← Book details My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 44

Sashe 37

My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cikin sanyi jiki da mamaki ya sanya hannu jikin takardar daidai lkcn da taxi ta tsaya Ja'afar ya fito suka zubansa ido yana sallamar me motar ya nufosu Mai martaba gabansa ya fadi ganin irin muguwar ramar da dannasa yayi ga wani baqi da yayi qarasowa yayi ya russuna cike da ladabi ya gaida mahaifin nasa da surikinsa suka amsa tare da tambayarshi hanya yace “alhmdllh" Shiru ce ta dan ratsa kansa na qasa kunyar Abba yakeji tunaninsa ko yasan meye yake faruwa tsakaninsa da Rafi'ah ganin babu wanda yabi takansa yasashi miqewa ya matsa kusa da Innah ya zauna ya rafsa uban tagumi.
Lkc yaja sosai sannan wata likita mace ta fito dauke da jaririn a towel me kauri tana zuwa ta tsaya tace “Waye Ja'afar M Wakil?" Miqewa yayi da sauri yace “Gag...gani" gabansa na faduwa ya nufi nurse din tayi ajiyar zuciya tace “petiant dinka ta farka tun dazun saidai bata cikin hayyaci sai yanzu muka samu ta dan samu so Kuma tunda ta farka take sharar hawaye munyi munyi ta fadi me take buqata bakinta baya fita sosai Amma na iya fahimtar tana cewa Ja'afar M Wakil meyesa kayimin haka me nayi maka alqawarin farin cikin da kayimin kenan irin tukuicin da na cancanta gareka kenan?
Wadannan kalaman tuhumar su taketa maimatawa shiyasa naga ya kamata idan kana gurin kaje kaji meye take buqata"

Numfashi ya sauke me qarfi tare da miqa hannu ya karbi bebien dake nade cikin towel ya bude fuskarsa yaja wata qaqqarfar ajiyar zuciya yace “barakallahu ahsanal khaliqin" kyakkyawan yaron me muguwar Kama da ubanshi saidai qanqanta kamar an fyatoshi a hanci.
Juyawa yayi ya nufi dakin da yaga nurse din ta fito rungume da dannasu dan qarami kamar yar tsana, tana kwance saman gadon ya tsaya a kanta yanajin bugawar zuciyarsa da numfashinsa suna neman daukewa Koda bata cikin yanayin lfy da Kuma walwala ya sani Kuma ya shaida shidin rahama ce garesa a duk lkcn daya rabeta sai yaji nutsuwa tana wanzuwa a cikin ruhinsa.
Idanunsa ya sauke saman nata da suke lumshe ruwan hawaye na kwarara, tausayinta ysna ratsa gabbansa ya rasa meye yasa ya qaurace Mata har tsayin lkc haka Kuma ya yanke duk wata hanya da zata sanya ta samu sauqi yanada tabbacin duk wannan halin da ta kasance a ciki shine sanadi domin da ace bashidin bane bazai kasance Abu na farko da zata bude baki dashi a wannan yanayin me hatsari ba tabbas aikine ja a gabansa ya dawo Mata da farin cikinta fiye da baya.

Miqawa nurse din babien yayi yace “Asashi a Inquivertor" ficewa tayi shikuma ya tsugunna a gaban gadon ya riqo hannun Rafi'ah da yake daure da callular ya hada tafin hannunta da nashi ya matsa a hankali ya dora harshensa saman kuncinta yana lasar hawayen da yake zuba a idonta taja ajiyar zuciya tare da daga hannunta dayan ta dora a kansa sai ta fashe da kuka ta qanqamesa shima hawaye ne suka zubo masa ya janye da sauri yana qoqarin rarrashinta yace “kinga Rafi'ah ki bari kukannan Kinga aiki akayi miki baa buqatar yawan numfashi ma me qarfi balle kuka"
Ajiyar zuciya tayi ta bude idonta akansa shima itan yake kallo cike da tausayi da kunya yace “please kada ki tuhumeni wlh bansan ya akayi hakan ta faru ba ki tayani da addu'a kawai" lumshe idonta tayi kawai kamar mai bacci Amma idonta biyu tabbas tuhumarsa takeson yi saidai ya riga ya katse Mata hanzari a hankali tace “ina fatan kana lfy ba wani abune yasa hakan faruwa daya shafi lfyrka ba" a hankali take mgnr wanda sai mutum yasa nutsuwa sosai zai fahimci me take fada tausayinta ya qara cika zuciyarsa yace “lfy Lau ki huta idan kinji sauqi zamuyi mgn na gde da kyautar dan da kikayimin mai kama dani" bata Kuma ce Masa komai ba suka zauna na kusan 15 minutes a haka kafin ya fita Innah ta shigo ita da su Mai martaba da Abba bude idonta tayi ta saukeshi akan mahaifinta shima Saida gabansa ya fadi ganin irin muguwar ramar da tayi, matsawa yayi ya riqota qoqarin hadiye damuwarta takeyi yace “anya babu wani abu a qasan zuciyarki uwar manya nasanki da baqin zurfin ciki menene waye?"

Yana mgnr ne a rikice idanunta ta sauke akan Ja'afar da yake shigowa da kaya a hannunsa yaji tambayar da Abba yakeyi Mata hakan yasast saurin kadanta Kai ko bai haneta ba bazata iya fada ba a ganinta wannan sirrin gidanta ne tsakaninta da mijinta, ganin bazata fadaba yasa Abba furzar da iska yace “shikenan uwata banayi Miki dole Allah ya kawo Miki mafita" sakin hannunta yayi ya fice tabisa da kallo gabanta yana faduwa tasan bai gamsu da shirunta ba to Amma ya zatayi sirrin ciki sai hanji tasan babu abinda yàke tabbata a rayuwa dadi ko wuya komai me wuccewa ne zata hqr ta jurewa komai akan mijinta musamman da yake uban danta qaddara ta ko Ina ta hadasu batada yanda zatayi dashi bashida yanda zaiyi da ita dole su rufe sirrin juna,

Kwananta uku a asibitin ta samu qwarin jikinta kullum suna tare a asibitin duk da ta lura har yanzun ba daidai yake ba Basu cika magana ba saidai kallo da ido amma yana kula da ita matuqa ya daukewa likitocin duk wani Abu daya shafeta su kansu suna jinjinawa qwarewarsa tare da mamakin yanda akayi hakan ta faru yana matsayin consultant doctor matarsa ta hadu da irin wannan matsalar me wuyar sha'ani wadda ko mutum ya warke idan ya shiga damuwa take taba tunaninsa.
Ba huruminsu bane shiyasa basu zurfafa ba a fakaice dai suke bashi shawara suka sallamesu kwanaki biyar lkcn yaron yayi qwari sosai abu na masu abu kamar Wanda aka hurawa iska ya wani cika abinsa jajir dashi qirar ubansa duk Wanda yaganshi sai yace “masha Allah kamar ba bakwaini ba" daganan gdan sarautar akaso wuccewa ya tubure akan cewa shifa bazaa mayar da matarsa gidannan ba tunda dai ta haihu idanma can dinne baaso ya Gina Mata wani gdan akaita can zai zuba masu kula da ita Hajiya Innah ce ta dage itama akan cewa wlh bazaa kaita gidansa ba a dakinta zata zauna har sai tayi arba'in ita ba lfy ba shima Kuma ba lfyr ya cika ba kansa na cikin kwartanniya yace akaita can waye zai kula da ita da jaririn"

Daurin gindi ta samu gurin Mai martaba dole ya hqr badon yaso ba suka wucce da ita fada ananma yaso hana kaita part din Hajiya Innah Amma Babu fuska yanaji yana gani aka wucce da ita bangaren Hajiya Innah daki guda ta ware Mata da parlour aka gyaranta aka zubawa jariri kayan buqatarsa shima wannan da yana ganin gata a gurin wannan family inda yake fuskantar adawar qarqashin qasa ta mafi yawan bangarori,
Sunada wata Al'ada a gidan idan aka haifi jikin farko na da namiji qanne mahaifinsa ne zasu siyansa gadon bacci da kayan fitar suna harda bargon dauka a yanda tsarin yake idan baayi yaro hakan ba to qasqancine anayin wannan ne tun kwana biyu da haihuwa ko uku Amma shi gashi har kwana biyar duk Wanda ya kamata yayi Hajiya Fatsum da Hajiya Kaltume sun hanasu wannan Abu ya damu zuciyar Hajiya Innah da Ja'afar gashi ya siyo gadon anqi kwantar da yaron akai wai banasa akeso ba itakam rafi'ah bata wani damu ba saboda batasan zafin al'adar ba sai daren rana ta shidda da Ja'afar ya shigo dakin tana kwance tana feeding din yaronta ya zauna ya zuba musu ido duk ya susuce yace “ina cikin damuwa fah Rafi'ah meye yasa hakan take faruwa dana ya kasa samun gata a dangina idan har akayi suna baa kawo gadonnan ba shikenan bazai gaji sarautar gidannan ba meyesa komai daya shafeki yake zuwarmin a baibai Meye karfa Rafi'ah dazu Hajiya Kaltume take cemin wai duk matar data haifi Lil Prince aka kasa samun gadon baccinsa daga dangin ubansa to karface Kuma asalinta jinin bayice harma tana cemin indai akayi suna baa samu ba to wajibine a cireki daga cikin zuri'a domin zaki bata iri meye kalmar karfa take nufi ne....."

_More comments_
_More typing_

*_45-46_*

_____________________________
_____________________________

Duka na sosai kalamansa sukayi Mata Wanda suka sanya zuciyarta lugude itakam wannan abu na wannan fam yana bata ciwon kai ta rasa meye laifinta meye ta tsare musu, shirun da yaji tayine yasashi cigaba da cewa “Al'amura sai lalacewa sukeyi gashi wadda zatayimin wannan alfarmar daga Badi'ah sai Karimah to Badi'ah mahaifiyarta ta hanata dazun take fadamin ta siyi gadon Amma Hajiya Kaltume tace idan ta bada Allah ya daidaitata ita Kuma Karimah babu ita a jadawali saboda kasancewarta qarama a gidannan na rasa ta Ina zan bullowa lamarin nan  Allah kibani mafita"
Numfashi taja tare da yunqurawa ya taimaka Mata ta tashi zaune ta dubeshi tace “in advise ka cire jinin bayi Kuma karfa daga sashinka hakan zaisa ka rinqa samun matifa cikin rayuwarka Ja'afar don Allah kayimin wannan alfarmar inaji ajikina idan naci gaba da zama matsayin mata a gareka zamu wanzu cikin rayuwar qunci Koda kasancewar nasan duk wani Abu daya fado rayuwata to yardar sarkin sarkice Wanda baa masa dole,
Chapter 37 · 0% Book details