← Book details My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 39

Sashe 10

My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk shuru suka yi saboda ba mai iya tanka mata, tsoron Ramlat ake saboda Hajiya Maamie domin ba ƙaramar masifaffiyar mata ba ne, yanzu sai ta iya hargutsa taron bikin,
Ummy uwar masu gida wacce jugowarta cikin É—akin kenam, kalmar da Ramlat ta furta ne ya daki dodon kunnenta, ai kuwa nan itama ta buÉ—i baki ta ce "dabbobin suna da yawa ai amma sai dai wacce take agolanci tafi dabbobin dabbanci..."

Ramlat miƙe wa tayi tsaye tana bin Ummy da kallo cike da mamaki ta ce "Ummy Ni kike ƙira da Agola?..."

Ummy ta ce "to ƙarya akayi miki ne? ko gidan Uncle mai martaba da kike zaune a gidan Ubanki ne shi? kin samu matsayi ne albarkacin zaman da kike a gidan sarauta amma in ba haka ba kin isa ki buɗe baki kiyi wani maganar banza ne anan, duk mutanen da kike gani acikin gidan nan duk jini ɗaya ne babu bare sai ke, Yayarki ce matar mai martaba ita kuwa ba haihuwa take ba hakan yasa ta jawo ki gidan sarauta kizo ki ci arziƙi babu a house..."

Ramlat ita kaɗai tasan takaicin da take shaƙa a yanzu buɗar baki tayi ta ce "au gorin haihuwa zakiyi wa Aunty nah? eh naji bata haihuwa amma ai ta kama kanta tana zaune a gidan mijinta, wata uwar kuma zubar da ƴaƴanta tayi take bin yawon hotel..."

Ramlat tana kammala fitar da abinda ke ranta tayi saurin barin room É—in domin tasan uwar Ummy ce take yawon hotel,
wani abu mai kama da kibiya ne ya soki saitin zuciyar Ummy tsabar takaici da baƙin cikin har an fara mata gori akan mahaifiyarta,
Da sauri ta juya zata bi bayan Ramlat taji an riƙo ta juyawa tayi taga Baiwar ALLAH ce take ta faman girgiza mata kai alamar karta biye mata,
Ummy tsabar takaici bata san lokacin da ta rausa uban ihu ba tare da durƙusa gwiwowinta ƙasi, duk mutanen ɗakin ne suka rufu kanta suna bata haƙuri akan abinda ya faru, Ummy kuwa kuka take ko sauraron su bata yi domin abun da ciwo ta sanadiyar haka yasa Mahaifiyarta tabar gidan Mahaifinsu,
Jin Ihun ya jawo hankulan wasu daga cikin mutanen gidan, Aunty Yolash ce first É—in shugowa dake tana kusa da É—akin sai ga Rukky da Pinky wacce ba'a daÉ—e da fito da ita daga É—akin duhu ba,
Ummy tambayarta ake meya faru da ita amma babu bakin magana sai waÉ—anda akayi a gabansu ne suka faÉ—i duk abin da ya faru, sam babu wanda yaji daÉ—in abinda ya faru a cikinsu,
Baiwar ALLAH dake tsaye ta kama kai tayi shuru sakamakon wani irin Jiri da hajijiyar da take ji, kanta ne yake mata wani irin matsanancin ciwo, ko kaÉ—an bata son hayaniya a halin da take ciki yanzu domin ba isasshen lafiya gareta ba,
a cikin tana jurewa har ƙarfinta ya ƙare ta yanki jiki ta faɗi a wurin, daga lokacin bata san ina hankalinta yake ba domin alamun suma tayi,
sai kuma kallo ya koma kan Amarya, nan da nan magana ta bazu cewa "Amarya ta yanki jiki ta faÉ—i ga babu maza a gida duk taron mata ne...

Ramlat kuwa ɗakin su ta shige ita da Auntyn ta Hajiya Maamie, tsaya wa tayi tana huci a yayin da Hajiya Maamie take zaune a bakin gado sai shan kwalliyarta take, ganin Ramlat a cikin wani hali yasa ta cewa "ke kuma lafiyar ki ƙalau kuwa?.."

Ramlat ta ce "ina kuwa lafiya Aunty Maamie, wannan ƙaramar Yarinya tana shirin raina mun wayo..."

Hajiya Maamie ta ce "koma wacece meyasa baki ci ubanta ba sai kuma kizo kina mun cika baki aikin banza kawai, ai indai bazaki buɗe baki kici mutuncin mutum ba to ke da raini kuwa yanzu kuka ƙulla, wai ma wacece yarinyar?..."

Ramlat ta ce "Ummy mana kodan a gidan ubanta take ne shiyasa zata nemi ta ci mun mutunci, har wani ƙirana take da Agola ke kuma ta ce bakya haihuwa..."

Hajiya Maamie data bugi ƙasa da ƙafarta ta wani narka uwar ashar ta ce "buuuuro uban nan, ke kuma me kike ce mata dan durun uwarki?..."

Ramlat ta ce "ce mata nayi ai kinfi uwarta da take yawon bin hotel tinda ke kin kama kanki kina zaune da mijinki..."
Hajiya Maamie washe baki tayi tare da faɗin "kin burge ni da kika gaya mata haka, kinga gaba bazata sake miki gori ba tinda abun gori yana gindin su, ai wallahi da baki tamka mata ba saina zabga miki mari sannan na kora ki garin Kaka can ƙauye..."

Ramlat ta ce "cab ɗin ai wallahi bazan iya zaman ƙauye ba hakan ma a wurin Kaka,
wai ma Aunty Maamie ya batun Aure na ne kam? an fasa ne?..."

Hajiya Maamie taja dogon numfashi tana hura iskar baki ta ce "ai ki bar batun nan kawai, domin sai bokan nan yayi mun aiki tuƙuru akan Razhdeen, ko ba yanzu ba za'ayi Auren, a duniyan nan babu wanda tsafi baya kamashi don haka ki kwantar da hankalin ki, domin idan muka cika yin maganar tsab Razhdeen rabaki zaiyi da duniyan nan gwara mu bi komai a hankali ba'a gaggawa da rayuwa..."

Ramlat ta ce "Ni dan Allah kibar batun Uncle Deen É—in nan, mu koma kan Yaya Roshan ni nafi son sa wallahi, kuma kinga shi da wuri za'a iya shawo kan sa..."

Hajiya Maamie ta ce "Dan ubanki Roshan É—in da aka tafi É—auro masa Aure shine zakiyi batun sa? ki bar komai a hannu na dole fa sai Razhdeen ya Aure ki..."

Ramlat ta ce "wallahi ban gama warkewa da dukan da yayi mun ba, har yanzu gaɓoɓina ciwo suke mun hakan ma ki duba yanda ya ɗaure ni a saman fanka kamar wata lauje, Ni gaskiya bazan iya zama da Uncle Deen ba..."

Hajiya Maamie har ta buÉ—e baki zatayi magana suka ji kururuwa a falo, hayaniya duk ta baza ko ina na gidan, da sauri suka fice domin gane wa idonsu,
suna fita suka tarar an fito da Baiwar ALLAH a sume, wasu sun riƙe hannayen ta biyu wasu kuma sawaye da haka suka fito da ita,
Aunty Yolash ce tayi gudun shiga room É—inta ta É—auko key É—in motar ta zata kai ta hospital,
A ruÉ—e take faÉ—in "dan Allah ku taya ni É—aga ta mu kai ta wurin parking kunga ba maza a gidan sannan duk sojojin ma babu wanda aka bari..."

wata tsohuwa ce ta ce "wai ma duk meya jawo haka ne..."
Ummy tana kuka ta ce "duk ata sanadiyar waccan Agolar yarinyar ce..."
ta ƙarisa maganar tare da nuna yanda Ramlat take tsaye.

Ramlat kama kunkumi tayi ta tari yawun ta da cewa "Hmmm! Allah na gode maka a iya Agolanci na tsaya, ke bari kiji in banda tsautsayi da kuma tsananin soyayyar Yaya Roshan a cikin zuciyata ba mai zai sa na tsaya haÉ—a kishi da wannan yarinya mai kama da farar goÉ—iya..."

Ummy ta ce "ai wallahi ko mata sun ƙare a duniya Yaya Roshan ba zai taɓa Auran ki ba domin bakya cikin lissafin tsarin matan da yake so..."

Ramlat tayi dariya tare da tafa hannayenta biyu tana faÉ—in "ai kuwa you should see what am going to do yarinya, Yaya Roshan Auren ta kawai zai yi amma ainihin shi É—in nawa ne..."

Pinky dake wurin ta ce "wai duk akan wancan marar asalin ake wannan ce ce ku cen? Lallai kun haÉ—u da aiki..."

Rukky itama buɗar baki tayi ta ce "ai daman tsautsayi da ƙaddara ne zai sa Yaya Roshan Auren marar asali..."

Ramlat ta kalle su tare da sau wata ƙayatacciyar murmushi ganin an goya mata baya ta ce "yawwa ƴan gari shiyasa nake ƙara ji da ku twins saboda akwai faɗan gaskiya sannan bakwa goya wa ƙarya gindi..."

Rukky ta ce "Ni fa dalilin da yasa bana ƙaunar Baiwar ALLAH saboda Abban mu ya fi nuna mata kulawa, bai damu da mu kamar yanda ya damu da ita ba, ni kuma inada kishi gaskiya..."

Pinky ta tari yawun ta da cewa "ni kuma daman can bata raina, haka kawai nake jin tsanar ta wallahi, na rasa mai Yaya Roshan ya gani a jikin ta har ya nace akan Auren ta..."

Ummy tana zaune akan kujera ta kifar da kanta akan gwiwowin ta tana jin duk tsegumin da suke amma ta kasa tanka musu,
Aunty Yolash kuwa daman ko tsaya sauraron su bata yi ba tin tinin sun fice da Baiwar ALLAH, a can wurin parking suka tsaya ganin an tsayar da wata jibgegiyar baƙar mota, cikin nuna damuwa Aunty Yolash ta ce "yawwa ga Razhdeen ya zo..."
Da gudu ta nufi wurin da yayi parking motarsa ko fito wa bai samu damar yi ba,
zuwa tayi ta fara ƙonƙosa masa murfin motar domin tasan halin sa kafin ya fito sai ya ja musu aji,
ganin tana shirin takura masa ne yasa shi fitowa fuska a turnuƙe ba alamun annuri, kafin ya buɗi baki ya yi magana har Aunty Yolash takai ƙarshen maganar ta tana faɗin "dan Allah Razhdeen ka taimaka ga can Amarya a kwance ta faɗi, kuma kaga ba wani namiji a gidan..."

kallon gefen ido ya yi mata tare da faÉ—in "zanje É—aurin Auren twins ne, tinda kun fito da ita ku kaita mana..."
yana kaiwa ƙarshe ya juya zai shige motar sa Aunty Yolash tayi saurin riƙo hannun sa tana faɗin "wai kai wani irin murɗaɗɗen mutum ne kam, ga can yarinya rai a hannun Allah amma kai ko a jikin ka? na tabbata inda Mijin ta ne kafin na ƙarasa magana ta zai nufi yanda take..."

Razhdeen haÉ—e gira ya yi tare da faÉ—in "Mijinta fa kika ce, ba Razhdeen ba don haka sai ku jira mijin natan ya dawo tinda muharramar sa ce..."

Aunty Yolash fuska É—auke da damuwa ta ce "Please Razhdeen ka taimaka dan Allah, ba dan ni ba..."
Chapter 10 · 0% Book details