← Book details My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 44

Sashe 21

My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Aikuwa ta Raina kanta ta dirzu miqewa yayi ya bare sabon towel ya miqa Mata fuskarsa kamar Bai taba dariya ba yace “ki tashi jiranmu akeyi ki fito banson sakarcin nan naki" yana fadin haka ya fice daga bathroom din yama fice daga bangaren gabadaya qarasa wankan tayi jikinta har yanzu rawa yakeyi tana jera masa Allah ya Isa dama Wanda ya fada mass batayi wanka ba, towel din ta dauro ta fito ta ishe wannan matar da taje yimata kwalliya taqi da wata me kamala a zaune a dakin tsoro ya cikata amma sai taga wannan kamilar ta matso ta kamo hannunta tace “na zaci can zaa kaiminke Ashe Baban Innah ya murda kambu to hakanma yayi Salamatu kiyi ki shiryata goma na dare zaa fara walimar naga yanzu har takwas kinsan Magaji ba hqr ya cika ba" zaunar da ita tayi Salamatu ta miqa Mata Mai ta fara shafawa har yanzu ta kasa tsayar da ruwan idonta bayan ta gama salamatu ta fara aikinta ana kwalliyar hawaye na gogewa daqyar Hajiya Innah ta rarrasheta tayi shiru akayi kwalliyar tabata wani arnen leshi tace tasa ta sanyashi yayi masifar yimata kyau kasancewarsa maroon daurin dankwalinta ma an dauki kusan 30 minutes sannan aka gama Hajiya Innah ta bata sabuwar alqabba milk da akayiwa ado da Marron tasa Mata takalmin alqabbar shima milk ne sai awarwaro na gold masu tsadar gaske dayan hannun Kuma agogo sai zobba da dankunne da sarqa habawa wannan rana ta musamman ce duk da bata cikin nutsuwar zuciya data kalli kanta a madubi Saida tayi hamdala tare da ajiyar zuciya.

Bude qofar sukaji anyi jakadiya ce tazo ta fadi gaban Fulani Innah tace “Allah ya qara Miki lfy Mai martaba Magaji ne yace ayi muku mgn taro fah yayi taro ku kadai ake jira" dago Rafi'ah tayi tace “mun gama yanzu zamu fito" turaruka ta fesa Mata ta Kama hannunta suka fito kicibis sukayi dashi a qofar shigowa bangaren ya kalli Rafi'ah ya kawar dakai yace da fulani Innah “sannu mun wahalar daku" murmushi tayi tace “nadai fada maka idan kun tashi yanda zakuyi" kallon Rafi'ah yayi yayi murmushi yace “natsani wannan kukan wlh ki daina babu abinda zai hana saima tunzurani da kikeyi"

Tsakaninsu da gurin zamansu babu nisa ya janyota jikinsa ya shaqi qamshin turarenta ya sauke ajiyar zuciya suka fara takawa a haka tanata qoqarin janyewa yaqi bata dama takan wani farin carpet sukabi wasu dogarai na takensu gaba da baya sunata kirari da ihu tuni sautin dake tashi a gurin ya canza akasa na gidan sarautar saida suka zauna sannan mutane suka rinqa tasowa suna zuwa suna kwasar gaisuwa suna zuba mawa amarya da ango kari Ni'imah na gda batasan wainar da ake toyawa ba.
Saida lkc yaja sosai ta samu labari aikuwa kishi da baqin ciki ya tunzurata ta dauko mota ta fito tana rayawa a ranta wato ita bata isaba shiyasa baiyi Prince's day a aurenta ba sai wannan auren cin amanar ya tarawa mutane, anacan anata shagali biki yayi biki taro yayi taro ango sai washe baki yake yana satar kallom Rafi'ah da tayi kicin² da fuska taketa jan zuciya shi hakanma nishadi yake bashi, batare da sunyi tsammani ba kawai saiji sukayi an wankesu da ruwan Sanyi qarara abinda yaja suka miqe gaba daya MC baisan me akeba yanata zuba babatu saiji yayi ance “ku dakata yaku taron tsinannanu Wanda kuka taru saboda auren tsinanne da tsinanniya to ku sani dukkanku kunyi kadan kuci mutunci na harni zaaci Amana a cuceni........

_Vote_
_Comments_
_Share_
_Please_

*_Ummuh Hairan_*

*_Ummuh Hairan_*

*_Wattpad-realfauzahtasiu_*

*_25-26_*

_____________________________
_____________________________

Tasowa dogarai sukayi da sauri sukayi Mata cahhh suna fadin “Saita kalami yar talakawa...." Saurin daga musu hannu yayi ya miqe ya taka cikin cikar Izzarsa ya Isa gabanta tanata huci tana cije lebe, dafa hannu yayi tsammaninta marinta zaiyi sai taji ya sauke hannunta a kafadarsa ya janyota jikinsa ta fara qoqarin fincikewa yasa dukkan qarfinsa ya mannata da qirjinsa ya karbi abin mgnr yayi gyaran murya cikin sauti me nuna asalin izzar sarauta yace “da farko inayiwa baqinmu barka da zuwa tare da baku hqr a bisa abinda wannan zautacciyar tayi muku akasi aka samu baasan ta fito ba tadan hadu da matsalar brain ne idan abin ya motsa tana fuzga so do Allah kowa yayi calm down komai zai wucce am Sarkin gda da Sarkin qofa ku mayar da ita bangarenta a qara Mata tsaro don gaba kadan duka zata fara"
Yana fadin haka ya dago sakar Mata murmushi ya daga Mata yatsa ya barta tsaye sororo kafin ta ankara taji an cafeta sama an fice da ita daga gurin aka cillata a wani killataccen bangare a gdan shikuma ya koma gurin amaryarsa yana zama ta miqe ta fice daga gurin a guje ya sa aka bita itama aka riqe masa ita ya taso ya iso gareta yasa hannu ya kamota ya fice da ita daga cikin taron bangaren da aka fara kaita nan ya nufa da ita ya cillata saman kujera ya fara bala'i yana cewa “kema mahaukaciyar ce irinta da zaki biyeta ku watsarmin da mutunci a bainan nasi?

Miqewa tayi tana huci tace “akanme zakace mata mahaukaciya bayan kafita hauka da kana tunanin zaka samu wannan damar ka gama shimfida son zuciyarka a banza ne kana tunanin ko ita ta qyaleka duniya zata qyaleka ne? Ja'afar Ka cutar damu Allah ya isa wlh bazamu yafe maka ba Kaine Ummul aba'isin kowacee masifa ta rayuwarmu da dadi da wuya mun jurewa juna har kawo lkcn daka riskemu Ashe Kaine qaddararmu Kaine bala'in da zai fado rayuwarmu ya rusa mu kacina son kanka da son zuciya Wanda na tabbata duk Wanda yabi son zuciya qarshensa nada......"
Wata fusga da yayi Mata ta hanata qarasa kalaminta ya cillata gadon yabita ta zulle a guje ta nufi bathroom yabita ya sake wartota ya hadata da bango yace “qarya kikeyi Rafi'ah bazan taba nadama ba a rayuwata giya nasha ko caca nayi kokuwa zina na nemeki da ita da zakice zanyi nadama? Oh God" ya fada tare da bude qofar a fusace ya fice daga dakin ta koma ta zauna tana wani irin kuka me ciwo tana tambayar kanta me hakan yake nufi kenan ya kawota bangare babu kowa ya ajiyeta babu kowa nata.

Tana wannan tunanin taji an bude qofar an shigo ta dago da sauri ganin qanwar Ammi Bushira da Aunty Murja da Aunty raziqa yasata miqewa da sauri qarasawa sukayi gabanta Aunty Bushira ta Kama hannunta ta zaunar da ita tace “bazaki daina kukannan ba ko gashinan kinjawa kanki Ja'afar ya rantse bazakibar gdannan ba kinzo kenan...." Dagowa tayi da razane tace “ban gane ba?" Aunty Raziqa ce ta harareta tace “wannan haukan da kukeyi Kuna gwara kan mijinku babu abinda zaija muku sai raini da wulaqanta ita idan kishi yasata ta haukace ke mene hujjarki na haukacewa to wlh Abba yace ki kiyayi fushinsa sarai zaku raba hanya indai akan aure ne kowa ma yasan mijinku bai kyautaba to Amma shima ya zaiyi da zanen qaddararsa tun kafin a haifeshi sukayi alqawari da Ubangiji na duk wani Abu dazai faru dashi tun daga ranar da ya fara shaqar iskar duniya har zuwa Rana ta qarshe a rayuwarsa haka kema haka Ni'imah to akanme zaku haukatashi ku mayar dashi ball a tsakaninku ita ta bugashi nan ke ki bugashi can ko kin dauka saboda ya aureki don yana mijin aminiyarki babu alqalami tsakaninku to wlh ki dawo hayyacinki nasan iyayenmu basu barmu da jahilci ba saidai kana sane ka take sani sakarya kawai da takeson wasa da damarta"

Durqushewa tayi a gurin sosai kalaman Aunty Raziqa suka ratsata Aunty Murja ta dora da nata itama me ratsa bargo kafin Aunty Bushira ta cafe da cewa “gashi Allah ya baki mijin da yake sonki duniya ta shaida hakan Amma kinason yin sakacin sane masa kibi a sannu duk abinda hqr Bai bada ba to tashin hankali ma baya badashi dole yace yau a gdansa zaki kwana Ammi da Abba basuda damar sake ganinki wannan dalilin yasa zamu ari bakinsu muci musu danyar albasa Rafi'ah gdan yawa kika shigo Kuma gdan sarauta akwai qalubale a gabanki musamman daya kasance surukarki bata maraba da zuwanki dama yan uwan mijinki da suke daki daya dayan dakin Kuma su bama asan inda suka dosa ba Fulani Innah ce kawau take maraba dake sai mijinki to aikine ja a gabanki ki nutsu ki gane masoyi da maqiyi ki Kama masoyanki shima maqiyin karki canza Masa kallo karbeshi ki riritashi idan ya zaqe kai qararsa gurin Allah zaiyi Miki maganinsa abokiyar zamanki ma yanzu cikin sahun maqiyanki take yanzu haka mun barota tana alwashin saita kasheki saboda haka itama iya zama da ita zauna da ita da kyakkyawar zuciya zakiga ribar hakan anan duniya da gidan qarshe"
Chapter 21 · 0% Book details