← Book details My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 44

Sashe 27

My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Ke shashasha ce to ki fito mana idan aka gama abinda zaayi minti nawa ne zaki dawo kiyi masa inma kafi tuwon alkama ne Kuma ma idan ansamu yadda akeso ai bai Isa yace qala ba" dadine ya cikata tace “ok hakane ganinan" daukar Jakarta tayi da mayafinta ta fice tana dariya tana cewa “Ja'afar Wakil ka bonu ka lalace a gurina" mota ta dauka ta nufi qauyen tana zuwa ta tarar da uwar mijin nata da uwarta sunyi gurfane kamar masu neman gafara.
Dariya boka na gangare ya sheqe da ita yace “shegiya haihuwar asara ta sabawa umarnin miji ta fito toke an fada Miki wannan yarinyar a zaune take ai munafurtarki takeyi tana zagayewa tana bin manyan bokaye yo baki ganiba ko a yammatancinku tafiki farin jini ke Saida aka rinqa hadawa da layu da guraye sannan aka samu aka hadaki da wannan kaffafen mutumin da kurwarsa taqi juyuwa to ai baki sani bama tuni burinki yana gaf da rushewa ke wata biyar yana baki kinaqin karba ita kuwa tun ranar farko ta karbe yanzu haka da cikin yariman Azare me jiran gado a jikinta....."
Zaro ido sukayi tare da dafe qirji dukkansu Hajiya Fatsum tace “ciki Kuma daga zuwanta haba boka sake dai dubawa ni dana bashida wannan azarbabin" tsawa boka ya daka Mata yace “ankare nutsu tsinanniya wacce ta fatalar da aljannarta na rantse da bukkata Rafi'ah amaryar danki Ja'afar tanada shigar ciki saidai a dauki mataki Amma cikikam akwaishi abinda yasa naqi yarda na rusa aurennan kenan na hango rabo me zafi yana yawo inma baayi aure ba to zaa lalace ayishi a titi yanzu mafita dayace idan bakwa buqatar cikinnan zanbaku wata laya kusan yanda zakuyi ku haqa saitin inda kukasan koba kullum ba wataran dole sai tabi gurin ku binne to indai kukayi haka duk sanda ta samu ciki ko ya Isa haihuwa indai ta taka gurinnan saiya bare hhhhhhhh tsinannu Kuma karba fa zakuyi ku?"
Tsoro ne ya shigi Ni'imah tace “kayy aa gaski....." Bige bakinta Hajiya Sahura tayi tace “aa ubanki ai dole mu karba ke baki kishin kanki baki fatan ki zama uwar sarkin wataran" kallon Hajiya Fatsum Hajiya Sahura tayi duk hatsabibancin Fatsum tana shayin Sahura take tace “abamu boka nima banason shegiyar yarinyar nan ta hada iri da dana wlh irin Hajiya Amina ai irin masifane buzuwa ce fah tsafi sukeyi su bama asiri ba".............

_More Comments_
_More Typing_

_Ummuh Hairan_*

*_Wattpad- realfauzahtasiu_*

*[email protected]_*

*_YouTube- Open eyes multimedia_*

*_Telegram_*
          👇
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7

*_33-34_*

_____________________________
_____________________________

Dariya boka ya sake sheqewa da ita ya dauko wata laya ya miqawa Hajiya Fatsum yace “to debabbiya wacce ta saki danta ta Kama gaibu wannan asan yanda zaayi a binne ta da an binne mgn ta qare ciki zai lalace duk lkcn data tsallaka gurin da aka binne amma ayi takatsantsan kada ido ya gani" murmushi Barebari tayi tace “haba boka yau muke tare mukayi aikin da yafi wannan wahala ma bare wannan gashi shekaru sunata tafiya 38 years taqi fasuwa kawai kabar komai a yanda yake ni zanji da komai"
Ashar ya qunduma Mata yace “hhhhh shegiya yar fashi da dabara ashefa ke har fashin rayayye kikeyi ki sanya matacce a wannan aikin bazaiyi Miki wahala ba dama na irinku ne marasa imani kije kiyi yawwa sai wannan ruwan rubutun duk yanda zaayi yau yakai cikin Rafi'ah kota abinda zataci ne indai batayi Bismillah ba to aikin gama ya gama sauran bayanin zakugani da idanunku Amma fah kubi a sannu idan kika kuskure kwabarki zatayi ruwa asirin da kika Dade da binnewa zai fasu" tsawa ya daka musu suka firgita yace “ku tashi tsinannu uku wadanda basuda rabon lahira" tashi sukayi da baya da baya suka fita daga bukkar bokan suka nufi mota kowanne da abinda yake aunawa itadai Hajiya Fatsum tunanin abinda kaje yazo takeyi tunda take da Ja'afar iyakar sonta data mallakeshi ta kasa ta kashe millions of Naira don kawai ta cire masa jin Hajiya Innah aransa Amma ta kasa saima ya zamana kamar qara musu shaquwa takeyi yanzun ma game da abinda ya shafi Rafi'ah tafi tsoron Hajiya Innah fiye da ita kanta Rafi'an domin ita tasan an gama da ita indai maganin nan yaje cikinta to mgn ta qare sallar farillah ma sai anyi da gaske zatakeyi bare nafila.

Cikin saa har suka koma qarfe daya da rabi Ja'afar bai dawo ba da sauri suka nufi qofar bangaren Rafi'ah dake Intalok ne basusha wata wahala ba suka qwaqule daya daqyar sukayi haqa suka jefa layar gashi kuwa sun iya saiti dake tsofaffin  mushirikai ne bayan sun gama suka mayar da abinda suka bambare suka debo farin yashi a waje suka zuba suka sake zuba ruwa suka saki ajiyar zuciya tare,
Bangaren Ni'imah suka shiga suna mayar da numfashi Hajiya Fatsum ta dubi Ni'imah tace “ah ke abin naki harda qazanta Magaji ya tsani qazamin mutum gsky ki zage wajen tsafta idan ba hakaba kina ganinsa zaiyi Miki fintinkau" yatsina fuska tayi tace “to Hajiya ga yan aiki harsai wani nayi aiki girman ma ai yanada halin da zai nema mana kuku tunda dama babu inda akace na rinqayi masa girki" tabe baki Hajiya Fatsum tayi tace “ai gakinan gashi ni Ina ruwana" kitchen din suka shiga su uku sukayi Mata tuwon alkamar da miyar kalkashi sai farfesun kifi cikin lemukan ne tace a hada na kwakwa a zuba rubutun a ciki saboda duk lemukan duniya Rafi'ah tafi sonshi, aikuwa suka zage suka hada ta dauka tasa a freegde suka tayata ta gyara bangaren su kansu ba wani iya gyaran sukayi na tsanaki ba andai burbura sukayi suka tafi saboda basason yauma ya dawo ya tarar dasu a gidan ita Kuma Ni'imah ta fada wanka ta kashe kala ashe iskanci ke hanata kwalliya ta iya,

Dawowa tayi parlour ta harde abinta Ja'afar ya shigo gdan bai shigoba sai bayan la'asar sosai suka shigo shiga Rafi'ah ya daukota daga makaranta tunda suka shigo taji gabanta na faduwa ta fara karanto addu'o'in neman tsari ya bude Mata motar Ni'imah na kallonsu ta window ya riqe Mata jakar ta fito ta sunkuya ta karba ya lakace Mata hanci sukayi dariya ya Kama hannunta suka shiga ciki,
Suna shiga suka fada wanka yau wankanma tare akeyinsa itadai duk a kunyace take Amma batada mafita hàka sukayi suka fito ta shiga kitchen da sauri dama tanada miya data soya jiya ta dafa musu farar shinkafa ta hada salat ta zubo musu suka baje a parlourn sunaci suna Hira tuni ta manta da komai ta zage tana bashi lbrn irin wahalar da tasha jiya da irin ciwon da kanta keyi bayan sunci abincin ya dauko Mata paracetamol a clinic dinsa na cikin gdan yabata tasha ta miqe da gaske yau taci biro da yawa kanta sarawa yakeyi ta shige daki ta kwanta
Sannu ya rinqayi mata yana tofa Mata addu'a a goshinta hardai ya samu bacci ya dauketa wannan dalilin ne ya hanata zuwa dinner lkcn dinner tanata baccinta yana jiran ta tashi har Tara na dare gashi Ni'imah ta dameshi da kira kawai saiya tashi ya tafi shi kadai tana ganinsa shi kadai tace “ina take?" Yanda tayi tambayar yashi qara saita injin idonsa akanta yace “wa kenan?" Qasa tayi da kanta tace “Rafi'ah Mana naga kun shigo tare Kuma naga yanzu kazo Kai kadai ita bazakayi Mata dole tazo taci abincin anan ba?" Murmushi yayi yace “bayin kanta bane yanzu hakama tana bacci kantane ke ciwo sosai karki damu ita batada matsala"

Shiru tayi zuciyarta cinkushe da takaici da baqin cikin yanzu idan batazo ba duk shirinsu ya rushe" kallonsa tayi tace “Amma daka tasota ai qila ta yini bataci komai bane batason cin abinci idan abinta ya motsa saita kwana uku bataci wani Abu me nauyi ba" baice Mata komai ba yayi Bismillah ya faracin tuwon yana korawa da lemon abarbar  duk da bayajin yunwa Amma yaci da kirki ya dago ya kalleta sai juya cokali takeyi ta kasacin abincin yace “bake kikayi abincin nan ba dandanon girkin ba naki bane na Barebari ne"
Da sauri ta dubeshi yace “banason musu akan abinda nariga nayi yaqini akansa kodai kinje ko Kuma tazo wanne ne ya faru a ciki?" Hade rai tayi ta fara qunquni yayi murmushi yace “bazaki nutsu ba da kinkwantar da hankalinki sai yar uwarki ta koya Miki da muka tafi nake fada Mata cewa tayi zakisha wahala na kiraki na fada Miki ki jira ta dawo sai kuyi" harara ta watsa masa tace “sai Kuma nace Ina neman taimakonta"
Ganin ta juyawa zancensa ma'ana yasashi jan bakinsa ya tsuke ya tashi yayi gyatsa yayi hamdala yace “babu wani Abu ko zan tafi?" Miqewa tayi da sauri tace “bari na baka wannan lemon kwakwar nasan tanaso Kuma zataji dadinsa kasa Mata a freedge idan ta tashi saitasha" yaji dadin nuna kulawarta ga abar qaunar tasa ya karba yayi kissing nata yace "kin fara hankali Saida safe" ficewa yayi yabarta tsaye  cikin jin dadi tasan indai Rafi'ah taga lemon to bazataqi shaba da zaran Kuma Tasha to aikin gama ya gama zasu kassarata cikin sauqi
Chapter 27 · 0% Book details