← Book details My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 44

Sashe 22

My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sosai nasihar ta rinqa shigarta hadi da tsoro wannan miyagun kalmomi na Ni'imah akanta sunfi komai gigita duniyarta sun jima sosai Saida Fulani Innah ta shigo ita da Karimah sannan suka fita tana kuka tana rirriqesu sukadai samu suka tsere Haj Karimah ya ce ga hajiya Kaltume Amma batayo halinta ba tanada sanyi da sauqin hali hakan tasa sukafi dasawa da Ja'afar komai daya shafeshi baya boye Mata tana gaba gaba a cikin kowanne lamari nasa yanzun ma shine ya tasosu takanas yace su shiryata su tafi da ita gdanta bikin ma an gamashi ayi dinner gobe.
Suma nasihar suka rinqa yi Mata hade da rarrashi shikenan dai da gaske ta tabbata matarsa duk wani tsuminta da dabararta ya qare batada wani katabus kowa kalmarsa daya ta cire mgnr aminci ya riga ya rusata itama Ni'imah tayi watsi dashi ta rungume mijinta su zauna lfy, shiri sukayi Mata sosai na amaren gaske Basu gama mataba sai goma da rabi suka kamo hannunta suka fito tuni mota tayi ready kawai shiga sukayi sukadau hanyar martaba Estate suna zuwa sukayi parking suka fito da ita tanata gunjin kukanta Ammi da Abba suna fado Mata shikenan ta rabu dasu ta dawo cikin wata rudaddiyar rayuwa mara tsarin bawa zuciya farin ciki shikenan qurunqus ta tabbata kishiyar aminiyarta aminiyar da take ganin duk abinda duniya zatace bazata iya rabuwa da itaba sai gashi cikin sauqi kaidin namiji ya farraqasu har tana neman rayuwarta wani sabon kuka ya sake qwace Mata lkcn da aka haura da ita saman aka bude wani daki aka shigar da ita tare da yimata matsugunni saman wani tattausan kilishi basuyi Mata sallama ba saboda sunsan sallamar qarin tashin hankalinta zasuyi suna fitowa motar su Ni'imah na shigowa ita da wata yar yayar hajiya Sahura da tun dacan ma batason alaqar Ni'imah da Rafi'ah sunayin parking sukuma suna fita shima motarsa tana shigowa Samiha ce taja Ni'imah suka shiga ciki tana ciccijewa tana cewa “yanzu fah gurinta zai tafi ko yanzu da ita zai kwana...."

Rufe Mata baki tayi tace “ke kincika zafafawa abinda bazaije ko inaba kwana nawane amaryar maye a gabanki fah Mom tayi waya da boka na gangare yace zaiyi iyakar yinss yaga wani abu bai shiga tsakaninsu ba kuma kinsan zaiyi" ajiyar zuciya ta sauke daidai lkcn daya shigo tabisa da kallo fuskarsa babu alamun fara'a ya ajiye Mata leda ya haura sama ya jima sosai sannan ya fito ya sake wucceta har yaje bakin qofa yace “good night" wani malolo taji ya taso Mata amma data tuna tsiyar da suka kitsa sai tayi murmushi kawai ta miqe ta haura saman.
Kwanciya tayi tana saqawa da warwara inda shikuma yana fita ya bude motarsa ya dauki kayan daya siyowa amarya ya nufi bangaren gabansa har faduwa yakeyi tujarar Ni'imah bata tsoratashi kamar ta Rafi'ah itan akwai mugun kwarjini budewa yayi da addu'a ya shigà ya tsaya yana qarewa parlourn kallo yayi wani kyau an qara qawatashi sosai yaja numfashi ya haura saman kamar bangaren Ni'imah shima daki biyune a saman sai parlour qasa Kuma daki daya da kitchen da dinning area dakina biyu ya bude ya shiga ya hangeta zaune ta hade Kai da gwiwa tanata shassheqar kuka ya jima akanta yana qare Mata kallo kafin ya ajiye kayan hannunsa ya sanya hannun nasa cikin faduwar gaba ya dago fuskarta gabadaya kwalliyar dake fuskarta ta dame da hawaye yaja ajiyar zuciya yace.
“Kiyiwa Allah ki daina kukannan haka hukuncin Allah ya riga ya tabbata Rafi'ah wai ya kukeso nayine nikam?" Jan zuciya tayi ya sake gyara zamansa ya qara tallafo kanta yana me share Mata hawayen da hannunsa yace “a qa'ida tashi zakiyi muje muyi sallah mu godewa Allah duk da nasan baki murna ni inayi Amma shi aure ko bakaso rahamane da yakamata ka godewa Allah idan ya nuna maka ranar"

Da dabara yajata ta miqe sukayo alwala yajasu sukayi sallah raka'a hudu ya miqa hannu zai Kama kanta ta janye Murmushi yayi ya sake matsarta ya Kama kan nata da qarfi ya farayi Mata addu'a ya jima yanayi kafin ya gyara zamansa ya janyota jikinsa qamshinta da dumin jikinta yana ratsa nashi yanajin wata nutsuwa me gudana tana shigarsa wata qaqqarfar ajiyar zuciya ta sauke ya dago fuskarta da sauri yana mamakin dalilin tata ajiyar zuciyar cikin sanyin muryar da bata taba sanin ya mallaka ba yace “nayi Miki tanadin farin ciki dimun da'iman dawa'un My Luv don Allah ki bani hadin Kai kada ki biyewa mutane masuja da hukuncin Ubangiji inasonki zanyi hqr da komai naki kema kiyi hqr da mijinki kinji?"
Lumshe idonta tayi tanajin zagawar hannunsa a bayanta ya sauke ajiyar zuciya ya janyeta yace tashi kije kitchen ki daukomin flat na baki abinci" sunkuyar da kanta tayi yayi murmushin gefen baki yace “af sorry fah Ashe yau aikin nawane karki damu zanyi Miki komai idan kinaso har bacci ma ni zansaki kedin special ce" yana wannan mgnr ya dawo bayan ya kulle bangaren gabadaya yazo ya juye abinda yazo dashi daqyar da takurawa ya matsa mata taci hanta Tasha lemo yace “kije kiyi wanka kiyi brush inajin bacci sosai yau kunbani ciwon kai?" Batayi Masa gardama ba saboda tuna abinda ya faru dazu ta shiga bathroom din tayi brush tayi wanka ta dauro towel ta zuro alqabbarta lkcn data fito a tsaye ta tarar dashi da wata matsiyaciyar rigar bacci a hannunsa yana juyawa.

Matsawa yayi ya ajiyeta ya sanya hannu ya cirenta alqabbar ya ajiye ya Kama towel din zai cire ta riqe da sauri yaja numfashi ya miqa Mata rigar ya nuna Mata mayukan da ya fito dasu da turaruka yace “ki tabbatar kin gama kafin nazo duk abinda bakiyi ba na fito to saidai a hadu gaba bana jira idan zan kwanta" bai tsumayi amss ba ya shige bathroom din ta dauki rigar ta juyata tayi Mata kyau Amma duk rashin kunyarta bazata sata ta kwanta a daki gata gashi ba mayukan ta shafa ta fesa turarukan ta Koma kawai ta zauna ya fito ya dubeta cike da takaici gata dai kamar wayayya Amma bulkuma ce.
Baice Mata qala ba ya shiga shiryawa bayan ya gama yakai hannu ya kashe hasken ya kunna qaramin haske ya matso gabanta batare da tajishi ba ita bacci ma takeyi a zaune kawai saiji tayi yayi sama da ita ta fara zillewa tare da bude baki zatayi Masa kuka yayi saurin dora bakinsa a natan ya rufeta ruf a gadon tare da zame towel din yaja musu bargo kuka ta rinqayi masa tana gunji tanayi masa magiya..........

_Vote_
_Comments_
_Share_
_Please_

*_Ummuh Hairan_*

*_Wattpad-realfauzahtasiu_*

*_27-28_*

_____________________________
_____________________________

Daqyar da dabara saboda bayason wahalar da ita ya samu ya cimma burinsa ya saki wata ajiyar zuciya tare da dakatawa duk da dama bai yarda da mgnr su Barebari ba Amma zuciyarsa ta danyi dar saboda yasan abokin damo guza tabbas idan ta kasance aminiyar Ni'imah to komai zata iya faruwa amma sai gashi ya sameta asalin Varging duk da itama Ni'imah ya sameta da budurcinta Amma baikai qualityn na Rafi'ah ba duk masifarsa bai iya shigarta gabadaya a wannan dare ba kamar yanda ya shigi Ni'imah a daren farko.
Wani tausayinta ne ya kamashi jin yanda take kuka tana jujjuya kai tana Kiran iyayenta, ji yayi bazai iya cigababa sarai ya fahimci ba qaramar wahala zasusha ba daga ita harshi gata itanma Masha Allah akwai dauriya amma wannan abun yafi gaban dauriya saidai dabara, janye jikinsa ya farayi a hankali ya koma ya kwanta a gefenta yanajin sinadirun qaunarta yana qara zagaye duk wani bangare na jikinsa a hankali ya janyota jikinsa lkcn da wasu hawaye suka zubo masa ya rungumeta tare da hura Mata iskar bakinsa a kunnenta da haka bacci yayi ram da ita.

Ya dade yana kallonta ita komanta me kyaune yana godewa Allah da yayisa cikin mutane masu saa yasan aurenshi da ita ba qarfinsa ko isarsa bace kawai lucky ne da yake dashi a rayuwarsa da wannan bacci ya daukeshi shima, Kiran farko ta farka tajita tsam a jikinsa ta rinqa motsawa har ya tashi bai bude idonsa ba sai sakarta da yayi ta zura qafafunta qasa ta taka saiji tayi wani zugi ya ratsa qasanta ta cije ta miqa hannu ta dauko kayanta ta daura zanin a qirjinta ta rinqabin bango ta samu ta shiga bathroom din tayi wanka ta tsaftace jikinta tanajin zafi idan takai hannunta gurin hakadai ta gama ta dauro alwala ta fito.
Wardrobe ta bude wani sanyin dadi ya shigeta ganin kayanta a jere a ciki ta zaro doguwar riga da hijjab tasa ta shimfida sallaya ta tayar da sallah raka'atainul fajri tayi ta zauna tana istigfari ta yarda cewa istigfari shine mabudin dukkan wani alkhairi na duniya saboda shine abunda yake goge maka duk wani zunubinka ya kusantaka da Allah salin alin.
Chapter 22 · 0% Book details