Sashe 16
My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ummy zaro ido waje tayi ganin Mohandas ɗan maƙiyin Abbah kuma shima maƙiyin ne tinda yana neman ɗiyarsa,
Ammy kuma dake bata san Mohandas ba yasa ta fara sakin murmushi tana faɗin "babban baƙo mukayi ne? sannu da zuwa Roshan ga wuri ku zazzauna..."
Hakan kuwa akayi duk zama suka yi, Ammy kuma tashi tayi ta shige kitchen zata haɗo musu abin taɓawa, Uwar masu gida kuma itama tashi tayi da haura saman upstairs da gudu zata je ta sanar wa Minal cewa ga Mohandas a gidan su, sai ya rage iya Baiwar ALLAH a falon, idonta akan Mohandas sau ɗaya ta taɓa ganinsa ran da suka je gidan Razhdeen nan ma bata ƙare shi da kallo ba sai yau, haka kawai take jin tsinkar jikinta yana tashi ga wani irin bugun zuciya, ta rasa meye dalilin faruwar wannan al'amarin, shima Mohandas ɗin kallon ta yake ya dai san itace Amaryar Roshan amma bai gaba saninta ba sai yau shima yana jin wani abu sosai a kanta,
Idon Baiwar ALLAH ne suka sauƙa akan wani ɗan sarƙar dake ɗaure a hannunsa shigen irin nata, sai dai ita a wuyanta yake ɗaure kuma akwai mayafi a kan ta balle ta sake ganin kalar natan, ƙirjinta ne yake wani irin bugawa sosai,
A lokacin ne Abbah ya fito daga part É—insa wayar sa a É—ore kan kunne sai muryarsa kake ji yana ta waya,
da haka ya gama sauƙowa daga upstairs idonsa ne suka sauƙa akan Mohandas kamar wanda aka ɗauke masa wuta haka ya tsaya cakk.
Itama Minal fitowa tayi da gudu ita da Ummy suka sauƙo falo, Ammy ce ta jejjera musu kayan abinci akan table ɗin falo saitin gaban Mohandas,
Abbah ne ya sanar a wanda yake waya dashi cewa "Please I'll call you back, cut the phone..."
Still idonsa akan Mohandas, shima Abbah zama yayi yana fuskantar su ba tare da ya ce komai ba..
Jikin Mohandas ne ya fara rawar sanyi ganin yanda Abbah ya chanza cikin lokaci ƙanƙani,
A fusace Abbah ya ce "meya kawo ka gida na?..."
Mohandas kasa magana yayi sai Roshan ne ya yi ƙarfin halin cewa "Am Abbah daman akwai maganar da muke so muyi ne..."
Abbah ya ce "nasan akan maganar Amina ne ko? wai shin dole sai ɗiyata zai Aura ne? nace bazan taɓa haɗa jini da familyn su ba kuma babu mahalukin da ya isa yasa na haɗi, dan haka ya tashi ya bar mun gida tin kafin na fusata..."
Roshan ya ce "dan ALLAH Abbah ka saurare ni..."
Abbah ya kalli wurin da Mohandas yake a zaune ya ce "saboda kai na hana ƴata zuwa wurin aiki, na hanata fita ko ina, shin me kake yi a Nigeria da har yanzu bazaka koma ƙasar ku ba, na hanaka tarayya da ƴata ka ƙi, to ƴaƴana mazan ma zan hanaka tarayya dasu saboda haka daga yau zamanka a gidan Razhdeen ya ƙare, na datse Abotar ta kun, sannan Roshan ma kada ka sake shiga sabgarsa na gaya maka, in har ba haka ba zanje na samu mahaifinka na ja masa kunne ya dakatar tinda ni ban isa da kai ba, idan ba haka ba gavar da nake da mahaifinka zai ƙara ninkuwa ne kuma wallahi sai mun shiga kotu da ku..."
Abbah tashi yayi zai koma ciki Roshan ya ce "Abbah Please ka bamu lokacin ka..."
Abbah a fusace ya juyo yana faɗin "Roshan ka maida hankalinka na gaya maka, ka fitar mun da wannan ƙabilan a cikin gidan nan..."
Ammy da ta kasance bata san komai ba amma a yanzu ta fahimta domin taji labarin Minal da Mohandas,
Baiwar ALLAH itama tana wurin akayi komai gaba ɗaya hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, ga bata san dalilin da yasa take jin tausayin Mohandas haka kawai ba, Uwar masu gida har da kukan ta.
Abbah har zai motsa ya tafi yaji Minal ta buɗe baki tana kuka ta ce "Abbah wallahi inason Mohandas kuma bazan taɓa rabuwa da shi ba, sai dai kayi haƙuri amma aikin gama ya rigada ya afku tinda akwai Aure a tsakanin mu..."
Ba Abbah ba hatta waÉ—anda suke wurin babu wanda bai girgiza da jin abinda Minal ta furta ba banda Roshan,
A firgice Abbah ya ce "whattttt!!!???..."
Murmushin takaici yayi ya kalli Roshan ya ce "kaine silar faruwar hakan ko? Minal bata fita ko ina sai da kai saboda na yadda dakai Roshan ashe kaima zaka iya cin Amana ta? Amma ka cuce ni Roshan saboda in ba dan kai ba babu yanda za'ayi Minal tabar gidan nan saboda tsaron da na sa mata, ban sa a raina cewa hakan zata faru ba saboda na yadda da kai, shiyasa duk abinda kace mun nake Amince maka..."
Roshan gaba É—aya jikinsa ne ya yi sanyi, bai san lokacin da ya fara zubda hawaye ba, sai yanzu ya yi nadamar aikata hakan..."
Abbah kallon Minal yayi tare da faÉ—in "kin kyauta, amma ki sani cewa bazai bar gidan nan ba tare da ya baki takardar sakin ki ba..."
Tana kuka ta ce "Abbah ya musulunta fa..."
Wani irin gigitaccen tsawa ya daka mata tare da faɗin "ko Alqur'ani ne a jere a kansa bazaki shiga familyn su ba, babu jini na da zai zauna da familyn su nayi Alƙawarin haka..."
Ya maida kallonsa kan Mohandas sannan ya ce "inaso a yanzun nan ka furta kalmar saki wa Æ´ata a yanzu..."
Ammy ce ta buÉ—e baki ta ce "Chief indai ya musulunta ka barsu kawai dan ALLAH, kar a toye musu hakki..."
Abbah ya ce "bana chanza magana idan nayi..."
Sai a wannan lokacin Mohandas ya buɗe baki shima wurin cewa "kayi haƙuri Abbah bazan iya sakin ta ba..."
A fusace Abbah ya ce "haka kace ko? to ku jira Ni ina zuwa, yau zan nuna muku zamani na ya ninka naku sau ba adadi..."
ABBAH yana kaiwa nan da sauri ya haura upstairs domin akwai abinda yake son ɗauko wa (kodai gum ɗinsa zai ɗauko 🤣🤣)
Ammy ce ta bi bayansa itama tana so naje tayi roƙo,
Bayan su Abbah sun haura Roshan da gudu yabi bayansu, yana haurawa can part ɗin da suke, jawo ƙofar room ɗinsu yayi tare da murɗa key yabar key ɗin a jikin ƙofar sannan ya dawo yana ce musu "Marshall ka kama matarka ku tafi duk yanda ya kamata, kada ka bari kowa yasan yanda kuke domin Abbah zai iya sawa a nemo ku a duk yanda kuke, daga nan ka wuce airport ku bar ƙasar..."
Girgiza kai Mohandas yayi alamun bazai iya ba,
Minal ta ce "Dan ALLAH Mohandas kazo mu tafi kafin Sojojin gidan su ankara kaga yanzu basu san halin da ake ciki ba..."
Jin haka yasa Mohandas riƙo hannun Minal suka fice, Roshan ne yabi bayansu saboda yana so ya fita dasu kar Sojoji su fahimci wani abu,
Hakan kuwa akayi motar Mohandas suka shiga, Mohandas shine mai driving sai Roshan a gefen sa, Minal kuma tana ta back seat da haka suka fice a gidan gaba É—aya kai tsaye airport suka wuce...
Abbah da Ammy suna cikin bedroom ɗinsu sai ji sukayi an ƙarƙame su, ga bindiga a hannun Abbah yayi ƙolon duniya akan azo a buɗe mishi ƙofa amma babu wanda ya nufi wurin, ga wayar sa ya barta a falo balle ya ƙira sojojin gidan gaba ɗaya Abbah ya rasa mai yake masa ciwo, ita kuwa Ammy alwalarta tayo tazo ta tsaida sallah domin a halin yanzu Abbah ba sauraronta zai yi ba,
Baiwar ALLAH tana so taje ta buɗe musu ƙofar jin yanda Abbah yake ta ƙiraye-ƙirayen sunayen su especially sunan Uwar masu gida yafi ƙiran ta akan taje ta buɗe amma Ummy fur taƙi zuwa sannan tana riƙe da hannun Baiwar ALLAH taƙi sakin ta,
Ummy tana kuka ta ce "haba Aunty Dota har yaushe za'a kawo karshen wannan bala'in ƙiyayyar Abbah da su familyn Yaya Mohandas? Aunty Minal da Yaya Mohandas suna matuƙar ƙaunar junan su hakan yasa bazata iya Auran kowa ba kuma kinsan a halin da take ciki, ita fa ba ƙaramar yarinya ba ce, tanada matsalar matsinancin sha'awa amma Abbah ya kasa ganewa, Yaya Mohandas saboda soyayyar Aunty Minal ya musulunta fa, ai abun alfahari ne wallahi, don haka baza'a buɗe ƙofar nan ba sai har Yaya Roshan ya dawo tukun..."
Baiwar ALLAH gaba ɗaya ta rasa mai zata ce a wannan al'amarin gashi bata san meya haɗa ƙiyayyar ba, amma itama tana mungun tausaya musu sosai...
Ganin bazata iya juran ƙiraye-ƙirayen sunayen da Abbah yake yi ba yasa ta fice a falon gaba ɗaya, kai tsaye can part ɗinta ta nufa zuciyarta a jagulgule...
Itama Ummy haurawa upstairs tayi can room É—inta,
Roshan bai tashi dawowa ba sai da ya tabbatar jirginsu ya tashi tukun, wuce wa part É—insa yayi cike da fargaba domin bai san wani irin hukunci Abbah zai É—aukar masa ba...
Dab da mangariba sai ga motar da ake kai Ƴar tinny school kuma a dawo da ita, a falo ta tsaya tare da jefar da jakar ta anan taci karo da wayar Abbah akan kujera, ɗauka tayi tana faɗin "Yaaa wayan Abbah..."
Da gudu ta haura upstairs ta nufi room ɗin su Abbah, buga ƙofar ta soma yi tana ƙiran sunan Abbah tare da faɗin "Abbah ganan wayay ka..."
Daga ciki Abbah ya ce "yawwa Auta duba mun akwai key a jikin ƙofar?.."