← Book details My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 44

Sashe 14

My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Rafi'ah bata fiye dariya ba saidai murmushi amma kalaman qawar tata Saida suka bata dariya tace “kullum burinki a kudi ya qare kamar wacce kika tashi da haushin talauci meyesa ne Ni'imah ki bari don Allah kudi basuda wani muhimmanci a aure soyayya tafi komai indai da rufin asirin ci dasha da sutura da gurin zama majority's na Mata tunanin kudi sune jin dadi shine ke wahalar damu bance kudi ba abinso bane aa nima inasonsu Amma banaso su zama abin duba a mizanin auratayya ki auri mutum domin Allah da Kuma cancanta Bestie Kuma kada ki auri namijin da baya sonki ki auri wanda yakesonki idan kinji kinason dole saikin aureshi to kiyi qoqarin koya masa sonki tanyar kwadaita masa kyawawan halayenki qwaqwalwar namiji tanada fadi Amma zuciyarsa jaririya ce an halicceta dason me rarrashinsa da faranta masa yanason tarairaya da tattali uwa uba hqr domin soyayya da rayuwar aure tafi komai buqatar hqr Bestie Ina tayaki murna da samun irin mijin da kikeso Allah ya daidaita yasa kizama tauraruwa a zuciyarsa Kuma ya baki ikon kula dashi"
Numfashi ta sauke tace “amin sarki wa'azi idan sweet yazo zan bashi lbrnki da nasiharki gareni ke har record nayi fah zan kunna masa" murmushi Rafi'ah tayi tace “bakya girma bakya rabo da shirme ki gaisarmin da angonmu bazan dawo ba saina gama exams" sallama sukayi suka aje waya Rafi'ah tanajin farin ciki Bestienta zatayi aure Amma idan ta tuna rabuwa zasuyi sai taji hawaye ya wanke Mata fuska washegari Ni'imah ta kirata ta fada Mata mgn fah ta girma har ansa lkcn biki wata daya Amma angon yabar qasar bazai dawo ba sai ana saura sati daya biki.

Tayi Allah sanya alkhairi tare da cewa saura practicing uku su gama exams suna gamawa zata taho su fara shirye²n biki Ni'imah taci gaba da cusa soyayyar Ja'afar a zuciyarta shikuma bai wani qoqarin koyawa kansa sonta kawai ya karbetane bisa tursasawar mahaifansa musamman Hajiya fatsum da tayi tsalle ta dire tace bazai watsa Mata qasa a idoba da wanne ido zata kalli Hajiya Sahura tace danta bayason yarta.
Wannan yasashi hqr dadin dadawa da roqon da Mai martaba yayi masa na cewa kada ya bashi kunya tunda yarinyar ta amsa shima ya hqr zai sota a hankali tunda batada matsala, dole ya yarda da zabin na iyayensa amma tunda ya tafi Cairo gurin qaninsa bai sake tunawa da itaba Saida yaga saqonta a WhatsApp voice ne a qasa ta rubuta Masa _“Mijina bude kaji abinda aminiyata tacemin game dakai tanada hankali gata da hangen nesa inasonta fiye da yanda nakeson komai"_
Budewa yayi ya fara saurara jin sautin muryar Saida yasa gabansa faduwa hakanan baisan dalili ba yaji ya kwadaitu dason ganin mamallakiyar wannan zazzaqar murya kuma ma'abociyar hankali"

Batare da tunanin komai ba ya rubuta Mata _“to yayi muryarta tayi dadi Allah yasa haka fuskarta take"_ bata kawo komai ba tace _“fuskarta tafi muryarta dadi komanta mekyau ne kyau ya qare tunda aka halicci Bestie dina"_ dariya yayi yace _“anya kuwa sai nakega kamar batafiki ba"_ da wannan ya yaudareta ta turo Masa hoton da sukayi ita da Rafi'ah a kwance yake Amma Saida ya miqe zaune ya zuba Mata ido tanata zuba murmushi yar siririyar wushiryarta sama da qasa ta qarawa kyakkyawar fuskarta kyau gata yar duma duma ma'ana chubby ko inanta a cike kamar babu jijiya da qashi a jikinta dukda batada jiki amma ta wucce kace Mata siririya sumarta har goshinta dauke kansa yayi ya maida hankalinsa ga Ni'imah sai kawai ya rinqa ganin muninta musamman da yake ita siririya ce shikuma Allah yayisa dason chubby star din hoton yayi daidai lkcn da Ni'imah tace _“kayi Shiru Sweet?"_ Ajiyar zuciya ya sauke yace _“ban tantance ba turomin Wanda take ida kadai kema kike ke kadai"_

Sakaryar tura masa tayi bai jira me zatace ba ya daukesu to Gmail dinsa ya kashe Wi-Fi dinsa yaje yayi wanka ya dawo ya bude abincinsa yanaci yana kallon hoton kyawun qawar budurwar tasa yana birgeshi yanajin wani yanayi me wuyar ganewa a qasan zuciyarsa tun daga wannan ranar Ni'imah ta samu kansa daya fahimci itanma batada wani abin cewa idan ba lbrn qawar tata ba sai yake biye Mata sosai suyita Hira tana bashi lbrn Rafi'ah don karta gane yanajin dadin lbrn wani lkcn yake gwasaleta amma bata iya dainawa hakanan suka rinqa tafiyar da soyayyar ita a haukanta sone yasa yake biye Mata shikuma sonjin lbrn qawarta yasa yake janta jikinsa,
Ana saura sati biyu bikin Rafi'ah ta dawo suka shiga shirye shiye da invite din qawaye wata rashin saa tunda ta dawo Ni'imah keson hadasu ko a wayane amma taqi karba sai tace “ai batason yasan muryarta yanda zaiyi saurin ganeta so take tabashi mamaki duk ranar da suka hadu, to shima dake dan duniyar qasa da qasa ne bai takura ba duk da yasojin zazzaqar muryar a kunnensa Amma ya hqr yana saita sa'arsa batare daya bari kowa ya fahimta ba Amma bai zurfafa sosai ba saboda shima shima yana tunanin tanda zaayi ana saura sati daya bikin ya dawo saboda ya kasa jurewa yaje takanas ya sami Mai martaba ya fada masa idan da hali a hqr da aurensa da Ni'imah zai kawo wacce yakeso very soon

Kai tsaye mai martaba yace masa Babu hali dole ya dauki yan qafafunsa ya tafi bangarensa inda Muhseen yazo ya sameshi ya dubeshi yace “yadai ango meye ne naga kamar bakafa da walwala" kawai dakai yayi sanin da Muhseen yayi ba mgn zaiyi ba yasashi cewa “wlh wata baby ta rudani Prince Ja'afar na rasa Kuma ta inda zan fara" kallonsa yayi yace “nima halin da nake ciki kenan gashi nace da Mai martaba a hqr da aurennan yace babu hali wlh indai haka so yake to andade ana wahala a duniya ji nakeyi kamar idan ban sameta ba bazan iya rayuwa ba kay nifa nasan akwai qura a gaba don wlh ba aminta ba ko twins ne saina rabasu saina auri kowacce"
Dagowa Muhseen yayi da mamaki yace “suwa?" Batare da tunanin komai ba yace “Rafi'ah da Ni'imah Ni'imah ta kawomin tallan Rafi'ah zuciyata ta karbeta bantabajin son Ni'imah ba Amma son aminiyarta Rafi'ah yana neman zautani gashi a yanzu ban isa motsawa ba ko zan motsa sai na bari ita na sata daga ciki" gumine ya karyowa Muhseen yace “garin yaya hakan ta faru kanaso inaso ya zaayi kena...." Daukeshi yayi da mari yace “ka cire matata ce idan ka matsa wlh kasanni tsaf zan batar dakai" numfashi Muhseen yaja zafin zuciyar Ja'afar da kafiyarsa abar rubutawa ne a world news idan bai tursasawa zuciyarsa mantawa da Rafi'ah ba to tsaf zai iya aikata abinda yayi niyya nacine dashi kamar kuturu.

Miqewa yayi yace “Allah yabada saa Amma Kai kanka kasan abinda bazai yuwu ba ka dauko Ja'afar kasan halin Mata da kishi kuwa da zakaji shawarata sai nace ka cire ka hqr mace tanada sauqin samu alaqa kuwa wuyar qullawa gareta" Bai ko saurareshi ba ya miqe ya shige toilet ya biya buqatarsa ya fito yana goge jikinsa.
Muhseen baiyi fushi ba yace “Dazu Rafi'atuh ta kirani take tambayata meye shirinmu game da events sudai guda biyu zasuyi zasuyi BESTIE'S day sannan zasuyi NIKAH day so mukuma meye namu shirin?" Murmushi yayi yace kace nace duk abinda ta tsara shi zaa wanzar" haka Muhseen ya kirata yanajinsu ya sanar da ita ta amsa da cewa “kace masa muna gdy" daga haka ta kashe wayarta suka kalli juna sukayi ajiyar zuciya a tare.

Kusan komai na bikin tsarinta ne an kashe kudi sosai duk wani saqo ta gurin Muhseen yake zuwa Allah ya sardanta sabani tsakanin Rafi'ah da Ja'afar duk zuwan da zaiyi batanan wannan dalilin yasa basusan juna ba sai ranar dinner ranar ne ganinsu da juna na farko amma shi ya dade yanajinta a ransa da mafarkin cikar burinsa akanta wannan dalilin yasa baisa wasaba a lamarinsa yakebin duk wata hanya da yasan burin nasa zaiyi sauqin samuwa.
Kamar dai yau tunda ya tashi da safe ya shirya ya fice daga gdan Kai tsaye gdansu Rafi'ah ya nufa saboda yaji lbrn dawowarta a gurin Ni'imah da suna waya jiya da dare gaisawa sukayi da megadi yace ya shiga yayi masa sallama da Rafi'ah fitowarta daga wanka kenan tana shafa mai Anti Murja ta shigo tace “ki gama kizo kinada baqo a waje?" Kallonta tayi tace “waye anti?" Iska ta shaqa tace “bsnsani ba Mado ne yazo yacemin kinada baqo kiyi sauri kije don yadan jima"
Jitayi kamar tace bazata ba saidai ta daure ta tashi ta sanya kayanta ta fesa turare da dauki mayafinta kasancewar dama Shirin fita takeyi ta fito gabadaya tun daga nesa taji gabanta na faduwa babu wata alama da take nuna Mata wayene numbers na motocinsa JMW ne so wannan number Bauchi ce BZ124 AZR shiyasa bata kawoshi ba ta matsi motar sosai tana duba fuskarta a wayarta tsayawa tayi a jikin motar ta bude Jakarta ta jefa wayar daidai lkcn ya zuge glasses din motar ya leqo ta dago suka hada ido gabanta yabada wani rass taja baya da sauri tare da cewa “A'uzubillahi"
Chapter 14 · 0% Book details