← Book details My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 39

Sashe 21

My Enemy Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abbah ya ce "a'a Daughter kar ki cuci zuciyar ki da kuma zuciyar wanda yake miki hallaci, nasan tinda kika furta masa cewa bakya son sa to kuwa bakya so ɗin dan haka a yau Roshan zai baki takardar sakin ki, da zaran ki kammala iddar ki za'a Aura miki Razhdeen, zan dakatar da tafiyar sa ƙasar U.S har sai an ɗaura muku Auren kafin nan..."

Baiwar ALLAH ba abinda take sai kuka domin tasan zai yi wuya Razhdeen ya amince, inda zai yadda to da kuwa tafi kowa farin ciki...

Abbah ne ya kalli Razhdeen sannan ya ce "Razhdeen kana dai jin abinda yake faruwa ko, bana buƙatar zaɓinka domin zaɓin marainiyar nan shine zaɓi na, ko ka so ko kar ka so dole zaka Aure ta tinda har Ɗan uwanka ya goyi bayan haka..."

Da sauri Razhdeen ya miƙe tsaye yana huci kamar wani kuntaccen zaki, har eyes ɗinsa sun rine yana motsi da lips ɗinsa a hankali ya ce "God forbid, that's not comp...."

Bai ƙarasa furta kalmar da zai fito daga bakin sa ba Abbah yayi saurin daka masa tsawa da cewa "You'll never escape for this choosing, dole ka Aure ta tinda ta nuna kai take so, uban waye ya ce ka rufe junanku a cikin bedroom na tsawon one week? daga kai sai ita, ita mace ce a koda yaushe kai take gani a cikin ƙwayar idanuwanta, idan zata kwanta bacci sai ta fara tozali da fuskar ka haka nan da zaran ta farka fuskar ka shine madubin ta, so know tell me how comes bazata kamu da sonka ba a halin da kuka kasance a tare? wanda nasan kaima ƙarya kake kace baka ji komai akanta ba, Razhdeen don't tell me the lie I known you too u really loving her..."

"Father I don't love her and I'll never love her in my life forever and ever..."
Razhdeen ne ya furta hakan tin kafin Abbah ya ƙarasa iddasa maganarsa.

Abbah ya ce "to amma meyasa ita take sonka?..."

wani irin kallo Razhdeen ya watsa mata mai haÉ—e da harara kafin ya ce "she losses her mind that's why..."

Cike da mamaki Abbah ya ce "Deen what are you talking about?..."

Tinda Razhdeen yake a wayonsa bai taɓa zubda ƙwallah ba sai yau shi kanshi Abbah sai da ya girgiza idonsa akan sa, shima Roshan miƙewa yayi tsaye ganin hawaye kwance saman fuskar Deen,
Razhdeen ya ce "bana sonta kuma bazan taɓa sonta ba har abada balle na Aure ta, Dad tell her bata samu mijin Aure ba indai ni zata Aura, now I hate her and if you post me to marry her I'll hate myself too..."

Abbah a firgice ya kalli wurin da Baiwar ALLAH take a zaune tana kallon ƙasin carpet ba abinda take sai kuka,
Abbah bazai iya juran ganinta a cikin wannan halin ba haka yasa ya girgiza kai ya maida kallon sa kan Razhdeen tare da faÉ—in "Deen dole zaka Aure ta, idan kuma ka azabtar da ita ko kuma ka kasa biya mata hakki zan iya tsine maka Albarka..."

A gigice Razhdeen ya É—ago da jajayen idanuwansa waÉ—anda suka sha kuka yana kallon yanda Abbah yake, jin kalmar da Abbah ya furta yasa kansa ya fara juyawa wani irin hajijiya ne yake shirin É—aukarsa..

Roshan shima zaro ido yayi yana kallon Abbah cike da mamaki, Uwar masu gida itama a ruɗe ta toshe bakinta da hannayenta biyu tana kukan baƙin ciki, bata taɓa jin haushin wani matuƙa ba sai yau daga Mahaifiyarta sai kuma Baiwar ALLAH...

Ammy ta ce "Amma Abban yara...."
bata ƙarasa maganar ba ya ɗaga mata hannu alamar ta dakata..

Ya ƙasara wurin da Razhdeen yake tsaye domin zama ya gagare shi, tsayawa yayi a gaban sa tare da faɗin "zaka sake bijire wa maganata a karo na biyu ko? Ƴar uwarka Amina ta bijire mun ta bi zaɓinta ta guje ni, kaima you can do that, now choose your's shin zaka bi zaɓin ranka ne ko kuma zaka yi abinda nace? idan har zaɓin ranka ka zaɓa kaje kaima na sallame ka..."

Abbah ya ƙarasa maganar yana zubda ƙwallah shima,
Razhdeen lips É—insa ne yake kakkarwa a hankali ya furta "Dad..."

Abbah ya ce "not your Dad har sai ka zaɓi ɗaya a cikin biyun nan, shin zaɓinka ko zaɓi na?..."

Razhdeen yana kuka ya matso dab da Abbah ya riƙe masa hannayensa biyu yana kuka ya ce "Dad you are my life and the something happen to my life I'll even to be leave, na amince zan Aure ta amma zaɓinka ne Abbah is not my chosen..."

Abbah ya ce "Deen are you sure are you going to get engagement with her ?..."
Razhdeen ya ɗaga masa kai tare da faɗin "bazan taɓa bijire maka ba..."

Razhdeen wani irin tsanar Baiwar ALLAH ne ya ziyarci zuciyarsa lokaci guda, ji yake kamar ya murɗe mata wuya tabar duniya, yayi matuƙar dana sanin haɗuwa da ita, tinda yake bai taɓa jin tsanar wani abu ko wani ko wata sai yau akan Baiwar ALLAH,

Abbah rungumarsa yayi yana faÉ—in "thank you very much my son..."
Shima Razhdeen rungumar Abbah yayi,
Baiwar ALLAH ce ta ɗago da manya-manyan idanuwanta waɗanda suka canza kamannu ta ɗora su akan Razhdeen wanda yake rungume da Abbah, lokaci guda taji zuciyarta yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske ganin irin kallon da Razhdeen yake mata na tsananin tsana...

Razhdeen idonsa akan Baiwar ALLAH yake maganar zuci yana faÉ—in "this is the first time that you make urself my Enemy, you are my enemy, I hate you and I'll never love you in my life, I hate you..."

Ga yanda ya zazzaro eyes ɗinsa waje sunyi matuƙar canza launin ja ya kasa ƙibta idonsa akan ta,
itama haka take kallonsa ido a zazzare tsananin tsoro ne da fargaba suka bayyana akan fuskarta, wani irin yawu ta haɗiya na tsoro, ba ƙaramin kwarjini ya yi mata ba...

Roshan idonsa akan Razhdeen ganin yanda yake mata kallon tsana da baƙin ciki gaba ɗaya jikinsa ba ƙaramin sanyi ba, dole yasan Baiwar ALLAH zata sha wahala sosai a hannun Razhdeen...

Abbah ne ya raba jikinsa daga na shi yana faÉ—in "idan ka taimaki marainiya kaima Allah zai taimake ka..."

Ya kalli wurin da Roshan yake sannan ya ce "Roshan kayi haƙuri ka bata takardar sakin ta..."

Shima Roshan ba abinda yake sai kuka yana daga tsaye ya ciro wata farar takarda a cikin aljihunsa ya nufo yanda Baiwar ALLAH take a zaune ya ce "Ammata yau burinki zai cika, ga takardar raba Aurenki da ni..."

Tana kuka ta miƙe tsaye itama tana fuskantar sa tasa hannu ta karɓi takardar idonta akan Roshan sai da ta dai-daici tsakiyar paper ta raba gida biyu, haka ta yayyaga takardar tana kuka ta ce "Yaya Roshan kayi haƙuri zan cigaba da zama da kai..."

Taje gaban Abbah ta durƙusa gwiwowinta ƙasin carpet tana kuka ta ce "Abbah ka gafarce ni, Uncle Deen baya sona bazan iya zama da shi ba, zan cigaba da zama da wanda yake sona har cikin zuciyarsa, zan canza hali na, zan masa biyayya yanda ya kamata..."

Abbah ya ce "kin tabbata har cikin zuciyarki abinda kike faÉ—i?..."
tana kuka ta ce "da gaske nake Abbah..."

Abbah ya ce "Alhamdulillah shikenam ki kwantar da hankalin ki mahaƙurci mawadaci yanzu wanda zai sama miki farin ciki shine ya dace dake Daughter..."

Jinjina kai tayi tana sauraron Abbah,
Roshan murmushi yayi ganin yanda ta sauya ra'ayi amma yasan ba har cikin zuciyarta ba, tayi hakan ne saboda gudun matsalar da zata shiga nan gaba tinda itama kanta tasan Razhdeen ba sonta yake ba, tsoronsa da fargabansa ne yasa tayi gaggawar janye ƙudirinta...

Razhdeen murmushin gefen baki yayi na mugunta a cikin ransa ya ce "is better for you..."

Razhdeen ya buÉ—i baki yayi magana yana faÉ—in "tomorrow early morning I will travel to U.S..."

Abbah ya ce "lokacin yafiyarka bai yi ba naga..."

Ya ce "Yes! zan tafi tin yanzu nayi muku sallama domin ba lallai na dawo ba, da sassafe zan wuce airport..."
yana kaiwa nan ya juya zai tafi, Abbah ya ce "Are you Angry with your Dad?..."

Razhdeen ya ce "no..."
a takaice
Abbah ya ce "okay zan tarar da kai a airport goben.."
Razhdeen ya ce "ok..."
daga nan ya yi tafiyar sa...

asmeetah writer ✍️

🤦‍♀️ *MAƘIYI_NAH*🤦‍♀️

*MY ENEMY _*

🫦 مقىينا 🫦

Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳

Asmeetah (giaÉ—e writer)

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

STEP TWO
👇
*26_ TO_30*

Razhdeen shigar shigar motarsa yayi ya zauna yana riƙe da sitiarin motar tsabar ƙololuwar baƙin cikin Baiwar ALLAH ne yasa ya kasa jan motar.
Baiwar ALLAH ne itama ta fito tana sharar hawaye ta nufi part É—inta bata ma lura da Razhdeen na wurin ba, shi kuwa idonsa akanta ganin bazai iya kyale ta haka ba yasa shi buÉ—e murfin motar sa ya nufi part É—in Roshan..

Baiwar ALLAH bayan shigar ta cikin falonta zama tayi a kujerar falon tana sabinta kukan ta, tana cikin wannan halin ta soma jin ana knocking ƙofar falon, da sauri ta share hawayen tayi tunanin Roshan ne bata so ta nuna masa damuwarta saboda kar ya ƙara samun Abbah da maganar, buɗe ƙofar tayi kwatsam ta tarar da Razhdeen a tsaye a bakin ƙofar yana mata wani irin kallo na ƙasƙanci wato kallon up and down...

Kutsawa yayi ya shige ciki a yayin da ita kuma take ja da baya domin ba ƙaramin ƙwarjini yake mata ba,
ma ta nuni yayi da ta zauna a kujera ba musu haka ta zauna eyes É—inta akansa shima jawo glass table yayi ya zauna a front É—inta suna fuskantar juna, fuska a haÉ—e ya ce "ki kalli cikin eyes É—ina kiga shin nayi kala da abokin wasan ki?..."
Chapter 21 · 0% Book details