← Book details My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 39

Sashe 5

My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajia Maamie ce tace "Ni ce nazo duba Ramlat ne ko tazo nan..."

Roshan yace "daman kinsan da zuwanta?..."

Hajia Maamie tace "ehh! A'ah!! Eyy!!! A'ahh!!!!! Ehhh tohhh...."

Razhdeen ne ya juyo suka haÉ—a ido da Roshan,
fuska a haÉ—e Razhdeen yace "ki shugo ki É—auke kayanki..."

Saiga Maamie ta shugo baki a washe ta É—auka cewa sun gama fahimtar juna ne data jita tayi shuru a É—akin,
ta shugo tana faɗin "tana inane? ha'a kodai itace a lulluɓe saman gado, ahhhh Masha Allah tinda bacci take bari na barku karna takura muku Koh....."

Har zata fice Roshan yace "É—aga kanki sama..."

Maamie tana ɗagawa ta wani sau ƙara tana dafe da ƙirjinta, ƙafafunta har wani rawa suke, lokaci guda gumi har ya wanke mata fuska...."

Sai ga mai martaba shima ya shugo jin ihun MAAMIE yana faÉ—in "lafiya kuwa meke faruwa?..."

Saiga INDO itama domin ihun ya karaÉ—e ko ina na gidan,
Ai kuwa duk suka É—age kayiwansu sama suna kallon ikon ALLAH,.
Mai martaba yace "meye wannan?..."

Maamie tana kuka tace "wani irin tambaya ne wannan kana ganin sun kashe mun ƙanwaaaa...." nan ta fashe da matsanancin kuka harda majina,

Mai martaba yace "meya kawo ta É—akin nan TOH?..."

Maamie tace "kafin ka gama tambayarka Ni a Ciro mun gawar ta tinda sun kasheta mungwaye kawai azzalumai macuta, Allah ya isana tsakanina daku wallahi...."

ta nufi wurin Roshan tana kai masa duka,
Shi kuwa sai faman kaucewa yake, ita kuwa sai duka ta ko ina...

Mai martaba ne ya rirriƙeta yana faɗin "meye haka kike dukansa shi ba ƙaramin yaro ba, ko ce miki akayi shi yayi mata haka? TOH gashi can kije ki same shi ki dake shi..."

ya nuna mata yanda Razhdeen yake,
kallonsa tayi taga yanda yake wurga mata wani irin kallo kamar idanun zasu faɗo, tin daga lokacin da ta fara kaiwa Roshan duka yaji kamar ya shaƙota kawai yana ganin mutuncin Mai martaba ne, shi dai yasan in har ya miƙe daga zaune to saiya ɗage mata numfashi ne,
kafin a ankara aka nemi Maamie aka rasa harta fice da gudu tana kuka...

Girgiza kai mai martaba yayi yana faɗin "kaga Roshan kayi haƙuri dan ALLAH, yanzu ya za'ayi mu Ciro ta..."

Roshan ya kalli Razhdeen sannan yace "my man ka temaka ka Ciro ta..."

Miƙewa Razhdeen yayi ya nufi yanda Akwatinsa yake tareda faɗin "Impossible..."
ya É—auko Akwati yana ja zai fice mai martaba yace "ina kuma zaka je?..."

Tsayawa yayi yace "Abbah yana son ganina right now sannan idan na ƙara kwana ɗaya a ƙasar nan wancan matar saina hallakata..."

Mai martaba yace "a'a! ALLAH ya huci zuciyarka Major General Razhdeen Allah ya kiyaye hanya ya tsare rayuwarka..."

Razhdeen amsa masa yayi da Amiin sannan ya fice...
Shima Roshan bin bayansa yayi zai rakashi can airport da motar gidan...

Mai martaba tsayawa yayi ya rasa yanda zai yi duk sun tafi sun barshi,
Saida yasa aka ƙira ma'aikatan mazan gidan kafin suka zo suka Cirota daƙer....

Roshan bai tashi dawowa ba saida yaga jirgin Razhdeen ya tashi kafin shima ya dawo masarautar,
Razhdeen an koma Nigeria.....

*POSTING DAYS*
*SUNDAY*
*TUESDAY*
*THURSDAY*
*FRIDAY*

*A SATI SAU HUÆŠU ZA'ANA POSTING*
*GA RANAKUN YIN POSTING...*

*ALLAH YA BANI IKON BIN TSARIN YANDA YA KAMATA*

*SANNAN A DAGE DA COMMENTS DOMIN SHI ZAISA A RINƘA YAWAN MUKU POSTING....*

asmeetah writer ✍️

*MY ENEMY _*

🫦 مقىينا 🫦

Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳

Asmeetah (giaÉ—e writer)

STEP TWO
7 to 8

Bayan Razhdeen ya sauƙa a airport already akwai sojojin da suka zo ɗaukarsa,
Saida yasa suka miƙi hanyar mabarata yanda zai ga Ƴar Amana,
cikin rashin Sa'a ya zuba ido yaga babu alamar ta sai tarin tsofin da suke zazzaune a wurin, Razhdeen yana zaune a back seat eyes É—insa kawai yake ta wurgawa, cije lips É—insa yayi sannan yayi magana ciki-ciki yace "let's go..."
Jan motar driver yayi suka miƙi hanya, haka sauran motar ma suka bi bayan motar su Razhdeen,
mabaratan ganin motocin sojoji ne yasa babu wacce tayi motsin tashi balle suzo yin Bara, sai gani sukayi wani soja ya dirƙo daga kan mota ya nufi yanda suke fuska ba annuri ga bindiga a rataye a kafaɗa,
ko wacce jikinta ne ya fara kakkarwa ganin sojan yayo kansu, tsayawa yayi ya zuge jakar hannunsa sannan ya Ciro wasu maƙudan kuɗaɗe duk ya rarraba musu, lokaci guda suka fara washe hakwara sai faman zabga masa godiya suke tare da Addu'o'i, ko amsa musu baiyi ba ya juya yaje ya shiga cikin motar daya rage iya shi kaɗai ne a wurin,
yana shiga kamar walƙiya suka bar wurin, daman Razhdeen ne yasa a raba musu ta hanyar tura musu saƙo ta waya....

Isar su keda wuya duk falon an hallaru ana jiran shugowar Uncle Deen, Ummy gaba ɗaya ta kasa zama tsabar farin ciki da zumuɗin ganin Uncle Deen, tayi matuƙar farin ciki sosai da Abbah ya dawo dashi cikin Ahali da temakon Aunty Yolash wacce take zaune itama a two seater sai faman pressing phone ɗinta take,
Pinky da Rukky suma suna zaune a five seater Rukky ce take kwance kanta a saman cinyar Pinky tana É—an lumshe ido kamar mai jin bacci, a yayinda Pinky take ta danna wayar hannunta alamar charting take, duk abubuwan da ke faruwa a gidan tana sanarwa mommy wato Hajia Kilishi, yanzu ma charting take da ita...

Baiwar ALLAH kuma tana can cikin É—akinta a kwance saman katafaren gadonta kamar mai yin Bacci, sai dai ba baccin take ba, amma idonta a lumshe suke,
Ga wata ƙatuwar waya ƙiran iPhone 15S, ƙira ake tayi ba ƙaƙƙautawa daga wannan ƙiran ya yanke sai wani ƙiran ya sake shugowa anyi ƙiran yafi sau 15 a lokaci guda kuma duk mutum ɗaya ne mai wannan ƙiran,
Baiwar ALLAH tana ji amma taƙi ɗaukar ƙiran domin ta rigada tasan cewar Roshan ne mai wannan damun,
wani ƙiran ne ya sake shugowa Once takai ƙwayar eyes ɗinta kan screen ɗin wayar ganin ROSH a rubuce kan screen yasa taja dogon tsuka tareda tashi zaune tana hararar wayar cikin ɓacin rai ta soma magana tana faɗin
"Mttssww! aikin banza wai dan saboda kai ka sayi wayar shine zaka takura Ni? I hate dis nonsense wallahi, banason mutum mai nacin tsiya, takurawarka ne yasa nake ƙara tsanarka wallahi Roshan....."
a fizge tasa hannu ta ɗauki wayar ganin bazai daina ƙiran ba,
ɗaukar ƙiran tayi ta kara a kunne tayi shuru tana hararar gefe, magana yake ta cikin wayar yana ambaton sunanta "Ammata! Hello Ammata!! Assalamu alaikum bakya jina ne? Ammata nah Dan ALLAH kiyi magana mana...."

ɗan tsuka tayi acan ƙasin harshenta tace "wai dan ALLAH meyasa kake son takura mun ne? ko dan saboda kai ka ban wayar shine zaka rinƙa takura mun, Ni gaskiya bana son irin haka..."
ta ƙarisa maganar tareda tura ɗan lips ɗinta kamar wacce take gabansa,

daga ɓangarensa sauƙe nannauyar ajiyar zuciya yayi murya ciki-ciki yace "oh my God, Ammata banida burin daya wuce na rinƙa ganin farin cikin ki akoda yaushe, inasonki wallahi l, ina ƙaunarki har cikin zuciyata, tinda Allah yasa nabar Nigeria ban ji muryarki ba sai yau, ina kan ƙiranki amma bakya ɗauka mun ƙira why?..."
buÉ—ar baki tayi zatayi magana saiga Æ´aR tinny ta kutso kai da gudu tare da faÉ—in "Aunty Dota Ankuy Deen ya dawo..."
tana iddasa maganar ta juya ta fice,
Ita kuwa Baiwar ALLAH ido ta zazzaro waje cike da mamaki take bin bakin ƙofar da kallo, lokaci guda wani irin farin ciki ne ya wanzu mata,
Roshan yanata magana amma shuru ko jinsa bata yi, bata san lokacin da tayi wurgi da wayar ba ta miƙe tare da sauƙar da ƙafarta ƙasin carpet da gudu tayi hanyar bakin ƙofa itama, zata je taga abinda idanuwanta suka daɗe suna muradin gani,
Da gudun gaske ta faɗa Falo, lokaci guda ta danna burki ganin kowa ya hallaru, duk juyowa sukayi suna kallonta ganin kamar wacce aka hankaɗota, itama tsayawa tayi tana binsu da kallo, idanunta ne suka sauƙa akan kayan lefen da aka bazasu a tsakiyar Falo, wasu irin tsararrun akwatina ne guda sha biyu pink colours, ga kayan cikin su kansu basu san adadin kayan lefen ba tsabar yawansu, ga takalma kala-kala kamar wanda za'a buɗe shagon kayayyaki, kayan bacci suma sunfi hamsin, kayan makeup ba'a magana, gyalulluka da hijabai abun ba'a cewa komai, komai da komai akwai su,
ganin kayayyakin yasa gabanta yanke wa domin tasan duk nata ne, a hankali ta ɗago da shanyayyun idanuwanta ta sauƙe su akan Razhdeen wanda shima yana zaune a kujerar da yake facing ɗinta, idonsa akan wayarsa yanata pressing, jikinsa ne ya bashi cewa ana kallonsa, kamar bazai ɗago ba shima a hankali ya ɗago da kansa tare da wurga ƙwayar eyes ɗinsa kan Baiwar ALLAH wacce take tsaye ta ƙura masa ido ko ƙibtawa babu,
shima kallonta ya shiga yi duk suka fara kallon juna, abinda ya fara tunawa shine wankan da yayi mata da kasancewar da sukayi a É—aki É—aya..."
Itama dogon tunani ta faÉ—a abinda take tunowa shine lokacin da tayi ciwon ciki a É—akinsa da kula da ita da yayi, har wankan da yayi mata,
Kowa da abinda yake tunawa acikin ransa...

Ƴar tinny ce tayo kan Razhdeen tare da faɗawa saman cinyarsa tana faɗin "Ankui Deen wai yauce Mommy nah jata dawo ne?..."
hankalinsa ne ya karkato kan Ƴar tinny murya ciki-ciki yace "Mamana kiyi haƙuri zata dawo coming soon kinji Koh..."
tace "Ni a dawo mun da ita, kullum idan nace Abbah ya dawo da ita sai yace zai dake Ni ...". kamar zata fashe da kuka ta ƙarasa maganar cikin lankwasa murya...
Chapter 5 · 0% Book details