← Book details My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 44

Sashe 36

My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonta takeyi da rashin fahimta tace “ban gane ba Hajiya" miqewa tayi ta rufe qofa ta dawo ta zauna tace “saboda munafukai masu fakar ido am Rafi'ah da Hausa nayi Miki bayani ki miqe ki dage ki zama tauraruwa a gurin mijinki ta hanyar yan shige² nifa bance ki fita ba aa ki barmin komai zanyi Miki nidai hadin kanki nakeso"
Saurin girgiza kai tayi tace “astagfirullah Hajiya aa bazan iyaba nikam babu wanda nake dashi daya wucce Allah shine zai iyamin" Shiru Hajiya Kaltume tayi tana nazarin mgnrta kafin tace “Eh hakane kam kin Kama dahir Allah yasa mu dace" miqewa tayi tace “zan wucce kidai duba maganganuna akwai gyara a rayuwarki idan ba hakaba kinaji kina gani Zaki zama yar kallo" sallama sukayi ta tafi Rafi'ah ta tabe baki tace “dama Hajiya Innah ta fadamin ba Allah ne take kawoki ba kaji mace yar kalan masifa zata liqamin tsiya ta jamin raba tsaba da mahalicci na" shigewa tayi daki tayi duk abinda zatayi dare yayi tayi addu'o'inta kamar yanda ta saba ta kwanta tanajin cikinta yanata motsi tasan harma da yunwa kasancewar damuwar rashin mijin nata ta hanata cin abinci.

Ita burinta bai wucce ko a waya taji lfyrsa ba inda ya kasance duk Kira ana rejected haka ta wanzu idan taga dare yaqi tafiya takan tashi tayi alwala ta nufi mahaliccinta da, da yamma ta gama duk wani shirinta na karbar miji har dare tana tsara girkinta ta kashe lkcnta wajen shirya masa abinci tagama ta dauki wanka ta harde tana duba agogo takwai Tara goma sha daya Shiru.
Cikin tsananin mutuwar jiki ta dauki wayarta ta katsa numbersa gabanta na faduwa ta Kira cikin saa ya daga batare da yace komai ba taja fasali tace “barka da yini" qaramin tsaki yayi yace “inajinki" a sanyaye tace “lfyrka nakeson ji kwana uku bamu gaisa ba" wata qaramar dariya yayi yace “idan banida lfy nan nake jinya saboda haka indai Ina wajen gdannan kikajini Shiru to qalau nake" Shiru tayi maganganun nata suna hautsina nutsuwarta ta hadiye wani Abu me ciwo tace “ba nufina kenan ba gani nayi baka nemana idan na kiraka ma sai kayi rejected don Allah ka yafemin Best wlh nakasa tuna kuskurena gareka iyakar sanina dakai cikin watannin da mukayi baka iya barin Abu a ranka wannan ba dabi'arka bace tawace nima Kuma kullum Ina addu'ar Allah ya sassautamin nauyin baki saboda gudun kamuwa da wani ciwon akan matsalar da zan iya maganinta da harshena"

Maimakon yaji kalamanta sunyi tasiri a zuciyarsa saima tafasa da yaji zuciyar tasa tanayi yace “saime idan kin kamu da ciwon bake kika dorawa kanki ba kwanane yau ban shirya yinsa anan ba ni bama na Bauchi Ina Abuja Kira Kuma banaso ki daina idan kinqi kuwa ranki ne zai baci a banza sakarya kawai...."
Ajiye wayar tayi da sauri saboda a duniyarta takan hadiye kowacce irin damuwa Amma banda cin mutuncin iyaye shikuma ta lura hakan yafi Masa komai sauqi, zuciyarta suya takeyi sosai nadamar Kiran nasa takeyi da tasan abinda zai fada Mata kenan, kuka kam har saida taji jijiyar kanta na daurewa ta hqr tasha magungunanta ta kwanta zuciyarta nayi Mata wani irin zafi.
Abu kamar wasa tafiya sai qara miqawa takeyi daga sati antafi wata babushi babu alamarsa waya kam tun ranar da ta kirashi yaci mutuncinta take tsoron kiransa Amma ta wajabtawa kanta kullum saita tura masa saqon barka da safiya dana Saida safe shi kansa abin na damunsa sosai yarasa ya zaiyi ne wani sharadine Ni'imah ta gindaya masa wai idan ya kuskura taji lbrn yaje inda Rafi'an take sai tasa ya saketa shikuma tsoro ya shigeshi wani mugun tsoronta yakeji saiya daga waya zai kirata sai ya tuna cewa idan tasan ya kira Rafi'ah cin mutuncinsa zatayi hakan duk zafin kansa zai hqr ya share, wasa wasa har gashi da wata biyu a Abuja.

Yau tun safe ya tashi dajin wani qwarin gwiwa nason ganin Rafi'ah yana qissima watannin cikinta fitowa yayi daga daki ya tarar da hakimar tasa a zaune tanata fama da tuffa ya dubeta yayi mata murmushi yace “gimbiya yau watanmu nawa rabonmu da Bauchi ne?"
Dagowa tayi ta dubeshi a banzace tace “wata biyu da sati biyu mana wani abune?" Gabansa ne ya fadi yace “aa kawai dai na tambaya ne" yatsina fuska tayi tace “ok na dauka tunanin waccan yar iskar yarinyar kakeyi" dagowa yayi da sauri sosai kalamin ya tabashi Amma suna hada ido sai yayi qasa dakai yace “ah haba dai kawai dai tunanin cikin jikinta nakeyi"
Wani banzan kallo tayi masa tace “to ko zakaje ne" qasa yayi da kansa yana wasa da yatsunsa kamar wani qaramim yaron da yaje jiran umarni ta daka masa tsawa tace “tambayarka nakeyi ko zakajene?" Saurin girgiza Kai yayi tare da dagowa kawai sai idonsa ya ciko da qwallah ya miqe da sauri ya haye sama ta sheqe da dariya tace “sakaran banza da kace bakaji saura shegiyar baqar kadarar can labarinta ma saiya shafe a duniyar mutane daga ita har cikin jikin nata muga ta tsiya

_More Comments_
_More Typing_

*_43-44_*

_____________________________
_____________________________

Tunda ya shiga dakin ya hade Kai da gwiwa kuka yakeyi sosai kamar yaron goye zuciyarsa na azalzalar sa ya tafi Azare ya gano lfyr matarsa da cikin jikinsa Amma babu dama tsoro yakeji kada Ni'imah ta fahimci inda ya dosa ji yake kamar idan ya bata Mata rai qonashi Ubangiji zaiyi dabara ce ta fado masa ya miqe da sauri ya rufe qofar ya shige bandaki da waya a Hannunsa ya fara duba number Rafi'ah Amma Babu a wayarsa tsoro ya qara cikashi gami da mamaki duk inda zai duba baigani bs hakan yasashi kiran Hajiya Innah ta jima tana ring sannan ta daga daga yanayin muryarta yasan akwai damuwa.
A gaggauce yace “Am Innah Ina Rafi'ah?" Numfashi taja cikin tausayawa halin da dan nata yake ciki tace “anya magaji kana addu'a kuwa" katseta yayi da cewa “inayi Inna please kibani Rafi'ah magans nakeson yi da ita" murmushin qarfin hali tayi duk jikinta yayi sanyi tabbas akwai alamun nasara wata biyu an tafi uku ita kanta baya kiranta tunda ta kirashi tayi masa nasiha tare da fada masa halin da matarsa take ciki na yawan damuwa da kuka ga ciwon Kai daya sata a gaba ko abinci tasa a gaba saita kasa ci idan ta tambayeta sai tace ita ba damuwarta yazo gareta ba damuwarta ya daga wayarta taji lfyrsa Amma yayi block contact nata kota Kira baya shiga.
Sake katse Mata tunani yayi da cewa “don Allah Inna kibani ita wlh inajin idan banjita ba komai zai iya faruwa Inna ko wani abu ya farune?" Numfashi ta sauke tace “akwai damuwa me tsanani a tattare da Rafi'ah yanzu dai ma kar naja maka zance bata gidannan tana babban asibitin Bauchi suna treatment nata sakamakon jininta da ya hau yaqi sauka yau kwana uku batasan waye akanta ba Amma sunankia take ambata dazu ma da mai martaba yazo sunce indai jininta bai sauka zuwa wayewar gari ba to zasuyi Mata Cx su cire cikin jikinta me watanni bakwai saboda idan aka basshi zaa iyayin biyu Babu ba itan babu shi...."

Katseta yayi da cewa “Wht Innah Amma shine baku fadamin ba" murmushinsu tayi na manya tace “ai Wai da mukaga ba sune a gabanka ba Ja'afar duk da nasan wani abun bayin kanka bane Amma yana ishe hali nidai banga abinda yarinyar nan zatayi maka ba ka dauki wannan matakin akanta kafi kowa sanin yanda akayi auren nan bataso iyayenta basaso rabone kawai me gaggawa ya baka saar mallakarta Amma tazama abar wulaqantawarka kada ka sake kakai hqrn mutum me haquri da zurfin ciki qarshe idan ya kwance maka rawani duk duniya babu Wanda ya Isa ya daura maka so ka kiyaye"
Kashe wayar tayi ta shiga dakin da Rafi'ah take kasancewar itace a gurinta taqi bari a fadawa iyayenta abinda yake faruwa koda sukazo asibitin kafin jikin ys rikice tace kada a fadawa Abbanta idan yaji akwai matsala, hakan tasa sukayi Shiru Mai martaba da Hajiya Innah da Karimah sune suketa jele sai Badi'ah yar Hajiya Kaltume ce Amma itama zakkace batayo halin uwa ba zuba Mata ido tayi cike da tausayi duk ta kumbura ta dashe kamar bayan hawan jinin ma akwai wani abin dayake damunta daidai lkcn ta wani zabura alamun allurar ta saketa idonta a rufe Amma sai bige bige takeyi ta qarasa da gudu ta riqeta abinda ya janyo hankalin Karimah ta shigo da sauri ganin yanda matar yayan nata ta datse harshenta tana make make jikinta yana jijjiga yasata fita a sukwane ta Kira likita ya biyota da sauri suka shigo daqyar ya samu yayi Mata allurar kashe jiki sannan ya Kira sauran ma'aikatan ya dubesu yace.

“Wannan bazatakai gobeba a yau ayi Mata aiki arabata da cikin nan idan ta qara awa daya zata farka alamominta sun nuna zata iya kamuwa da ciwon jijjiga Wanda zai iya haifar Mata da depression domin kuwa akai damuwa danqare a zuciyarta" Babu bata lkc suka sanya Mata kayan theater suka turata suka shiga da ita dakin theater sai a lkcn ne Hajiya Innah ta Kira Mai martaba ya daga take fada masa halin da ake ciki tare da cewa “Ranka ya dade fah abinnan yafi qarfin Shiru a fadawa iyayen yarinyar nan likitoci sun shiga da ita dakin aiki Amma sunce sai wani shaqiqinta ko mijinta ko mahaifinta yasa hannu sannan zasu tabata" miqewa yayi daga kishingidar yace “to bari yanzu zan fito" dakansa ya tuqa mota hankalinsa a tashe sai office din Abba ya rakitosa suka tafi asibitin Abba baisan meye yake faruwa ba Saida sukaje likitan yayi masu bayani ya shiga rudu da tashin hankali ya dago yace “ina mijin nata to ranka ya dade ai huruminsa ne wannan" qasa Abba yayi da kansa yace “bayanan yana Abuja baimasan abinda yake faruwa ba Amma zamu sanar dashi yanzu dai kasa hannu a ceto rayuwarta yafi komai muhimmanci.
Chapter 36 · 0% Book details