← Book details My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 39

Sashe 2

My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Harara ta watsa masa tareda faÉ—in "Duniya kam gani a cikinta ta ishi kowa ma bani kaÉ—ai ba,
Kuma wallahi kusan yanda zakuyi ku Aura wa Razhdeen Ramlat tin kafin ajiyo kan mu, kana maganar wai tace Roshan take so yooo banda na ga, mai Roshan yake da shi, wanda ko rabin kamo ƙafar Razhdeen baiyi ba a arziƙi..."

Sai a yanzu Ramlat ta buÉ—i baki tace "nifah Maamie Yaya Roshan nake so...."

Maamie a fusace ta miƙar da hannu tana danƙwalonta tareda faɗin "ke kin ci ubanki, ina samar miki waran da zakiji daɗin rayuwa ki ƙwanta a dukiya ki tashi a dukiya amma ke kina Kai kanki wurin wahala, mai za'ayi da kishiya banda dole, ALLAH ya tsinewa wanda ya ƙirƙiri sunan kishiya babu daɗin ji,
Haka zamu ƙare rayuwar mu a zuwa kan kishiya?
lokacin da mai martaba zaiyi Auran farko mu biyu ya haɗa ya Aura lokaci guda Ni da Maimuna wacce ba'a san duniyar da take ba yanzu, kafin daga baya ya ƙara Auran wannan matsiyaciyar,
shine ke kikeso kema ayi miki irin nawa? kamar wasu marasa gata da farin jini,
toh bazaiyu ba Razhdeen É—in zaki Aura..."

Mai martaba hannu yasa ya dafe saitin zuciyarsa jin an ambaci sunan da yake tada masa da hankali wato Maimunatu...

Ana cikin wannan halin saiga Razhdeen da Roshan sun shugo falon, duk maganganun da Maamie tayi suna jinta,
Roshan ne yazo har gaban Maamie ya tsaya yana mata kallon ƙurilla daga bisani ya cire glass ɗin kan dara-daran idanuwansa, ya soma magana cikin ɓacin rai yake faɗin
"Alhamdulillah tinda ALLAH ya hore mun abinda zan rufawa kaina asiri, dukiya inada su dai-dain gwargwado kuma fiye da yanda kike tunani, domin da za'a haÉ—a kanki dana danginku gaba É—aya bazaiyi kwatan yawan adadin dukiyarda nake da shi ba, naji É—an uwana Razhdeen ya fini yawan dukiya amma inaso ki sani cewa ko a yanzu nace ya bani rabin dukiyarsa ba musu zai bani saboda mu É—in gudan jini ne, nashi nawa ne haka kuma nawa nashi ne,
Ƙanwarki kuma ki sanar mata cewa koni Roshan bazata samu shiga ba balle my twins da ko ƴar aiki bazai ɗauketa ba balle a matsayin mata..."

Hajiya Maamie kama kunkumi tayi tana kallonsa cike da mamakin maganganun da yake jifarta dasu,

Murmushi tayi tana yatsina fuska tace "Hmmm! Roshan kenam, Ni baka isheni kallo ba, bata kai nake ba ka matsa ka bawa É—an uwanka wuri mu magantu..."

Roshan É—aga kafaÉ—arsa yayi tareda faÉ—in "okay fine! Idan kikayi dashi tamkar kinyi dani ne..."

Ya ƙarasa maganar tareda komawa gefe,
Razhdeen ne ya maye gurbin da Roshan ya tsaya shima yana fuskarta da hannayensa a goye kan ƙirjinsa, fuska a ɗaure ba Annuri.

Maamie itama kallonsa take fuska a sake sai faman sakin murmushi take tace "Razhdeen inaso muyi magana ta fahimtar juna, kaga yanzu mun zama É—aya Ramlat tamkar Æ´ar uwarka ce, kuma ka dubeta ita É—in marainiya ce bamuda uwa babu uba, dan ALLAH ka temaka ka Aureta ko zata samu farin ciki,
Ni zanyi iya ƙoƙarina naga ka Aureta tinda wannan matsolon Sarkin ya kasa aiwatar da komai...."

Saida ta kammala zantuttukanta tass sannan tayi shuru tana son jin amsar da zai bata, itadai addu'arta shine yace ya amince..."

Sakin nannauyar numfashi yayi sannan yace "kin gama?..."

Tace "kai nake sauraro Razhdeen..."

Kafin ta ƙibta ido har ya kai hannu ya zabga mata wani irin gigitaccen marin da bata san lokacin da ta dungura kan kujera tayi tsalle ta faɗa bayan kujerar ba,

Kaf waran babu wanda bai tsorita da wannan marin ba,
hatta shima mai martaba bai san lokacin daya miƙe tsaye ba, ita kuwa Ramlat bata san ta zamo daga kan kujerar da take ba, ta kafa gwiwowinta a ƙasan carpet,
Itama INDO ja da baya tayi tana zazzaro ido waje hannayenta a toshe da bakinta,
Shima Roshan bai taɓa tunanin Razhdeen zai iya marinta ba, abun yayi matuƙar bashi mamaki sosai kuma ya jinjina wa zafin ransan nan...

Maamie tana kwance a bayan kujera shuru bata É—ago ba har zuwa wannan lokacin,

Mai martaba murya na kakkarwa yace "Razhdeen meka aikata haka? shin bakada hankali ne? Matata ce fah? ka manta yanda nake a wurinka?..."

Cikin ɓacin rai Razhdeen yake kallonsa tareda faɗin "bana juran ganin irin waɗannan dabbobin matan, saboda haka ne yasa bana zama inuwa ɗaya da matar Abbanah saboda nasan wata rana zan iya illata ta, duk da yanzu naji labarin basa tare, don haka itama wannan tabi a hankali kafin nabar ƙasar nan..."

yana kammalawa ya juya zai fita shima Roshan bin bayansa yayi zasu fice a tare,
Juyowa Roshan yayi yana kallon Mai martaba cikin tausayawa yace "Uncle akwai ɗauri a jikin ka Please ka nemi maganin karya asiri domin ba haka aka barka ba, Uncle wanda na sani a baya bakai bane yanzu, duk zafin ran Abbanah baiyi ka ba amma yau kaine nake gani haka mace tafi ƙarfinka? Amma zan tayaka da addu'a karka damu...."

yana kammalawa shima ya fice, kai tsaye part É—in su suka nufa...

Mai martaba girgiza kai yayi domin al'amarin yana shirin fin ƙarfinsa,
kallon yanda INDO take yayi sannan yace "ki kai musu abinci basu ci komai ba tinda suka zo, sannan ki lallamesu su ci karsu zauna da yunwa..."

Amsa masa tayi cikin girmamawa ta wuce kitchen,

yana tsaye yaji kukan Ramlat tana faÉ—in "Abul ta mutu kazo ka duba ta bata motsi wayyo Allah nahhhh..."

tana kuka sai faman jijjigata take amma Maamie ko motsi babu, Saida mai martaba ya zagayo bayan kujerar ya tarar da ita kwance ga fuska har ya kumbura,
a hankali ya furta cewa "kije ki É—auko mun ruwan sanyi.."

Da gudu Ramlat ta miƙe taje frig ta ɗauko jug mai ruwan sanyi ta kawo,
ana watsa mata kuwa ta farfaɗo tana sauƙe numfashi sama-sama,
tareda faÉ—in "aina nake? ina ne Nam? gida nake son zuwa.."

Daƙer mai martaba ya ɗagota sannan ya wuce da ita bedroom ɗinta tana sumbatu cikin rashin hankali domin ji take kanta yana juyawa bata san a yanda hankalinta yake ba, da haka aka shige da ita ciki...

*A TANTANCE MUN*
*SHIN DA HAJIYA MAAMIE DA KUMA HAJIYA KILISHI WACCE TAFI WULAƘANCI????*

asmeetah writer ✍️

*MY ENEMY _*

🫦 مقىينا 🫦

Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳

Asmeetah (giaÉ—e writer)

STEP TWO

sorry for the mistake a farkon step two nasa 51 to 52 maɗorin ƙarshen step one neh, naga wasu suna mun complain akan anyi musu nisa sosai a step two, toh ba haka bane farkon ne, but yanzu zamu cigaba akan page 3 and 4 na step two

*Chapter* 3 and 4

Mamie kamar wata zautacciya haka ta rikice bata san yanda kanta yake ba,
lalume ta fara yi tareda faÉ—in "ina Ramlat? Ramlat kina ina bana gani dai..."

Ramlat ce ta zauna gefenta a bakin gado ta riƙo hannayenta tana faɗin "Aunty gani nan dai..."

Maamie tana kuka tana cewa "duba mun akwai fuska a jikina?.."
Ramlat tace "akwai fuska mana"
Maamie ta kuma cewa "ki duba da kyau shin ba'a rabe mun kaina da gangan jikina ba? yanzu haka kina kallon fuskata? naga duhu nake gani sannan banji alamun kai a jikina ba..."

Ramlat tace "haba Maamie ai duk ke kika jawo haka, gashi kema Uncle Deen bai barki ba balle Ni,
shin har yanzu kina kan bakarki ne? gashi kinyi mun biyu babu shima Yaya Roshan ɗin yana shirin kuɓuce mun..."

Maamie tace "kina nufin kice ba Razhdeen zaki Aura ba? toh wallahi tallafi ko naman jikina yake yanke wa kullum saina sa ya Aureki dolensa..."

"Hmmm! kece a wahalai nidai zanbi tawa hanya yanda bazan jawo a illatani ba...". a cewar Ramlat.

Maamie cewa tayi "au ina nema miki gidan daɗi ke kuma kina mai watsa mun ƙasa a ido?..."
cikin ɓacin rai Ramlah tace "shikenam Aunty Maamie kiyi duk yanda kika ga ya dace..."
tana kaiwa nan tayi ficewarta,

Maamie cikin É—aga murya tace "Ai kuwa zanyi abinda ya dace idan naje wurin Boka matsagwal, wallahi sai Razhdeen yazo yana binki har da tsuguno..."
ta ƙarasa tana jan numfashi sama-sama ga fuska yanda ya kumbura suntum har shatin photon hannunsa ake gani akan fuskar...

🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️

ƳAR AMANA tana zaune a yanda suka saba hallaruwa tana riƙe da jitar ta sai kaɗawa take,
Dake duk mutanen wurin ba wanda baya jin daÉ—in sautin jitarta,
tana cikin wannan halin sai ga wata danƙararriyar mota baƙa ƙatuwa wasu matasa ne su biyu suka fito suna rufe da fuskokinsu da baƙar hula suka yo kan Ƴar Amana dake zaune,
duk waran babu wanda bai tsorita da ganinsu ba domin har da masu riƙe da bindiga, ɗagowa tayi tana binsu da kallo kafin ta ankara har sun finciko hannunta, sun ɗagata sama tana bubbugan bayansu haɗe da shure-shure amma ba bakin yin ihun,
kafin kace mai tsofin wurin sun haɗe waran da kururuwan "wayyo ɓarayi mun shiga uku, akawo mana ɗauki ƴan fashi...."
Nan danan suka ja motarsu a É—ari suka bar wurin,
daman sun juma suna target É—inta tin barinta a hannunsu ogansu ya hura musu wuta akan sai sun nemota sai yau Allah ya bada sa'ar kamata...

Cikin Daji aka nufa da ita already sun rufe mata fuska da baƙin ƙyalle..

🤏Baiwar ALLAH tin da Aunty Yolash tazo take faman gyarata irin gyaran Amare duk da bata son Auren ko kaɗa, har ila yau fuskar Razhdeen ne yake mata gizo, wani sa'in sai taji kamar ta fita taje ta nemo Razhdeen ta roƙe shi akan ya Aureta,
kwata-kwata batada wani sukuni, ba wai bata son Roshan bane Ita dai zuciyarta Razhdeen ya zaɓa mata kuma shi yafi dacewa da ita amma babu yanda ta iya...

Minal kuma tana can gidan Razhdeen ita da Mohandas ita take masa girki duk da bata iya sosai ba sai ya saka mata hannu, wani sa'in kuma shi yake yi da kansa,
Soyayya iya soyayya suna shanta sun fahimci juna sosai domin har Mohandas ya amince akan cewa bayan bikin Roshan shima zai musulunta sannan a ɗaura musu Aure a ɓoye in har Abbah bai amince ba....

Misalin ƙarfe 2 na dare Roshan ya yi sujjada yana sallar lafula, shi kuwa Razhdeen yana saman gadonsu yana karanta karatun Alkur'ani mai girma.
Chapter 2 · 0% Book details