buÉ—e baki zaiyi magana yaji wayarsa tana ringing,
Dubawa yayi yaga number Abbah ne, Saida ya kalli Roshan tukun yace "shine..."

Zaro ido Roshan yayi ya haɗe hannayensa biyu alamar roƙo kar Mai martaba ya gayawa Abbah halinda ake ciki,
Mai martaba ne yasa wayar a speaker yanda Roshan zaiji duk tattaunawar da zasuyi...

Mai martaba ne yayi sallama tareda faÉ—in "na gaida mazan pama..."

Abbah yace "yadai muna cikin waya ka katse ƙiran?..."

Mai martaba yace "wallahi naÉ—anji hayaniya ne shine naje dubowa meke faruwa..."

Abbah yace "okay! yakamata yaran nan su dawo gida yau saboda hidimar bikin da za'ayi yau sauran kwana huÉ—u..."

Mai martaba yace "yau kuma? sai dai gobe su taso da sassafe, saboda har da matan gidan gaba É—aya zasu tafo..."

Abbah yace "TOH shikenam kaifah?..."

Mai martaba yace "a'a Ni sai ana gobe É—aurin Aure zan taho,
Amma Roshan shi kaÉ—ai za'a Aurar ne? mezai hana a haÉ—a da Razhdeen?..."

Abbah yace "kabar zancen Razhdeen shi da bai tsayar da kowa ba, ai baza'a Aura masa babu ba..."

Mai martaba yace "hakane amma maizai hana a haɗa shi da Ramlat ƙanwar Matata Maamie naga tana sonsa sosai..."

Abbah ne yace "shi ɗin yana sonta ne? In har yana sonta sai a haɗa Auren gaba ɗaya, idan kuma Razhdeen baya ra'ayinta TOH gwara Abar maganar nan saboda banason damuwa, kasan halin Razhdeen nima haƙuri nake dashi, kuma ba kowace mace ce zata iya zama dashi ba in har ba sonta yake ba, domin ita zata sha wahala Ni kuma hakan ne banaso..."

Mai martaba dogon numfashi yaja tareda faÉ—in "toh maganar gaskiya dai Hajiya Maamie ce take son haÉ—in nan amma shi Razhdeen baya so domin jiya ma Saida suka samu matsala har Saida Razhdeen ya mareta a take ta sume a wurin..."

Abbah yace "whattt! Ita yarinyar ya mara ?..."

Mai martaba yace "a'ah ita kanta Uwar yarinyar, kasan Razhdeen bashida haƙuri kuma baya son raini ita kuma Maamie rashin kunya da wulaƙanci..."

Abbah yace "kana nufin kace matarka Razhdeen yasa hannu ya mara?..."

Mai martaba yace "No bawai na gaya maka saboda ranka ya ɓaci bane i just tell you that haɗin Auren bazai yu bane tinda ba son yarinyar yake ba..."

Abbah numfashi ya sauƙe yana faɗin "ba abun mamaki bane domin Razhdeen zai Aikata, shiyasa banason tura shi baƙunta wani wuri amma zanyi maganin shi, Please King kayi haƙuri Razhdeen Sam bai kyauta ba..."

Mai martaba yace "wallahi ko a jikina Yaya, kadai san zaman haƙuri kawai nake da ita, ta zamo mun ƙarfen ƙafa..."

Abbah yace "kayi haƙuri idan kuka zo gaba ɗaya za'a san yanda za'ayi..."

Mai martaba yace "TOH shikenam ba damuwa,
Amma Yaya ita kuma Minal fa ya za'ayi da ita yakamata a Aurar da ita tinda ta kammala karatunta..."

Abbah yace "bata da manemi shiyasa..."

mai martaba yace "naji tace tanada wanda take so ai..."

Abbah yace "Arne take so kuma ko zata mutu bazata Auri jinin Christal ba..."

Mai martaba yace "inda zai musulunta sai kawai a Aura mata shi..."

Abbah ya kuma cewa "Da nayi tunanin nan amma yanzu na sauya ra'ayina koda ya musulunta ma Æ´ata bazata Auri jininsu ba, yanda ta fito a cikin Musulunci haka jininta zai cigaba da gudana a cikin Musulunci, banason jikokina su kasance sunada family christoci..."

Mai martaba yace "Yaya wannan hukunci yayi......."
bai ƙarasa maganar ba yaji Abbah ya katse shi da cewa "nafa gama maganata babu sauyi kuma,
idan Roshan yana kusa ka bashi wayar...."

Mai martaba babu yanda ya iya haka ya miƙawa Roshan wayar,
Roshan hannu na kakkarwa ya karɓa tareda karawa a kunne da sallama a bakinsa,
Abbah yace "ina Razhdeen?..."

Roshan yace "na barshi a É—akin kwanan mu..."

Abbah yace "kaje ka same shi kace ya taho Nigeria yanzu yanzu inason ganinsa..."

Roshan yace "TOH Abbah.."

Kafin Abbah ya katse ya kuma cewa "inaso zanyi video call da Minal kaje ka same ta yanzun nan..."

Saida ƙirjin Roshan ya buga jin abinda Abbah ya faɗa,
A birkice ya tsaya yana kallon screen É—in wayar,
bai ankara ba yaga Abbah ya juyar da ƙiran zuwa video call, sai gwala-gwalan idon Roshan ne suka sauƙa akan Fuskar Abbah dake cikin wayar, nan suka fara kallon juna, Abbah ne ya katse shi da cewa "meye kake kallona haka, kaje ka bata wayar ina kallonka..."

Shima mai martaba Saida ya jinjinawa Abbah Sarkin wayo...

Roshan tashi yayi ya fara tafiya da haka yabar falon mai martaba ya fice kai tsaye ɗakinsu ya nufa yana zuwa ya buɗe ƙofa ya shige,
samun Razhdeen yayi yana zaune a bakin gado ya shirya tsab cikin ƙananun kaya ga yanda ƙamshin turare yake tashi,
Roshan yana zuwa ya juyar da wayar saitin fuskar Razhdeen,
wani irin kallo ya watsawa Roshan ganin yanda ya saita masa fuskar waya a tunaninsa photo zaiyi masa ne, sai ji yayi daga cikin wayan ance "Minal nace ka haÉ—ani da ita ba wannan mai kama da mutuwa ba fuska ba annuri...."

Razhdeen idonsa akan wayar ta ciki yake kallon Abbansu, shima Abbah kallonsa yake, daga bisani Abbah yace "kai kuma Razhdeen inaso yanzu ka dawo gida banason dogon zance..."

Kai kawai Razhdeen ya É—aga masa,
Roshan kuwa kasa É—age wayar yayi daga saitin fuskar Razhdeen hannu sai kakkarwa yake,
Abbah ne ya kuma cewa "ina Roshan ya haka ne, nagaji da kallon fuskar Razhdeen haka ka kawar mun da wayar kaje ka haÉ—ani da Minal...."

Roshan wayar ya kawo saitin fuskarsa yana kallon Abbah fuska a jagwalgwale kamar zaiyi kuka,
Abbah yace "ha'a Roshan zan saɓa maka fa, ina wasa dakai..."

A hankali yake jan ƙafa zai fice daga ɗakin kwatsam yaji Abbah yana faɗin "dakata! dakata mun!! Ɗaga mun wayar sama saitin fanka naga abu yana lilo kamar mutum..."

Shima Roshan É—aga kansa sama yayi domin tabbatar da abinda Abbah ke magana akai,
Zaro ido yayi baki a sake ganin Ramlat a ɗaure saman fanka kanta na kallon ƙasi, sawaye kuma a ɗaure da fanka,
Saida ya nannaɗeta da zanin gado kafin ya ɗaureta sannan ya janye ta sama, iya fuskarta ne a waje, bayan ya gama mata dakun sakwara, ba ƙaramin duka yayi mata ba ganan hancinta yanda yake ɗigo da jini,
Dasauri Roshan ya sauƙar da kansa ƙasi yana maida kallonsa kan Razhdeen sai yanzu ya lura da dorinar da yayi kaca-kaca a ɗakin,

Ji sukayi Abbah ya fara salati yana faÉ—in
"Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Razhdeen Koh? Razhdeen Koh? nasan shi yayi mata haka, wayyo Allah ya zanyi da Razhdeen É—in nan,
Kai Roshan miƙawa Razhdeen wayar nan..."

Dasauri Roshan yaje ya miƙawa Razhdeen wayar domin yana so Abbah ya manta da batun Minal,
Razhdeen karɓa yayi tareda kawar da fuska gefe domin bazai iya fuskantar Abbah a halin yanzu ba,
yana jin yanda Abbah yake zaginsa game da cewa
"anya kuwa Razhdeen kai mutum ne? Dan ALLAH ka dawo na kai ka bakin ruwa nafi tunanin kai É—an ruwa ne,
Amma Aljanun nan basu kyauta mun ba, kai kaÉ—ai ne suka canza mun kai, ban saniba ko tin kana cikin uwarka suka É—auke mun Razhdeen ko kuma tin kana jariri,
Bakin ruwa dole saina kaika domin bazan barka kaita kashe Æ´aÆ´an mutane ba...."

Razhdeen kai a gefe kunne ne kawai yake jiyo maganganun Abbah,

Shi kuwa Roshan ya kama kunkumi kansa a sama yanda yake ta kallon Ramlat yana tunanin ta yanda akayi Razhdeen ya É—aureta haka, kuma alamun a sume take domin ko motsi bata yi kodai mutuwa,
haka yake ta wannan tunanin,

Abbah yace "Razhdeen na roƙe ka da sunayen Allah ka dawo Nigeria a yanzun nan dan ALLAH,
Ina Roshan?..."

Roshan ne ya karɓi wayar yana faɗin "gani Abbah..."

Abbah yace "kasan yanda zakayi ka since yarinyar nan..."

Roshan yace "TOH Abbah..."

Daga nan ya katse wayar...

Roshan sauƙe numfashi yayi yana faɗin "yanzu ta ina zan fara?..."

Razhdeen kuwa ko kallonsa baiyi ba balle ya furta wani abu,

suna cikin wannan halin sukaji bugun ƙofa,
Roshan ne yayi ƙarfin halin cewa "waye?..."
Chapter 4 · 0% Book details