Sashe 27
My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aunty Yolash ta ce "hakane kamar yanda kike gadarar gidan mijinki ne haka Nima nake gadara da gidan Yayana ne uwa ɗaya uba ɗaya, kuma hasali na fiki iko da gidan domin ke ko a yanzu aka baki takardar saki dole ki bar gidan, kuma mu ƙi maido ki in juninki rashin mutunci ne..."
Maamie ta ce "ai wallahi bari kiji ni da gidan nan Auren zobe ne ba rabuwa sai dai mutuwa, in hassada kike mun ma gwara ki shanye abun ki..."
Suna cikin wannan cacar baki sai ga Mai martaba ya shugo da sallama a bakinsa domin ya gama sallamar baƙin da yayi a falon masarautar,
zama yayi yana fuskantar Aunty Yolash da murmushi akan fuskarsa domin ba ƙaramin farin ciki yayi ganin Autar ɗakinsu ba, gaisawa suka yi sannan ya ce "Yolash mutan boko yau ɗin boko ya barki kin kawo wa ɗan uwanki ziyara kenam..."
Aunty Yolash ta ce "Yaya mai martaba inason zuwa daman amma É—awainiya sun mun yawa..."
Mai martaba ya ce "yanzun ma nasan akwai abinda ya kawo ki ai tinda ban ganki da akwatin zaman hutu ba..."
Dariya tayi ta ce "wallahi a yau zan koma sai kuma idan na tashi zuwa da akwatin zan zo nayi muku hutu sosai..."
Murmushi yayi tare da faÉ—in "Allah sarki Æ´an uwa daÉ—i..."
Itama murmushi tayi.
Mai martaba ya ce "fatan dai kinci abinci ko?..."
Ta ce "tin zuwa na Aunty Amarya ta kawo mun ina ci muna shan hira da haka na kammala..."
Ya ce "Masha Allah haka ake so ai, yanzun me yake faruwa ne?..."
Aunty Yolash ta gyara zama ta kwashe duk halin da ake ciki na Abbah da Hajiya Kilishi ta sanar masa, ta cigaba da cewa "Mai martaba ko dan Æ´aÆ´anta a dawo da ita duk da yaran sun mallaki hankalin kansu, itama kanta Kilishi zata fi nutsuwa, a halin da take ciki inta cigaba da zama a haka ba'a san mai zata aikata zuwa gaba ba tinda indai wahala tayi wahala mutum zai fara neman mafita, to mafitan ne ba'a wani iri za'a nema ba, tinda ta nemi yafiyar mutane ta gyara halayenta sai a dawo da ita..."
Mai martaba tayi gyaran murya sannan ya ce "hakane duk naji batun ki Insha Allahu zan je na samu Chief da maganar, sai dai matsala shine ba lallai ya aminta ba, kar yazo yana faɗa mun maganganu ne kinga shine gaba da Ni, kuma waɗanda suka girme shi ma bai fi maganar su ba, baffanun mu sun same shi da maganar amma fur yaƙi to ba lallai ne Ni ɗin ma yaji ba..."
Aunty Yolash ta ce "a'a Yaya mai martaba kar ka karaya kaje ka lallame shi akan batun dan ALLAH..."
Ya ce "toh shikenam idan kin tashi tafiya sai mu tafi tare Nima inaso na dawo a yau saboda inada uzurirruka a gabana sosai..."
Aunty Yolash ta ce "ai Ni yanzu zan tafi..."
Ya ce "to mu tafi tare..." duk suka miƙe akan zasu tafi,
Maamie tana zaune ta ce "shikenam yarinya ƙanwar bayanka tazo zata kwashe ka ku tafi ba irin ɗan bada girman nan...".
Mai martaba ya ce wa Aunty Yolash "ki sharar da ita kawai mu tafi..."
Aunty Yolash bata kulata ba domin tasan inta biye mata zasu kaure da faÉ—a ne yanzu kuma bata da lokacin ta, haka suka fice Indo ta raka su har wurin parking, suka shiga mota security ya jasu suka tafi airport.....
Bayan sun koma Nigeria, Mai martaba ne ya shiga gidan Chief ɗaya daga cikin sojoji wani ya kaishi har ciki da mota, ita kuma Aunty Yolash tana daga waje a cikin mota taƙi shiga gidan domin ba ƙaramin ɓata mata rai Abbah yayi ba,
Mai martaba ne yake zaune a falon Abbah shima Abbah É—in yana nan anyi dace yau bai fita ba, bayan sun gaisa ne Mai martaba ya ce "a gaggauce nazo domin a yau nake son komawa Jidder..."
Abbah cikin nuna farin ciki ya ce "Tinda kuwa hakane nasan kaima akwai abinda ya kawo ka..."
Mai martaba ya ce "sosai ma kuwa shiyasa ka ganni nayi zuwan bazata ai..."
Murmushi Abbah yayi sannan ya ce "Yolash taje ƙasar da kake ko? nasan ƙarata takai kaima kazo kayi mun maganar wancan matar da yanzu ji nake kamar na hallakata ko ....?
Mai martaba ya ce "duk abinda haƙuri bai baka ba rashin sa ba yanda za'ayi ya baka, duk abinda yayi tsanani a rayuwa haƙuri shine maganinsa, kuma ita gaskiya ba'a faɗa da ita, bai kamata ace duk wanda zai gaya maka gaskiya kayi faɗa da shi ba, kuma duk wanda zai yi maka nasiha akan abinda zai fissheka to kayi haƙurin zama dashi koda baka jin daɗin zama da shi ɗin, Ni nazo ne akan na baka shawarwarin da zai taimake ka a rayuwa a mazannina na ɗan uwanka bawai don na kai bane, ita wannan matar da kake gani tayi abubuwa da dama a rayuwa na rashin tunani amma yanzu da rayuwa ta sauyata mai ya kamata ayi mata? sai a yafe mata sannan a cigaba da zama da ita tinda ta gyara kurkuren da ta aikata..."
Bai ƙarasa iddasa maganarsa ba Abbah ya dakatar da shi da cewa "shin na tambaye ka mana...?"
Mai martaba ya ce "inajinka Chief.."
Abbah ya ce "shin ba'a mutuwar Aure ne?..."
Mai martaba ya ce "Anayi mana amma a dole badan ana so ba..."
Abbah ya ce "to kuwa tinda na rabu da ita har abada bazan ƙara kallon yanda take ba balle tayi tunanin zan maido ta, kuma wallahi zanje na sameta ta fita shirgi na, ta daina bibiya mun ƴan uwa idan ba haka ba zan yi mata abinda batayi tunani ba, kuma da kuke cewa saboda ƴaƴanta na dawo da ita shin a tsirara kuka ga ƴaƴanta? ko kuma barinsu nayi da yunwa? to ko su yaran su ɗauka cewa uwarsu ta mutu domin baza su ƙara kusantar yanda take ba kada ta shafa musu baƙin hali da dabbanci, na rantse da sarkin dake busa mun numfashi duk wanda ya ƙara mun maganar na dawo da Kilishi wallahi sai nayi shara'a da shi domin bana son harkar shishshigi, kuma ko kaine idan na sake jin kayi mun maganar na dawo da ita wallahi zan yanke alaƙata da kai har abada..."
Mai martaba cike da mamaki yake kallon Abbah ya ce "Subhanallahi abun bai kai ga haka ba, Allah ya huci zuciyarka Ni zan koma yanda na fito, na barka lafiya..."
Mai martaba fita yayi yana fita ya tarar da Ummy a tsugune sai faman kuka take, tsugunawa yayi tare da É—ago kanta yana faÉ—in "Uwar masu gida ki kwantar da hankalin ki insha Allahu mamanki zata dawo..."
Ta bayansu Abba ne ya fito yana faÉ—in "sai dai su haÉ—u a lahira domin ita da mahaifiyarta sai a mafarki, duk photunan Kilishi nasa an fitar mun da su a cikin gidan nan, a duniyar nan babu macen da ta sa hannu ta mareni sai ita na tsane ta..."
Ummy cikin ɓacin rai ta taso tana kuka ta ce "wallahi Abbah banda sai a lahira kam, mahaifiyar mu tana raye amma ka haramta mana ganinta? duk ƙiyayya ai bazai sa ka raba mu da ita ba, idan kai baka sonta ai mu muna sonta tinda har ta shayar damu ruwan nonon jikinta..."
Abbah a fusace yayo kanta zai dake ta Mai martaba yayi saurin riƙo shi yana faɗin "a'a banda dukan uwar masu gida domin daga baya zakayi nadama..."
Ummy da gudu ta koma cikin babban falon gidan tana kuka, Ammy tayi rarrashin duniyan nan amma taƙi daina wa..
Abbah a fusace ya shugo yana balbala masifa ya kalli yanda Ummy take ya ce "ina kema kin koyi rashin kunya irin na yayunki dana uwarki ko? to kar ma ki fara domin karya ki zanyi a cikin gidan nan, ke har nawa kike? Uwar ki ce bazaki ƙara sakata a idonki ba na gaya miki..."
Bayan ya gama surutansa ya haura part É—insa, Ammy ce ta cigaba da rarrashinta...
Mai martaba bayan ya fita motar Aunty Yolash ya shiga rai a ɓace, Aunty Yolash murmushi tayi domin tasan matsalar shiyasa bata shiga ciki ba domin zata iya yiwa Abbah rashin kunya..
Airport suka nufa anan ta sauƙe Mai martaba kafin ya shiga jirgi ya kalli Aunty Yolash ya ce "zaku daɗe baku ganni anan Nigeria ba..."
yana kaiwa ya shige jirgi, ita kuma Aunty Yolash wuce wa tayi kai tsaye Suleja taje daga nan ta wuce Bauchi...
★★★★★★
Bayan Aunty Yolash ta samu Hajiya Kilishi a garin Suleja zama sukayi suka tattauna akan maganar Abbah,
Aunty Yolash kamar zatayi kuka ta ce "Hajiya Kilishi shawaran da zan baki shine ki cire Abban yara a ranki domin bazai taɓa mai dake gidansa ba, ki duba kika irin wulaƙanci da yayi mana Ni da mai martaba abun ba daɗi, kuma ya rantse cewa bazai taɓa kusantar yanda kike ba to kuwa kinga babu amfanin kiyi ta bibiyansa yana wulaƙanta ki, shi kaɗai ne namiji? ko shi ɗin ɗan gwal ne, to bari kiji inda nice wallahi ko ɗan gwal ne bazan kalli yanda yake ba balle ya samu damar wulaƙanta Ni, Ni mamaki ma kike bani har kina bibiyansa kina roƙonsa cab aini namiji baka isa ka samu wannan damar ba, bazan taɓa roƙon namiji abu shi kuma ya tsaya yana mun Rashin kunya ba.....
asmeetah writer âœï¸
🤦â€â™€ï¸ *MAƘIYI_NAH*🤦â€â™€ï¸
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء Ù…ØÙ…د أولا 🥳
Asmeetah (giaÉ—e writer)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 âœï¸
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan Æ™asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauÆ™i_.âœï¸
STEP TWO
👇
*41_ TO_45*