← Book details My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 44

Sashe 20

My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Numfashi Hajiya Fatsum ta sauke tace “malam me hawainiya yace dole sai ta shigo gdannan abinda nakeso dake ki sanyawa zuciyarki salama ki barmu dasu wlh daga ita harshi tunda suka taboni saina tashi hankalinsu suda zaman lfy saidai idan anayi a lahira suyi ta shigo din  Fatsum cefa" kuka Ni'imah tasa tace “kuma fah itama kwanciya zaiyi da ita kwanciyar aure ko?" Tsaki Hajiya Fatsum tayi tace “to meye don ya kwanta da ita ke kin cika shashanci dukkanku ya isheku indai Magaji ne" numfashi Hajiya Sahura tayi tace “nidai zan koma gurin na gangare ayi yanda bazai kwanta da itaba don nima banason ya hada shimfida da ita irin Haj Amina jarabane idan namiji ya dandanasu baya iya rabuwa dasu kinsansu da tsafin tsiya ke yakamata ki fadamin haka tunda kece kike bani lbrn matar babanku buzuwa"  haka suka rinqa saqawa da warwarewa basubar gdan ba sai dare sukace Mata gobe ta fito da wuri zasuje gurin Mal na gangare zasu gabatar da ita sai Rafi'ah ta zama yar kallo Haj Sahura tayi Mata alqawarin gobe zatasa Dad ya canza Mata komai na parlourn ta, sunanan suna saqa da mugun zare Hajiya Innah da Karimah da Hafsatu yayan Hajiya Kaltume da sauran dangin ango sukakai kayan lefen Rafi'ah tare da sanya lkcn biki sati biyu abinda akayi zaayi wata guda Ja'afar ya murza kambu yace shi yagaji da ajiyar Mata a gidan wasu abashi abarsa kawai haka Mai martaba da Dad suka taushi Abba ya yarda a hakan Dad ne yace shi ya daukewa Abba komai da uba yakeyi shi zaiyiwa Rafi'ah  nan fah gidan Alh Nuhu ya hargitse aka shiga shirye shirye babu Kama hannun yaro ana bikin auta sha lele dinner kuwa Saida aka shirya hudu tun saura kwana biyar bikin ya dawo wani salo harda Prince Day wasu abubuwa da yawa baiyi a aurensa na farko ba hatta rawar jikin da yakeyi baiyi a bikinsa na farko ba duk abinda akace yana barin jiki zai zaro ya bayar kowa yasan cewa wannan aure na musamman ne a gurinsa Amma fah baisan halin da amaryar take ciki ba tun ranar da yaje tace bata buqatarsa ko waya Bai qara kiranta ba balle yaje itama kuwa ta watsar dashi dama baa gabanta yakeba.
Sai dare yaje gidan ya tarar da hakimar tasa a zaune a parlour sai karkada qafa takeyi bai kulata ba ya haye sama yayi wanka.

Saida ya huta sannan ya sauko sanye da kayan bacci ya zauna yana danna wayarsa Rafi'ah ya Kira har tayi Ring ta katse bata dagaba ya sake Kira saboda sosai yake azabtar da kansa da rashin jin nata ta daga tayi sallama ya dube Ni'imah yace “ranki ya dade saraki sai Allah wai bakisan kin sosa raina ba ko?" Banza tayi dashi yayi murmushi yace “shiyasa kullum kike qara mamaye zuciyata kin iyabada hqr sorry My luv wow! Sunan ya hau nikam na gama sa'ar Mata a duniya, am nace ba me kike shiryawa game da shagalin bikin nan ne kinsan fah wannan bikin na musamman ne banason a samu matsala"
Mamaki ya hana Rafi'ah mgn taji yayi dariya yace “kinada basira ok karki damu zanyi qoqarin naga na daidaita komai...." Qit ta kashe wayarta ita tsoroma yabata saikace zararre shi kadai sai zance yake yana bawa kansa amsa, kissing din wayar yayi ya kalli Ni'imah ya tashi ya matsa kusada ita yace “uwargida sarautar Mata ke me kike shiryawa ne?" Dannan zuciyarta takeyi saboda hudubar da Haj Sahura da Haj Fatsum sukayi Mata amma qarshe yakaita zuciyarta tafasa takeyi murmushi yayi yace “mgnr tarihin amarya kece zaki gabatar dashi ranar dinner saboda ke kikasan komai game da ita...." Zabura tayi ta miqe shima ya miqe ya daga Mata hannu yace “baki Isa kice aa ba dolene ramawa kura aniyyarta a gdannan dole kema kiyi Mata abinda tayi Miki bazata rasa wannan gatan ba wlh Kuma banason son zuciya gaskiya nakeso na rantse da Allah kikace aa yau saikin koma gdanku Kuma kikayi son rai wajen gabatarwa sai na tsinke igiyoyin aurena akanki"............

_Hmmm uhmm tab Allah ya qarawa Bestie's hqr wannan tantirin miji naku ya shirya🤔_

_Vote_
_Comments_
_Share_
_Please_

*_Ummuh Hairan_*

*_Wattpad-realfauzahtasiu_*

*_23-24_*

____________________________
____________________________

Hayewa sama yayi yana yan waqoqinsa tabisa da idanunta daya kawo ruwa wai itace zata gabatar da tarihin amarya Kuma har yana iqirarin idan taqi zai qara sakinta zubewa tayi a gurin zuciyarta na hantsilowa tace “allah wannan wannan irin dan iskan mutunne" ta jima tana kuka kafin ta tashi gwiwa a salube ta shiga dakinta Hajiya Sahura ta Kira take fada Mata abinda yake faruwa ta danna Mata ashar tace “ke me kikace masa?" Shiru tayi tana tsiyayar hawaye tace “idan nace zanyi mgn Mom sakina zaiyi nikuma wlh bazan tashi a banza wata tazo taci bulus ba"
Shiru Hajiya tayi daga bisa taja ajiyar zuciya tace “Hakane Kinga bari na Kira uwarshi naji ko zata iya wani Abu" ajiye wayar tayi ta zauna tayi sukuti saida wajen awa daya ta wucce ta kirata tace “ki kwantar da hankalinki kije kiyi idan kin tashi ki zagesu tsaf dagashi har ita wannan shawarar uwarsa ce Kinga ko banza kin bata musu taro...." Katse Mom tayi da cewa “mom bakisan Ja'afar ba itama Barebari batasanshi ba wlh duk abinda ya furta baya masa wahalar aiwatarwa saura fa igiya biyu auren idan na kuskura nayi abinda kukace nasan biyun zai tsinke a bainan nasi"

Tsaki Mom tayi tace “to kiyi abinda ya dace nikam wannan tujararren mijin naki ya fara kaini qarshe wallahi idan na waiwayeshi saiya Raina kansa ace aure ko wata uku baayi ba tashin hankali ya cikashi daga wannan sai wannan kayy wannan Ja'afar din jarfa ne gsky Hajiya Fatsum ta haifo mugun iri irin tsiya irin jaraba" haka suka hadu sukayita zaginsa bata ankara da yana tsaye akanta ba Saida suka gama tana juyowa taganshi harde da hannu a qirji.
Saida taji qirjinta kamar zai tsage tsabar tashin hankali ya shafa gashin bakinsa ya juya ya ficeTsaki taja sosai yaji tsakin amma dake miskili ne bai juyaba ya bude dakinsa ya shiga ya kwanta yanata juyi babu mataimaki takaici ya cikashi ya sake gyara kwanciya kawai yaja pillow ya rungume.

Amarya Rafi'ah kuwa tananan kullum cikin quncin zuciya take ta kasa karbar auren Ja'afar a qasan ranta kowa dai daya shafeta a salube yake hidimar bikin saboda damuwar da tayiwa amaryar tasu yawa duk wata kwalliya da akewa amare taqi yarda ayi Mata hatta lalle da wankin Kai qememe taqi duk wani daya Isa ya fada Mata taji ya fada tayi kunnen uwar shegu shikuwa Abba dama da aka fada masa cewa yayi a qyaleta kukanma kansa yakeyi babu meyi Mata maganin damuwarta sai Allan daya jarabceta, ranar ranar alhamis akayi kamu juma'ah takanas Hajiya Innah ta turo me kwalliya akan ayiwa amarya nanma tayi tsalle ta dire itafa bazaayi Mata ba dole haka aka qyaleta da yamma likis aka turo wasu arnan motoci domin daukarta wai Prince's day tana kuka tana komai Aunty Murja da Aunty Raziqa suka fito da ita cikin alqabbar da Saida akasha dambe sannan ta yarda ta saka suka sanyata cikin daya daga cikin motocin.
A cikin gidan Sarautar aka ware wani bangare aka kashe masa manyan nairori aka tsara gurin dinner tunda suka shigo sautin sarewi da algaitu ya cika Mata kunne suna busawa da bugun zuciyarta daqyar ta samu ta fara kamo addu'o'i tanayi wasu matane su hudu suka nufo matar da take suka bude suka fito da ita suka kamata anata yi musu ruwan kudade da turare itakam sai ruwan hawaye takeyi da shassheqa.

Wani bangare suka nufa da ita suka shiga Basu tsaya ba Saida sukakai qarshe suka qwanqwasa wani daki aka bude musu suka shiga Saida sukayi Mata guri a gefen gadon sannan suka russuna suka kwashi gaisuwa suka fice matsowa yayi gabanta ya jima yanajin sautin kukanta tanata shassheqa yanajin diran gunjin kukan nata har tsakiyar ruhinsa ya tsugunna a gabanta ya sanya hannu ya dage hular alqyabbar.
Babu kwalliya a fuskarta ga hawaye ya bata fuskar Amma bai hana asalin kyaunta fitowa ba, yaja ajiyar zuciya yana qara sauke injin idonsa akanta idanunta a lumshe suke sosai kukanta yake tabashi ya miqe ya zagaya dakin ya dawo fuskarsa a daure ya sanya hannu ya miqar da ita ya fara qoqarin zare Mata alqabbar ta riqe da sauri ya furzar da iska me zafi ya bude baki yace “ance rabonki da wanka tun shekaran jiya tunda bazaki iyaba ni zanyi Miki yanzu saboda banson qazanta"

Batasan sanda ta bude idanunta akansa ba yaci gaba da qoqarin cire mata rigar ta sake qanqame jikinta tana kuka tace “don....don Allah ja'....." Rufe Mata baki yayi ya dago kanta yace “ki roqeni wani abun Banda wannan tunda Ammi da Abba Basu Isa su saki kiyi ba ni na isa nayi miki"
Baijira cewarta ba ya faketa ya dagata cak tana kuka tana shure² yaqi sauketa Saida ya dangana da ita bathroom din dama ya shirya terming dinsa kawai ya tsomata cikin ruwan alqyabbar kawaiYa cire Mata nanfa suka Dora kokawa kowa naji da taurin kai takaici ne yasa baisan sanda ya keta riqar sabuwar atamfar sharratone din ba ta rintse idonta da qarfi jikinta na rawa ganin ta saki Masa tanata ajiyar zuciya yasashi kunce zanin ya zare Mata komai na jikinta pant da bra kawai yabar Mata ya fara wanketa tayi tayi ya qyaleta tayi yaqi.
Chapter 20 · 0% Book details