← Book details My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 39

Sashe 36

My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayar Ummy ce ta fara ringing tana duba wa taga Uncle Deen ne, É—agawa tayi tare da yin sallama,
Daga ɓangaren Razhdeen cewa yayi "wai meyasa Abbah baya picking call ɗina ne sannan ina ƙira Roshan shima baya ɗaga wa why?..."

Ummy tana kuka ta ce "Uncle Deen su Abbah suna hospital ciwon heart É—in Yaya Roshan ne ya tashi, sun tafi ko motsi baya iya yi sai aman jini yake..."

Razhdeen cikin tashin hankali ya ce "whattt?..."
daga nan ya katse wayar...

Hajiya Kilishi ce ta ce "anya bamu bisu asibiti ba? muje mu gano ya ake ciki..."

Ammy ta ce "gaskiya kam..."

Har sun miƙe zasu fita sai ga ƙiran wayan Abbah ta wayar Ummy nan ma ɗagawa tayi tana faɗin "Abbah gamu nan zuwa..."

Abbah ya ce "No ku zauna domin ko kun zo ba samun mu zaku yi ba, yanzu haka muna airport zamu fita ƙasar waje domin sai anyi masa aiki..."

yana kaiwa nan shima ya katsar da ƙiran...

Ummy ta ce "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un ciwon Yaya Roshan yayi tsanani dole sai anyi masa operation a heart ɗinsa, yanzu haka suna airport zasu fita ƙasar waje...."

Baiwar ALLAH tana jin haka data fashe da wani irin marayan kuka ai kawai ta nufi bakin ƙofa da gudu ta fice..

Duk bayanta suka bi suna faÉ—in "ki dawo Daughter ina zaki je kuma..."

Gudu na gaske take ta buÉ—e gate É—in farko ta fice, tana zuwa gate na biyu nan ma ta buÉ—e ta wuce security da gudu, bayan ta suka bi suma suna faÉ—in "lafiya kuwa me yake faruwa ne..."

ai kuwa nan da nan ta iso gate na uku wato babban gate nan ne bazata iya buÉ—e wa da kanta ba haka take bubbugawa tana ihu, har sauran security suka tarar da ita, sai ga su Hajiya Kilishi da Ammy da sauran suma sun iso ta,
Sojojin dake waje jin yanda ake ta bubbuga gate yasa su buÉ—e wa suna faÉ—in "who's here?..."

Ganin mutanen gidan ne yasa su cewa "meyasa ku ka fito?..."
suka yi magana fuska a haÉ—e ba alamun annuri ga jajayen idanuwa...

Ai kuwa Baiwar Allah bata tsaya sauraronsu ba ta zille ta tsakiyar su ta wuce, gudu take bana wasa ba, suma haka sojojin suka bita suna faɗin ta dakata amma ko sauraronsu bata yi ba, ai kuwa tana cikin wannan halin sai ta ƙara tarar da asalin babban gate ɗin gidan gaba ɗaya wanda daga shi shikenam sai outside, anan kuma sojojin dake wurin sun fi goma banda waɗanda suke ta waje,
Baiwar Allah ganin bata da wata mafita kawai ta durƙusa gwiwowinta a wurin ta fara zabga uwar ihu, duk sojojin suka kewaye ta suna tambayar ta meke faruwa amma ta kasa yin magana sai cewa take
"Ku barni naje na gano mijina dan Allah, inason ganawa da shi kafin su shiga jirgi, mijina nake son gani..."

Wani soja ne ya ce mata "kiyi haƙuri ki koma ciki domin jirginsu har ya tashi sun tafi..."

Su Hajiya Kilishi da Ammy kam tin a gate na biyu suka dakata domin ba ƙaramin gajiya sukayi ba, daƙer su Ummy suka ƙaraso wurin gate na huɗun yanda Baiwar Allah ta dakata suma ɗin ba ƙaramin gajiya suka sha ba..

Daƙer aka rarrashi Baiwar Allah ta haƙura suna shiga mota aka komar dasu can cikin gidan amma ta kasa dakatar da kukan....

A haka suka wuni har zuwa dare kowa a cikin damuwa yake,
Misalin ƙarfe 9 na dare duk suna zazzaune a babban falo sai suka ji an turo ƙofar falo da ƙarfi, a matuƙar tsorace duk suka miƙe tsaye idonsu akan bakin ƙofa ganin mutum sangamgam gashi a kwance saman bayansa sai haki yake domin a ruɗe ya iso, kana ganinsa kasan ba'a cikin hayyacinsa yake ba,
Ummy ce ta ƙaraso yanda yake tana faɗin "Uncle Deen..." ta ƙarasa tana kuka...

Duk suma suka nufi yanda yake a tsaye suna ambatar sunansa, banda Baiwar Allah dake zaune tayi tagumi ko kallon yanda suke bata yi ba...

Razhdeen ya ce "wani hospital suke?..."

Ammy ta ce "sun fita ƙasar waje sai anyi masa aik..."

Cikin tashin hankali Razhdeen ya ce "which country?..."

Ammy ta kalli Ummy ta ce "wani ƙasar waje Abban ku ya ce miki sun je?.."

Ummy ta ce "wallahi bai gaya mun ba..."

Hajiya Kilishi ta ce "Razhdeen ka jira zuwa nan da kwana biyu zasu dawo...."
bata ƙarasa maganar ba ya katse ta da cewa "i can't wait..."

Haka yake zarya a cikin falon yana trying number Abbah amma baya shiga, duk wasu numbobin da yake tsammanin zai samu labarin su Abbah amma basa tafiya, cikin ɓacin rai da takaici haka yayi wurgi da wayarsa sai tin plasman, nan danan wayar ta fashe, hatta plasman ɗin ma ya samu rauni domin da iya ƙarfinsa ya wurga, durƙusawa yayi da gwiwowinsa yana cakurkuɗa sumar kansa lokaci guda ya zabga wani irin gigitaccen ihu, ai kuwa nan da nan kamar wani mahaukaci ya fara wargaza falon yaje ya janyo plasman yayi wurgi da shi, yaje ya buga glass dinning har sai da shima ya dagargaza shi,

Baiwar Allah ganin zai iya ji mata rauni yasa ta tashi ba shiri taje ta ɓuya a bayan Ammy...

Hajiya Kilishi ce tayi ƙarfin halin zuwa har yanda Razhdeen yake a durƙushe itama taje ta tsuguna tana ambatar sunansa a hankali "Razhdeen! please ka kwantar da hankalinka Roshan zai samu sauƙi, ai cuta ba mutuwa ba ne..."

Razhdeen fuskar nan tayi jawur haÉ—i da idanuwansa haka ya É—ago su a shanye yana faÉ—in "ciwon nan yaushe zai warke na har abada? meyasa ciwon bazai dawo kaina ba?...."

A zabure cikin tsawa ya ce "wai shin meye silar faruwar haka? waye yayi sanadiyar tashin ciwon sa? nasan haka kawai ciwon sa baya tashi sai da dalili, who....?..."

Ita kan ta Hajiya Kilishi sai da ta tsorita da tsawar sa nan...

Baiwar Allah haka take cakumar Ammy ta baya tana ɓuya zuciyar ta na harbawa da ƙarfin gaske...

Baiwar ALLAH bata ankara ba taji an jawo ta tare da yin wurgi da ita a tsakiyar falon, a ruɗe ta ɗago tana kallon Razhdeen wanda yayo kanta yana faɗin "me kika aikata masa? nasan bakya ƙaunarsa fatan ki shine ki rabu da shi, kina son kashe mun ɗan uwa ko?..."

ya cabko sumar kanta a fusace tare da É—ago da kanta yana kallon fuskar ta ya ce "kafin ki kashe mun twins wallahi sai kin rigashi tafiya lahira..."

Gwara kanta yayi da jikin kujera ya nufi kitchen cikin ƙanƙanin lokaci ya fito hannunsa riƙe da wuƙa...

Gaba ɗayan su zaro ido suka yi suna kallon Razhdeen, ganin ya fito yana riƙe da wuƙa, yana zuwa ya ɗaga hannunsa zai caka mata wuƙar ta zabga wani irin gigitaccen ihu, dai dai lokacin da Abbah ya shigo a ruɗe ya ambaci sunansa " *RAZHDEEN*" ..

Dasauri ya ɗago tare da kallon yanda yaji an ƙira sunansa domin kunnensa sun jiyo masa sautin muryar Abbah ne..

Ammy kuwa tinda Razhdeen ya ɗaga wuƙa ta ƙanƙame idonta zuciyarta na bugun uku-uku...

Hajiya Kilishi kam ja da baya tayi sauran kaɗan ta faɗi ta baya badan Pinky tayi saurin riƙe ta ba...

Ummy itama ihu ta zabga tare da faÉ—in "Uncle Deen..."

Abbah a ruÉ—e ya shigo falon tare da nufan yanda Razhdeen yake yana faÉ—in "da hankalin ka kuwa Razhdeen? shin ka haukace ne?..."

Baiwar Allah tana kuka ta tashi da gudu ta nufi yanda sauran suke a tsaye Ammy tayi saurin rungumo ta tana rarrashinta...

Abbah ya ce "kawo wuƙar nan, wa ya gaya maka itace silar kwanciyar sa jinya?..."
Abbah ya karɓe wuƙar yana bubbugan kafaɗar sa cikin rarrashi...

Razhdeen kuka ne ya kuɓuto masa Abbah yayi saurin rungumar sa tare da faɗin "ka kwantar da hankalinka Roshan ya farfaɗo cikin yardar Allah, domin har anyi masa aiki anyi treat ɗinsa sosai, kasan asibitin ƙasar Ethiopia muka je, su kuwa aikinsu ba wasa..."

Razhdeen ya É—ago yana kallon Abbah sannan ya ce "yana ina Abbah? inason ganin twins É—ina..."

Abbah ya ce "na baro shi acan cikin kulawa, gobe zan koma Insha Allahu..."

Razhdeen ya ce "inason ganin shi..."

Abbah ya ce "okay don't worry..."
ya ciro wayar sa tare da dialing call wani ma'aikaci daga can hospital....
cikin ƙanƙanin lokaci aka ɗauka daman video call ne, Abbah ya ce "ina buƙatar ganin Roshan..."
daman suna kusa da shi domin sune masu bashi tsaro,
Roshan ne ya bayyana akan fuskar wayar yana kwance kan gado ya na sanye da oxygen,
Abbah ya nuna wa Razhdeen yana faɗin "ka gànshi nan yana cikin kulawa..."

Razhdeen ya karɓi wayar idonsa akan Roshan wanda eyes ɗinsa suke lumshe kamar mai yin bacci, ga yanda fuskar tayi fiyau ya ƙara yin kyau sosai...

A hankali Razhdeen ya furta "My twins..."

A ɓangaren Roshan kuwa jin an ambaci sunansa kamar muryar Razhdeen yasa shi buɗe eyes ɗinsa a hankali, yana kallon screen ɗin wayar dake yana sanye da oxygen ba halin yin magana sai ido, ga babu riga a jikinsa sai tin zuciyarsa alamun anyi aiki a wurin...

Razhdeen murmushi yayi ya ce "Quick recovery my lovely twins..."

Shima Roshan É—aga masa kai yayi alamar amsawa,

Abba ne ya karɓi wayar yana sanar da sauran ƴan gidan akan suma su zo su duba shi, kowa yazo ya duba shi banda Baiwar Allah dake tsaye gefe guda har yanzu ta kasa dawo wa hayyacinta, sai da Abbah yaje har yanda take ya nuna mata Roshan yana faɗin "Daughter kinga mijin nakin ..."

Baiwar Allah idonta akan Roshan ga yanda hawaye yake faman zirya akan fuskarta,
Razhdeen kuwa wani irin kallo yake watsa mata na ƙiyayya da tsana....

Washe gari da safe Abba ne zai koma Ethiopia wurin Roshan har Razhdeen ya shirya zasu tafi tare Abbah ya bashi haƙuri akan ya zauna da iyalansa domin suma bazasu juma ba...

Razhdeen ya ce "Dad inason ganin twins..."
Abbah ya ce "ka kwantar da hankalinka yanzu jikin yayi sauƙi Insha Allahu yana samun ɗan sauƙi zamu dawo..."

Daƙer Abbah ya rarrashi Razhdeen ya zauna shi kuma Abbah ya nufi airport....
Chapter 36 · 0% Book details