← Book details My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 44

Sashe 43

My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamaki ne ya cika Jamal ya miqe yana riqe da hannun Mahir ya matso gabanta ya tsugunna Alh Hashim ya miqe ya fice, ajiyar zuciya yayi yace “da farko nayi Miki kallon tuhuma dana sani Amma dana tuna wasu abubuwa saina cire tunanin komai araina nasa a zuciyata Kama biyu kikeyi min tabbas hakane Rafi'an Prince ta mutu kwana biyu da haukacewarta an samo gawarta data babienta a dajin Dambuwa Kuma ke ance Mijinki mutuwa yayi so karna jaki da nisa My Raf inasonki Kuma aurenki na daura dambar yi duk da kasancewata saurayi hakan bai dameni ba domin sunnah zan raya ma'aiki shine yayi mana nuni da hakan zan aureki Rafi'ah da gaske wlh tun jiya na afka ki bani hadin Kai bada sauri ba mu fahimci juna ke nifa idan kika amince dani zaki aureni gobe zantada hankalin Azare baki dayanta sai an dauramin aure dake...."
Wani Abu taji ya caki qirjinta da yasata dafewa tace “azare! Azare!! Azare!!! Kamar na tabajin sunan?" Dariya yayi yace “ya Kama babie kina qasar Hausa kice bakisan Azare ba ni dan sarautar Azare ne mahaifina shine sarkin Azare yayana daya namiji yana Canada shekara guda bashida lfy saidai yaji sauqi idan bege da shauqin rashin matarsa da dansa ya motsa Masa Kuma yayi kamar ba zaiyi raiba Ina tausaya masa sosai har kuka nakeyi Masa saboda magauta sun sashi a gaba kawai don ya kasance me jiran gado shi kansa anso haukatashi Allah Bai nufaba sai aka sa Masa tsanar qasar Nan gabadaya wannan dalilin yasashi komawa Canada dazama Amma dukiyarsa duka tana Nigeria duk wata jaha dake arewacin Nigeria idan kika shigeta zakiga R&J pharmacy mallakinsa ne sunansa ne da sunan matarsa marigayiya Rafi'ah....."

_Comments_
_Share_
_Vote_

*_Ummuh Hairan_*
[2/2, 6:28 PM] Real Oum Hairan: I think you'd like this story: "MY BESTIE'S HUSBAND" by realfauzahtasiu on Wattpad https://www.wattpad.com/story/252522858?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create_preview&wp_uname=realfauzahtasiu&wp_originator=YZa%2Bnq8Gv74dk%2Br3fmroHt2fOS%2BrJAgPESvojabuR6mlrCBKlGcg1k%2FY8%2FEhPI0MmEXId7KOWuX%2F9qb4sodRsV9pyRkdk1Kk%2Bbe1YCuenDmpizIAObNjZFqoveTxmA0%2B

*_Mbh_*

*_Ummuh Hairan_*

*_Wattpad-realfauzahtasiu_*

*_Telegram Link_*
👇🏻
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7

*_53-54_*

_____________________________
_____________________________

Shiru tayi batare da tace masa komai ba ya zuba Mata ido yana jiran tace Amma taqi cewa sai ya miqe yace “kiyi tunani akan manufata ta alkhairi ce gareki dani baki daya idan kin yanke hukunci zan kiraki sai naji ya ake ciki saboda nasan mataki na gaba" tabe baki tayi ta miqe itama yabita da kallon mamaki tunda yake baitaba ganin birkitacciyar mace irinta ba tama saurareshi din babu dama.
Qwafa yayi daidai lkcn da Alh Hisham ya shigo suka qara gaisawa yace “yadai ta amince kuwa?" Murmushi yayi yace “aa batama cemin komai ba inaga barinta zanyi ta nutsu tukunna saita yanke hukunci" numfashi Alh Hashim ya furzar yace “haka takewa kowa bazatace maka komai ba saidai kawai zan baka dama ka turo magabatanka ayi mgn inaganin hakan zaisa ta samu nutsuwa"

Kallonsa yayi da sauri yace “da gaske?" Murmushi yayi yace “eh da gaske mana" hamdala yayi yace “Amma naji dadi sosai gobe kuwa zan tafi Azare zan sanar da Mai martaba abinda ke faruwa idan ya amince jibi ma zamuzo"
Jinjina Kai Alh Hashim yayi suka fita ya rakashi har gurin motarsa cike da kulawa inda yabar shirgin sha Tara ta arziqin daya hadowa mahir sun jima suna tattaunawa sannan sukayi sallama ya tafi Alh Hashim yana komawa gida ya Kira rafi'ah balbaleta da fada yayi abinda Bai tabayi Mata ba yana tuhumarta dalilin wulaqanta Jamal.

Hawaye ta rinqa sharewa tsayin lkc yana fadan nasa kafin ya sauko ya zauna yanayi Mata nasiha taci gaba da matsar hawayenta kamar tana daukar abinda yake cewa, Saida ya dakata sannan ta dago tace “bazanyi jayayya da abinda ka zartar ba Amma inason ki fahimceni wlh bansan komai game dani ba inaji a jikina Ni matar aurece Amma bana iya tuna komai so kuyi hqr ki qyaleni na rayu a haka har zuwa lkcn da Allah zai kawomin qarshen matsala ta tabbas akwai wani Abu da kullum zuciyata ke qoqarin tunawa ta kasa"
Shiru yayi na dogon lkc Itakam Allah yayi Mata baiwar saita kalami idan ya biyeta bazasu tsinanawa rayuwarta abin arziqi ba dubanta yayi yace “amma da sharadin zaki daina fita ko Ina don na gaji da mazan dakemin sinturi a gidana" saurin daga Kai tayi tace “na amince da hakan" dariya ma taso ta bashi saidai ya dake ya tashi ya shige ciki miqewa tayi ta shige ciki ta Kama danta suka kwanta ranar kwana tayi bata rintsaba ta takurawa kwanyarta son tuno abinda ya goge a cikinta hakan yake haifar Mata da matsanancin ciwon kai.

Kwanaki suka rinqa tafiya cike da abubuwa masu rikitarwa duk yanda Jamal yaso ta bashi hadin Kai taqi yaje ya samu Mai martaba da maganar auren shine yace masa ya fara samun soyayyar yarinyar tukunna gashi abinda yake tunanin bamai wahala bane yayi masa wahalar samu, duk da bata bashi damar soyayya ba Amma tana sakin jiki dashi suyi hira.
Abinka da abinnan da hausawa suke cewa me da Wawa soyayyar da yake nunawa Mahir tasa takejinsa a jikinta idan yaga haka yakan dauka fara sonsa tayi Amma da yayi mgn sai tace itafa uban danta kawai takeso bayanshi bata ra'ayin kowanne namiji a duniyaWannan kalma na Sosa zuciyar Jamal saidai bashida wata madafa shi s hakanma dadi yakeji duk da ya zurma da yawa yakan taushi zuciyarsa akam ta sassauta Masa kar yaje yayi saukon bukukuwa ya Gina zuciyarsa da qaunarta Rana daya ta juyansa baya Da wannan tunanin yake ragewa kansa shauqi game da ita

Al'amarin Ja'afar kuwa tunda Rafi'ah ta Bata ya shiga kwale²n masifa tun suna sakaran ji ko ganinta har suka fara fidda rai tsayin wata guda shikam yaqi lfy kullum cikin faduwar gaba da ciwon qirji yake, dadin dadawa Ni'imah da taketa qoqarin dole wai ita saita gogensa tunanin matarsa da dansa yakanyi Mata kashedi me qarfi game da hakan saidai taqiji wannan yasa suka rinqa samun sabani idan taje ta isheshi da mita wani lkcn idan takaici ya isheshi ya ware qwanji yayi Mata mugun duka ranar saidai ta kwana a bangaren Hajiya Fatsum.
Ana haka watarana ya zaneta cikin dare tazo ta isheshi aikuwa ba arziqi ta gudu bangaren Hajiya Fatsum tana kuka anan hajiyan take fada Mata tayi hqr bayin kansa bane aljani sukasa ya cire masa tunanin Rafi'ah sannan ya batar dashi shine suketa fada da zuciyarsa da aljanin idan ya ciks takurawa ma haukacewa zaiyi shima, suna tsaka da wannan tattaunawa kawai sukaga wani jan haske ya keto bango ya nufosu gadan gadan take suka watse suka rinqa tsere Amma Saida ya cimma Hajiya Fatsum kawai saiji sukayi ta fasa qara ta fadi qasa Tim tundaga wannan Rana ta zama kamar mutum mutumin babu motsi babu magana babu komai a wannan ranar ne Kuma bakin Rafi'ah ya bude,

Sosai hankalin kowa ya tashi Amma banda Ja'afar da ya fara susucewa kullum cikin hada kaya yake ana riqeshi zaibar gari wata Rana da bazata goge ba cikin tarihin rayuwarsa yana kwance da dare kawai saiji yayi an qwala mass Kira ya miqe a firgice saijin murya yayi ana cewa dashi "Canada ka tafi Canada matarka da danka sunacan zaka ishesu acan"
Aikuwa batare da tunanin komai ba ya miqe cike da farin ciki ya dauki passport dinsa da master card dinsa da wasu takardunsa masu muhimmanci ya sace jikids qafa ya fice ta bsyan gdan saboda masifa ma ta katanga ya haura Hajiya Kaltume tana kallonsa tayi dariya tace “shege da kace bakaji ya tafi inda ajalinsa yake" tunda ya fita bai tsaya a ko inaba sai a inda zaiyi Visa ta tafiya kudi ya saki sosai akan cewa shifa tafiyar gobe gobe yakeso sunyi iyakar bakin qoqarinsu suka sama masa ta jibi daqyar ya hqr ya karba ya fice ya nemi masauki ya qarasa kwana washegari kuwa kashe wayarsa yayi Bai budeta ba Saida ya sauka a Canada ya nemi mazauni ya huta sannan ya bazama gari neman farin cikinsa duk Wanda yagani indai baqar fatane saiya tambayeshi inda zaiga Rafi'ah a qarshe ma mutane sukamai dashi mahaukaci kwana da kwanaki yana bilayi daganan zuwa nan a kwana na sha biyar ne aka kirashi a waya ake fada masa anga gawar Rafi'ah da danta a jejin Dambuwa daga tsaye ya yanke jiki ya fadi shine har yau Bai qara lfy ba.

Jamal ne ya biyosa yake jinyarsa kwanansa ashirin yaji sauqi sauqi aikuwa a ranar ya turawa da Ni'imah saqon sakinta uku harda qarawa da cewa “dama Ina zaune dakene arziqin Rafi'ah tunda na rasata kema dole kibarni nayi rayuwata ni kadai ki nemi miji kiyi aure Ja'afar na Rafi'ah ne ta mutu ta barni zan jira ranar mutuwata mu hade da ita a darussalam" wannan saqo ya rikita Ni'imah ta rinqa kwarara ihu an dauka na iskanci ne Ashe qaiqayine ya dawo kan masheqiya tun ana daukan abin yanzu anjima har Abu ya tatura ta fara surutan tonan asirin kansu tashin hankalin da kowa ya shiga ba kadan bane aka rinqa Allah wadarai da halinsu.
Daqyar Abba ya rarrashi daddy Ni'imah ta koma gdansa Yana tur da Allah wadarai da halinta ita da uwarta aka rinqayi mata magani amma Babu sauqi Abu sai gaba yakeyi dole sai daki aka ware Mata aka rinqa Kiran malamai sunsyi Mata ruqiyya aljani kuwa yaci laya akan bazai barta ba tunda Rafi'ah tafi qarfinsa ai dama Saida sukayi sharadi shi baya zama hakanan batare da ya kada wani juji ba sukace sunji sun gani saboda haka Babu inda zashi Abu kamar wasa Abu sai gaba yakeyi takai tana tsigar gashin jikinta da kanta tana cinyewa kusan shekararta guda a haka sannan aka samu daqyar wani malami ya rabasu Amma me yana barinta ya koma kan Hajiya Fatsum.
Tashin hankali Ashe ga inda ake hauka can tuburan rawa da juyi takeyi tana yagar jikinta tunda akayi katari ta falle daga gdan sarautar har yau baaji duriyarta ba, inda Ni'imah take cikin tsananin nadama mabayyaniya son zuciya da zugar jahilan iyaye takaita ta baro gashi tayi uku babu babu mijin da take hauka akanshi babu aminiyarta babu auren Kuma babu mutunci da qima saima tarin tsana da qyamata da take fuskanta gurin mutane.
Chapter 43 · 0% Book details