← Book details My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 44

Sashe 7

My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Batare da yayi aune ba ko ya zata yaji saukar yatsun hannunta akan kyakkyawar fuskarsa me cike da saje abinda ya haddasa masa cin wani uban birki ji kaki qiiiiiiy! Abinda yasasu wata girgiza hakan baisa Rafi'ah ta daina tsumar da takeyi ba idanunta har yanzu na kansa ya saki baki yana kallonta rabon da asa hannu a mareshi har ya manta.
Bude qofar takai hannu zatayi yayi saurin danna pin din ta juyo cikin bala'i tace “zanci kutumar ubanka Ja'afar zan yaga alfarmarka da mutuncinka matuqar baka budemin motarnan ba...." hannu ya sa ya toshe kunnensa ta sake daga murya cikin qaraji tace “ka budemin mota nace stupid man kawa...." Bata rufe bakinta ba ya cafki bakinta da nasa ai baigama Kama harshenta ba ta gasa masa cizo a harshe dake cikkaken dan air ne ido kawai ya rintse ya sake tura harshen nasa cikin bakinta yana qoqarin sanya qarfi ya janyota jikinsa ta cure jikinta ta banqara ta kwace ta zame daga kujerar ta rushe da kuka tace “nashiga uku ni Rafi'ah wannan wacce irin baqar ranace Jama'a meye yake faruwa danine...." Bude motar yayi ya dube fiddausi yace “jeki little jirani...." Kafin ya ankara Rafi'ah ta bude qofar ta dire waje kamar wata mahaukaciya ta kwasa da gudun bala'i ta runtuma cikin daji.

Cikin tashin hankali ya fito yabi bayanta a guje dake dogone ita Kuma tsayin ba sosai ba sai gashi yacin Mata da taimakon bishiyar da tayi karo da ita ta caki goshinta tayi baya taga taga zata fadi ya tareta ta fada hannunsa ga matsanancin mamakinsa sai yaga ta fado hannunsa sumammiya abinda ya qara fitar dashi a hayyacinsa ya dagakai ya kalli Fiddausi data dafe qirji tanason mgn Amma tsoron jizginsa ya hanata yace “meye hakan Fiddausi saboda nace inasonta shine harta suma"
Cije lebe tayi tace “yaya abinda girma ka taimaketa ka kaiyi Mata urgent treatment" sabarta yayi a kafadarsa ya sata a mota ya shiga cikin garin Kai tsaye wani asibintinsa ya nufa sabone bai dade da budeshi ba ya dauketa kamar beby ya shiga da ita har dakin da zai dubata ya cire babbar rigarsa duk likitocin dake asibitin ya hanasu tabata dakansa yayi treet nata ya cire Mata iccen daya shiga goshinta ya wanke gurin da magani, yana tsaka da dressing din gurin wayarsa ta fara ring ya daga ganin number Ni'imah ya danna ok Bai bata damar mgn ba yace “naje cikin Bauchi ne inada wani petiant bama lallai tafiyar nan yau ba saboda yanada muhimmanci a gurina" yana Shirin kashe wayar yaji tace “sweet kaje gurin Bestie kace nace tabani abin dadi" duk da damuwar dake cinsa Saida yayi murmushi yace “insha Allah zanyi qoqari" yana fadin haka ya kashe wayarsa yaci gaba da abinda yakeyi.

Yana gama dressing din ta farka ganinta daure da drip yasata miqewa ta fincike allurar ta watsar juyowar da zaiyi yaganta tana daye dressing din da yayi mata ya nufota a guje yana cewa “kewai meye hakanne baki da hankali ne jibi yanda kika jiwa kanki ciwo kina tunanin hakanne zaisa na janye qudurina" wani matsiyacin kallo tayi masa ta nufi qofa ya nufota da niyyar hanata fita ta juyo tace “wlh tallahi ka qara matsata sai nayimaka ihu na tona maka asiri fajiri maci amanar qauna ka dauka ni yar iskace da zakazomin da wannan games din to kayi gaggawar lashe amanka kafin ka fuskanci qasqanci a gurina Ja'afar bana zama inuwa daya da maci amana maha'inci dan uwan shaidan me burin shiga tsakanin qauna,
Sakin baki yayi tare da rungume hannunsa a qirjinsa shi masifar tata ma burgeshi takeyi baitaba ganin mutumin da yake fada yana kyau ba sai ita yana wannan tunanin ta fice da sauri cikin saa tana fita ta fada napep ta fada masa inda zai kaita Koda ya fito baiga alamarta ba ya tambaya akace tahau napep kafin yaje ya dauko rigarsa ya nemo Fiddausi har takai school tana zuwa ta nufi hostel tanata wucce mutane bata gane su waye har ta Isa dakin ta fada gado ta rushe da kuka tana furta “ Innanillahi wa Inna ilaihirraji'un Allahummah ajirni fih musibati wa'akalifni khairin minha" ta jima tana kuka me dafa zuciya bata taba shiga tashin hankali irin na yauba ji tayi anzauna a gefenta ta tashi firgigit.
Ajiyar zuciya tayi ganin Nina ce tace “meye Kuma pretty?" Kukanta ta qarawa qarfi tanasa tisue tana tsane jinin da Bai daina zuba a ciwon ba Nina ce ta dauko wani dan qaramin akwati ta bude ta dauko auduga da magani tayi Mata dress na gurin tace “yanzu Mutuminnan na jiya yazo yabani magunguna yace na kawo miki garinyaya kikaji ciwo?" Dora Mata magungunan tayi a cinyarta tayi watsi dasu tace “kije kice masa banaso bana buqata ki hada masa da kayansa na jiya duka banaso ya fadi meye yakeso bayan wannan na fadawa abbana ya biyashi nidai roqona ya janye furucinsa, kwanciya tayi tace “Nina meye yasa mutane basusan girman aminta ba meyesa basusan darajar alaqa ba ? Meyesa Ja'afar zaiyimana haka wlh bantaba zatoba Koda wasa nayi tunanin duk abinda yakeyimin saboda Bestie na yakeyi min meyesa zaiyimin haka me yake nufi dani Nina ya cutar dani ko iya haka kalamansa suka tsaya na rantse da Ubangijin da yake rayani bayan ya kasheni a kowanne lkc nayi bacci bantaba jin tsanar wani mutum araina ba sai yau naji tsanar Ja'afar Wakil ta darsu a qoqon zuciyata natsani mutum maci amana"

Ta qarashe maganar tana shigewa jikin Nina tace “ko iya haka da wanne ido zan kalli Bestie mijinta yace yana Sona har ya hada bakinsa da nawa innanillahi wa Inna ilaihirraji'un Hasbunallahu wani'imal wakil wannan masifa dame tayi Kama nikam na shiga ukuna Nina qaddarorina sunada wahala"
Miqewa tayi kamar zararriya ta kalli gabas tama manta da ciwon dake goshinta tayi sujjada tace “Allah inhar ka qaddara yankewar alaqata da Ni'imah alaqar daka sardata tun bamusan kanmu ba Allah kada ka yanketa ta wannan hanyar ka karbi rayuwata na tafi na barta da mijinta abin qaunarta farin cikinta Allah nafi kowa sanin cewa Bestie na tanason mijinta Allah kada kabashi ikon cutar da ita Allah ka cire masa so da sha'awar duk wata ya mace a ransa bama niba ya Allah idan kayimin haka ka gamamin koma...."

Ji tayi an rufe Mata baki ta dago Nina tace “meyesa kike roqon farin cikin wata har kike roqon Allah ya kasheki akan farin cikinta?" Share hawayenta tayi tace “ba wata bace Bestie nace wlh tafi gaban haka a gurina zan iya bata rayuwata matuqar zata rayu cikin farin ciki meyesa mijinta zaice yanasona Nina meye bambamcina da Ni'imah mutane suna cewa saboda aminta Kama mukeyi toshi meye yasa yakeson raba amintarmu?"
Murmushi Nina tayi tace “ai jiya dana fada Miki baki yarda ba Rafi'ah tun ranar bikin da kika gayyacemu na fahimci sinadarin dake fita a idonsa sone da zallar qauna Amma wanne mataki kika dauka?" Shiru tayi nadan lkc kafin ta dago tace “zan yanke mu'amala da matarsa na dan lkc idan burinsa kenan" girgiza Mata Kai tayi tace “kada ki fara hakan zaisa ta zargeki kici gaba da mu'amala da ita shikuma ki take Masa dogon burki kiyi duk meyuwuwa kiga kinsa masa tsanarki ta yanda dakansa zai janye Rafi'ah jiya dana fada Miki haushina kikaji har kina cewa bazai yuwuba to gashi dai kin gasqatani" Jinjina Kai tayi ta miqe ta fada bathroom tayi wanka ta dawo ta kwanta ranar duk wata lecture batayi ba tanajin wayarta tana ring taqi ko dubawa balle ta daga Nina ce ta zauna tanata rarrashinta tare da nuna màta bafa wani Abu bane latsine irin na mazan zamani yanzu haka ma bazai qara mgn ba tunda ta nuna masa batada mutunci,

Da wannan ta dan samu kanta harta dauki wayarta ta fara duba kiraye kirayen kiransa yafi hamsin da layin data sani saina dayan daya rinqa turo Mata saqo jiya Wanda shima yakai talatin saqonni kuwa sunyi ashirin batako dubaba tayi delete all ta watsa layukan a black list kiran Ni'imah ta gani har hudu tayi kamar ta share sai Kuma taga rashin dacewar hakan yau gabadaya basuji junaba zatayi tunanin ko ba Lau ba hakance tasata kiranta dagawa tayi cikin muryar kuka tace “inata Kiran wayarki kinqi dagawa Bestie kinsan Kuma bana samun nutsuwa idan banjiki ba har na fara tunanin ko wani abune ya sameki na kiraki sosai da wayar Sweet ma baki dagawa I hope fine dai?"
Ajiyar zuciya tayi tace “banji dadi bane Bestie kaina na ciwo sosai Amma nasha magani na samu relief Ina fatan kina lfy Ina unborn dina?" Dariya tayi tace “waye yace Miki inada ciki wlh banida komai yanzuma period nakeyi in fada Miki jiyama Saida mukayi fada da sweet wai saina bashi nutsuwa Wai Ashe akwai yanda akewa namiji ya samu nutsuwa ko ana halin haila?" Dariya Rafi'ah tayi tace “matsalace dake babba Bestie Ina littafin dana zauna na rubuta na baki harfa buga mikishi nayi saboda kinsan rubutunmu na likitoci ba kowa ke ganewa ba, idan kika duba book din Zaki samu komai har addu'o'in da zaki samu daukaka da soyayyar mijinki nabaki sannan ki cire ganda Bestie ki tallafi mijinki namiji da kike ganinsa bashida tabbas don Allah kada kibani kunya wlh a shirye nake na baki taimako ta kowanne bangare indai akan mijinki ne inason Kuma Ina burin ki zama tauraruwa a gurin mijinta"
Chapter 7 · 0% Book details