← Book details My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 39

Sashe 23

My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

STEP TWO
👇
*31_ TO_35*

_________ONE YEARS AGO_________

Abbah yana zaune a babban falo tare da iyalansa, Ammy da Uwar masu gida da kuma Ƴar tinny dake kwance saman cinyar Ammy matar Abbah domin yanzu har ta fitar da Momminta daga cikin zuciyarta, dake tana samun kulawa sosai a wurin Ammy lokuta da dama tare suke kwana shi kuma Abbah ya koma part ɗinsa,
Suna zaune a falon sai ga Roshan da Baiwar ALLAH sun shugo falo a tare bakin su É—auke da sallama daman wasu lokuta sukan zo ziyarta su Abbah duk da a gida É—aya suke...

zama suka yi suma bayan sun gaggaisa da su Abbah, Ammy da murmushi akan fuskarta ta kalli Baiwar ALLAH ta ce "Daughter Abbah meyasa kwana biyu bakya shugo wa ne?..."

Baiwar ALLAH kai a sunkuye ta ce "wallahi Ammy bana jin daÉ—in jiki na ne shiyasa..."

Ammy ta ce "ayyah ban sani ba ai da zan je na duba ki, kuma naga Ummy tana zuwa part É—inki amma bata sanar mun ba..."

Baiwar ALLAH ta ce "ai itama bata sani ba..."

Ummy uwar masu gida tana gefen Abbah cikin zolaya ta ce "kodai kodai mun samu ƙaruwa ne..."

Zaro ido waje Baiwar ALLAH tayi
tana faɗin "ƙaruwar mai?..."

Ammy ce ta fara yin dariya ganin kallon da Abbah yake yi wa Uwar masu gida har da taguminsa jin yanda ta taƙarƙare ta zuba zance, girgiza kai yayi tare da faɗin "Allah ya shirya mun ke Mamana..."

Rufe fuska tayi tana dariya domin sai yanzu take jin kunyar abinda ta faÉ—a...

Ita kuwa Baiwar ALLAH kallon Roshan tayi ta gefen ido tana maganar zuci cewa "taya zan samu ciki alhalin a ƙaurace muke da juna, yau tsawon shekara guda da Auren mu amma ko a gado ɗaya bamu taɓa kwanciya ba, abun yana damu na wallahi, shi ya ce indai bani na neme shi ba bazai taɓa nema na ba, Ni kuma kunyar hakan nake, hmmmm! meye makomata a wurin Ubangiji na? shin laifi nake aikatawa kodai? dole zan nema wa kaina mafita domin a halin yanzu ina matuƙar ƙaunar mijina Roshan, yafi mun duk wani namijin da zan Aura, bazan taɓa rabuwa da kai ba Roshan..."

Shi kuwa Roshan Abbah ne yake tambayarsa cewa "ina dai babu wata damuwa a tattare da zamantakewar ku na Aure?..."

Da murmushi akan fuskar Roshan ya ce "babu komai Abbah muna zaune cikin ƙoshin lafiya..."

Ya ƙarasa maganar yana kallon Baiwar ALLAH wacce itama shi ɗin take kallo domin yasan tana cikin damuwa na rashin son zama da shi wanda ba hakane a ranta ba, Baiwar ALLAH ta kasance mace ce mai zurfin ciki sai dai abu yaita damunta a ranta amma bazata iya sanarwa ba, ita a ranta tana son Roshan ya kasance da ita a matsayin matarsa ta Aure, burinta shine su zauna su cigaba da soyayyarsu kamar yanda ma'aurata suke kowa a cikin farin ciki,

Roshan ganinta a cikin damuwa hakan na nuna masa cewa haƙurin zama da shi kawai take, especially idan ya tuno cewa twins ɗinsa take so, cije lips ɗinsa yayi yana kukan zuci domin yana da kishi sosai wanda bazai iya cigaba da zama da ita a haka ba, shi har yanzu baya ɗaukar kansa a matsayin mai Aure domin duk abinda ake samu a cikin Aure har yanzu bai same shi ba...

Ko wannen su da abinda yake tunani a ransa, ita Baiwar ALLAH tana tunanin neman mafita yanda zata nasar masa cewa tana masifar son sa, shi kuma yana tunanin lokaci yayi kawai ya rabu da ita...

Bayan nan Roshan ne ya tashi tare da faÉ—in "Abbah zan wuce wurin aiki na sai na dawo..."
Abbah ya amsa masa cikin kulawa da cewa "Allah ya kiyaye a dawo lafiya..."

Shima Abbah tashi yayi yabar musu falon suka cigaba da hirar su, ita dai Baiwar ALLAH a dole take iya yin magana...

____________________________________

Aunty Yolash ce take zaune a wantalelen falon ta dake garin Bauchi tana tare da wata ƙawarta wacce ta kawo mata ziyara,
Knocking ƙofar falo aka shiga yi murya ciki-ciki Aunty Yolash ta ce "waye?"
Daga waje ne Mai gadinta ya ce "Hajiya kin yi baƙuwa ne..."
ta ce "daga ina?..."
Mai gadi ya ce "wallahi ban sani ba Hajiya..."
ta ce "ok ka ce ta shugo..."

Mai gadi ya amsa mata tare da komawa bakin gate..

Aunty Yolash suna zazzaune suka ji an turo ƙofa da sallama a bakin matar da ta shugo, cike da mamaki Aunty Yolash ta miƙe tsaye baki ya gagara rufuwa ta ce "wa nake gani kamar Hajiya Kilishi..."

Hajiya Kilishi murmushi tayi tana faÉ—in "wallahi Ni ce, kinyi mamakin gani na a garin Bauchi ko?..."

Aunty Yolash ta ce "gaskiya kam saboda naga baki taɓa taka ƙafarki kinzo mun ba, nasan yanzun ma uzurinki ne ya kawo ki..."

Hajiya Kilishi ta ce "ai ko ba uzuri zan iya zuwa miki ai..."

Aunty Yolash taɓe fuska tayi ta ce "Banga alama ba saboda tin ana tare ma baki zo ba balle yanzu da ba'a tare..."

Hajiya Kilishi sunkuyar da kanta ƙasi tayi tana shirin zubda ƙwallah,

Ƙawar Aunty Yolash Hamdiyya ta ce "haba ke kuma Yolash ba'a haka bai kamata ba sam, mata ta taso daga yanda take tazo wurinki ki tsaya kina gaya mata magana ko wurin zama baki bata ba balle kayan drinks..."

Aunty Yolash ta ce "ai nasan uzurinta ne ya kawo ta Bauchin..."
Hamdiyya ta ce "to ko uzurinta ne ya kawo ta ai ta mutuntaki ne yasa ta zo har yanda kike, inda wata ce ai tafiyar ta zata yi baza ma ta kalli hanyar gidan ki ba...".

Aunty Yolash kallon Hajiya Kilishi tayi sannan ta ce "ko dai kin yi bazawari ne anan Bauchi shiyasa kika kawo masa ziyara..."

Hajiya Kilishi dai kai a sunkuye ta kasa É—agowa balle ta haÉ—a ido da Aunty Yolash,
Aunty Yolash ce ta kalli Hamdiyya ta ce "wannan É—in dai Hajiya Kilishi ce matar Yayana General wanda ya rabu da ita...."

Hamdiyya sake baki tayi tana kallon Kilishi cike da mamaki ta ce "wannan É—in Hajiya Kilishi ce? Innalillahi naga duk ta rarrame kamar mai HIV ga fuska ta kokkoÉ—e tayi fiyau, ai ni bangane ta ba wallahi, duk meya faru da ita haka?..."

Aunty Yolash ta ce "Nima ina zan sani, kamata yayi yanzu muga kin ƙara murmurewa kinyi ƙiba sakamakon ba'a takure kike ba, zaki iya fita duk san da kika ga dama ki dawo gida duk lokacin da kike so babu mai takura miki, kinsan General yana takura miki baya barinki kije duk yanda kike so yanzu kuwa kura ta mutu muyi wasa, yanzu kuma naga akasin haka sosai da duk kan alamu kina cikin tashin hankali Hajiya Kilishi,
Kinga duk taƙamarki da izzarki da girman kanki yau ke ce a gaba na kina zubda ƙwallah?..."

Hamdiyya ta ce "Kinga Yolash ki ce ta zauna mana tin shugowar ta take tsaye babu daÉ—i, ko ba komai ai an haÉ—u tunda akwai yara a tsakani..."

Aunty Yolash ta ce "Ok ki shigo ki zauna..."

Hajiya Kilishi ce ta ƙarasa shigo wa ciki ta zauna a ƙasin carpet,
Aunty Yolash ta ce "a'ah tashi ki zauna akan kujera, ni bana wulakanta mutum duk wanda yazo gidana zan karɓe shi hannu bibbiyu yawwa..."

Hajiya Kilishi ta tashi ta zauna akan kujerar falo ba tare da ta ce komai ba.

Hamdiyya ce ta tashi tana faÉ—in "Ni zan koma gidana na bar yara su kaÉ—ai..."

Suka yi sallama Hamdiyya ta tafi tana mamakin ganin Hajiya Kilishi a cikin wannan halin...

Aunty Yolash ce ta ƙwalla ƙiran ƴan aikin gidanta tare da sanar musu cewa su kawo wa baƙuwarta abinci da kayan drinks,
Bayan Æ´an mintuna sai ga su da kayan abinci da su fruit da drinks sun ajiye akan table É—in tsakiyar falo tare da jan yo shi gaban Hajiya Kilishi, sai da Hajiya Kilishi ta gama cin abinci da sauran kayayyaki tukun ta fuskanci Aunty Yolash,
Itama Aunty Yolash kallonta take tana son jin mai ke tafe da ita...

Bayan Hajiya Kilishi ta ci tayi nak sai kawai ta fashe da kuka,
Aunty Yolash ta ce "ha'a lafiya kuwa?..."

Durƙusawa Hajiya Kilishi tayi da gwiwowinta tare da haɗe hannayenta biyu tana roƙon Aunty Yolash da cewa "Dan girman Allah Auntyn yara inaso ki mun wani taimako ba dan hali na ba, kamar yanda Allah ya rufa miki asiri dan ALLAH nima ki taimake ni ki rufa mun nawa asirin..."

Aunty Yolash ta ce "kema Allah ya rufa miki asiri sai dai kece kika tona wa kanki asirin, abun ya ban mamaki shin wani irin taimako ne kike so nayi miki har da durƙusawarki wanda tunda kike baki taɓa yin gigin yin haka ba..."

Hajiya Kilishi tana kuka ta ce "dan Allah kiyi haƙuri akan abubuwan da na aikata miki, nasan ban kyauta miki ba amma ki gafarce ni..."

Aunty Yolash murmushi tayi tare da faɗin "nasan ba wai neman gafarata kika zo yi ba, akwai abinda ke tafe dake, Ni indai nine za'a zauna lafiya ƙalau ba tare da ɓacin rai ba don haka komai ya wuce a wuri na, shin wani taimako kike so nayi miki indai baifi ƙarfi na ba zan taimaka miki,
Sannan ki tashi ki zauna akan kujerar bana son durƙusawarkin Nan..."

Hajiya Kilishi tana sharar hawaye ta tashi ta zauna tare da faɗin "bazai ma fi ƙarfin ki ba, nasan kina ɗaya daga cikin waɗanda zasu faɗi magana General ya ɗauka ko shawari haka, kina ransa sosai, yana matuƙar ji dake...."

Aunty Yolash ta katse ta da cewa "duk nasan wannan wa'azin just go ahead..."

Hajiya Kilishi ta cigaba da cewa "Auntyn yara inason komawa gidan mijina, wallahi ina son kasancewa tareda mijina da kuma ƴaƴana, ina shan wahala sosai a gidan da nake, ga bani da kuɗi yanzu abincin da za'a bani ma ƙyashinsa ake wani sa'in ba'a bani, gidan mijina ya fi mun kwanciyar hankali, wallahi nayi nadamar abubuwan da na aikata a baya, nayi kuskure wanda yanzu nake son gyarawa..."
Chapter 23 · 0% Book details