← Book details My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 39

Sashe 34

My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummy ta ce "sannu da zuwa Abbah, amma dan ALLAH kar kaga laifin Mommy domin mu muka zaɓi mu zauna da ita ba wai ita ce ta riƙe mu ba, kar ka sa mana ita kuka tana cikin farin ciki..."

Abbah ya ce "to meyasa ku ka zaɓi ku zauna da mahaifiyar ku akan Ni mahaifinku wanda zanfi baku kulawa sama da ita..."

Ummy ta ce "Abbah kayi haƙuri mahaifiyar mu ita ce sama da kai a wurin mu, domin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama yana umartar mu da mu bi uwa, mu bi uwa! mu bi uwa!! mu bi uwa!!! har sai da ya maimaita sau uku kafin nan ya ce mu bi uba, don haka zamu fi samun farin ciki mai ɗorewa idan muna tare da mahaifiyar mu..."

Abbah ya ce "hakane uwar masu gida amma ki zauna a gaban mahaifinki shine mutuncinki da darajar ki wanda ko neman Auren ki akazo yi uwa bazata bayar ki ba dole sai da uba ko Æ´an uwan mahaifin ki, ke da Æ´an uwanki duk wani abun more rayuwa da kuÉ—i kuna samu daga wurina bana takura muku...."

Ummy ta ce "Abbah ka sani fa inda ace kuɗi suna dawwamar da mutum cikin farin ciki da Babbar Yayar mu bata gudu tabi mijinta ba saboda tasan duk da kuɗin da take da shi bazai taɓa sanya ta cikin farin ciki ba, haka zalika inda kuɗi sune kwanciyar hankalin mutum da baka kasance cikin damuwa da kaɗaici ba to haka mu ma kuɗi bazai taɓa sanya mu cikin farin cikin ba without our mother, because our mother she's our happiness...."

Abbah shuru yayi yana kallon Ummy ya ma rasa mezai ce mata, yana cikin nazari sai ga Pinky da Rukky sun shugo sunata shan hirar su na school da suka baro, idonsu ne ya sauƙa akan Abban su da gudu suka wuce shi suka je duk suka ɓuya a bayan Mommynsu suna faɗin "Please Mom please kar ki bari ya tafi da mu please..."

Hajiya Kilishi kanta na kallon ƙasi ta kasa cewa komai domin yanzu Ummy ta fi su baki gaba ɗayan su,
Su Pinky su kam sai dai masifa da munafurci da rashin mutunci ga kuma tsoro, amma ita Ummy akwai ta da iya zayyano da zance wanda ko mai shekara 40 bazata nuna mata iya magana ba, domin tinin zata saye zuciyar mutum da kalamanta ko masu daÉ—i ko akasin haka.....

Abbah ya ce "to yanzu mai ku ke so ayi?..."

Ummy ta kalli su Pinky ta ce "kune Auntys shin ya ku ke so ayi?..."

Daga Pinky har Rukky duk kasa yin magana suka yi daga sun haɗa ido da Abbah sai suyi saurin sunkuyar da kansu ƙasi kamar wasu marasa gaskiya,

Ummy ta ce "Abbah akwai yanda za'ayi amma mu shiga cikin É—akin mana Abbah kana ta tsaye tin É—azu..."

Abbah ba yanda ya iya haka ya shiga ciki, duk suma suka shige, Ummy ta ce "Abbah ka zauna a bakin katifar mana..."
Nan ma ya zauna yana binsu da kallo.

Ummy ta tsaya tare da kama kunkumi ta ce "kash ga ba'a kammala girki ba ai da an kawo wa Abbah..."

Abbah ya ce "no bana buƙatar komai..."

Ummy ta ce "Abbah to bari a kawo ruwan sha.."
Nan ma ya ce "a'ah..."

Ummy ta ce "tam shikenam Mommy kema zauna domin akwai maganganu masu mahimmanci da zamu tattauna akai..."

Kowa ya nutsu yana sauraron Ummy domin ita kanta Hajiya Kilishi bata san wani irin magana Ummy zata sanar ba..

Ummy tana zaune a ƙasin ledar ɗakin kusa da Mommyn su, suma twins suna gefen Mommy domin duk cikinsu kowa ba son yin nesa da ita yake ba, sai Ƴar tinny dake bayan Abbah a kwance kan katifa..

Ummy tana kallon Abbah ta ce "Abbah..."

Abbah ya amsa mata cikin sassanyar murya domin har yanzu jikinsa bai gama warkewa ba.

Ta ce "dole a cikin abu biyu ayi É—aya ko a rasa ko kuma a samu shine kawai..."

Abbah ya ce "muje zuwa Uwar masu gida..."

Ummy ta cigaba da cewa "idan kanaso mu kasance da kai cikin farin ciki da annashuwa to dole sai muna tare da mahaifiyar mu a kusa, in har zamu bika mu tafi to dole sai da mahaifiyar mu, ƙafar ta ƙafar mu,
Idan kuma hakan bazai yu ba to zaka iya barin mu anan in yaso idan kana son ganin mu zaka zo ka gan mu amma da sharaɗin bazaka ƙuntata wa mahaifiyar mu ba domin ba wurinta kazo ba, wurin mu kazo, idan kuma tafiyar tayi maka nisa ai kanada gidaje a cikin Abuja sai ka kai mu can mu zauna da mahaifiyar mu, amma baza mu taɓa yin nesa da ita ba sai dai mutuwa...."

Abbah kawai tsaya kallon Ummy yayi tana ta zayyano da zance, daga bisani ya ce "okay duk naji abinda kika ce an ɗauke ku har ita na maida ku gidana domin hankali na bazai taɓa kwanciya idan bana ganin ku a kusa dani, gani nake wani abu zai faru da ku especially idan kuna fita yawo koda yaushe dole wasu samari zasu dakatar da ku daga lokacin da ku ka fara tsayawa da wani namiji a titi shikenam rayuwar ku ta fara tafiya, especially Balkisu da Ruƙayyat sun fiye rawan kai dole sai idanuwa na suna kansu, idan suka yi nesa dani hankalina bazai taɓa kwanciya ba, dan haka na zaɓi ku koma gida yanda zaku samu tsaro na musamman..."

Pinky da Rukky farin ciki kamar zasu fidda fikafiki su fura da Mommynsu jin da ita zasu koma gida....

Ummy murmushi tayi sannan ta ce "Abbah nayi farin cikin jin haka amma sai dai akwai abu a ƙasa...".

Abbah ya ce " to sarkin ƙorafi ina jinki..."

Ummy ta ce "in har Mommy zata koma gidanka to a tabbatar an maida Auren ku domin bazata taɓa komawa gidanka babu Aure ba, kayi haƙuri Abbah..."

Dogon numfashi Abbah ya ja sannan ya ce "Uwar masu gida meyasa kike haka ne? meye laifi don ta koma gidana da zama ba tare da Aure ba? duk wata É—awainiyar ta zan É—auka, ci da sha sutura kuÉ—in kashe wa duk zan bata, sannan zan mayar ta wurin aikin ta..."

Ummy ta ce "duk da haka Abbah domin idan ta zauna da Auren ta zata fi yin daraja a idon mutane, bayan haka Mommy ba tsufa tayi ba balle ace tayi tsufar da bazata yi Aure ba, idan ka barta a haka zaka cutar da ita ne, kuma sannan idan tana gidanka babu wanda zai zo neman Auren ta kuma mu ma bason ta Auri wani muke ba, nasan Ammy bata da matsala zata yi farin cikin kasancewa da Mommy, please Abbah wannan shine Alfarmar da zakayi mana, sannan ka jawo mana mutunci Please..."

Abbah ya ce "shikenam idan har kasan shi zai sa kuyi farin ciki sannan ku zauna a inuwar mahaifinku nima na amince amma saboda ku..."

Ummy tsabar murna bata san lokacin da ta tafo ta rungumi Abbanta ba, duk sauran haka suka tafo duk suka rurrungumi Abbah..

Ummy ta hango Mommynsu tana zaune kai a sunkuyar ita kaÉ—ai sai zabga murmushi take..

Ummy ta ce "Mommy ke ma tafo gurin mijinki mana..."

Hajiya Kilishi ta girgiza kai tana dariya, dai dai lokacin Æ´ar tinny ta tashi daga bacci, ganin Abbah yasa ta nufo wurin sa da gudu tana faÉ—in "Abbah nah! Abbah nah..." ta rungume shi...

A yau suka magantu Abbah da Hajiya Kilishi suka fahimci juna da cewa tayi alƙawarin bazata sake ƙuntata wa kowa ba, zata yi ƙoƙarin ganin ta zama mutumiyar arziƙi, kuma zata cigaba da zama a gidan mijinta har ƙarshen rayuwar ta...

Gaba É—aya hamdala suka yi Abbah sai da ya jira aka kammala girki sannan suka ci su ka sha, kuma a wannan ranar Abbah zai tattare su a mota ya tafi da su tinda ba wani shirgi ne da su ba, duk wasu kayan É—akin Hajiya Kilishi ta sayar da su taci abinci da kuÉ—in,

Kafin su tafi sai da Abbah ya biya kuÉ—in hayan gidan da suka zauna sannan suka fiffito da akwatina da jakakkuna kowa ya kasance cikin shiri tsab, daga nan suka nufi Abuja...

★★★★★★★

Baiwar ALLAH gaba ɗaya garin ya yi mata zafi, tayi kukan har ta gaji, ga yanzu duk halin da zata shiga bata samun mai rarrashin ta, domin Roshan ko leƙa ɗakinta baya yi sannan itama bata zuwa yanda yake, suna gida ɗaya amma sai suyi kwana biyar basu haɗu ba...

Tana kuka tana tura kayayyakinta cikin akwati domin a halin yanzu bazata iya cigaba da zama a haka ba, ta yanke hukuncin barin gidan gaba ɗaya, ta shirya kayanta tsab ta fito falo hannunta riƙe da takarda da biro, ajiye akwati tayi a falo ta nufi part ɗin Roshan, a hankali take knocking cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya buɗe fuskar nan tayi fiyau ga yayi fari tass kamar ba jini a jikinsa da duk kan alamu bashi da lafiya ne..

Ganin Baiwar ALLAH yasa zuciyarsa bugawa ganin hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarta, a hankali yake motsi da lips ɗinsa ya ce "meya faru da ke?..."

Miƙa masa takardar hannunta tayi tare da biro tana kuka ta ce "ga shi nan, ban ga amfanin irin wannan zaman ba, dan ALLAH yau a kawo ƙarshen zaman nan Ni na gaji, wani sa'in har manta wa nake da inada Aure, dan ALLAH yau kam ka sallame ni, gidan zan bari gaba ɗaya, zan fita naje na nemo iyaye na..."

Roshan ya ce "ki kwantar da hankalin ki Razhdeen ya kusan dawowa..."

Cikin ɓacin rai ta katse shi da cewa "Ni babu ruwana da wani Razhdeen ban sanshi ba, dan Allah Yaya Roshan ka dawo hayyacin ka, ka tantance abunda nake so da kuma abunda bana so, amma yanzu komai yazo ƙarshe, yanzu dai ka sallame ni kawai...."

Lumshe idanuwansa yayi cike da damuwa ya ce "shikenam.." yasa hannu ya karɓi takardar da biro ya juya zai je ya rubuta mata, wani irin suka yaji zuciyarsa tayi tare da bugawa da ƙarfin gaske a firgice yasa hannu ya dafe sai tin zuciyarsa yana shirin kaiwa ƙasi.
Chapter 34 · 0% Book details