← Book details My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 44

Sashe 33

My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lkcn daya shigeta ne abubuwa suka rinqa canzawa shi ba dadi take wani samu na musamman ba saboda itan ko maganin Mata bata iya kadawa Tasha ba sai aukin turaren asiri Amma sai yaji yanajin wani shauqi hakadai sukayi suka gama tun kafin su gama ta fara tureshi sabanin Rafi'ah da take qara riqeshi tana dago jikinta sosai yanda zai samu nutsuwa,
Ranar tare sukayi wanka yanata rawar jiki akanta ta cika da mamakin aikin boka Koda yayi sallah cewa yayi ta shirya suje su dubo Rafi'ah batayi musu ba saboda tanason ganin qwal uwar daka fita sukayi anata yauqi da yatsina ita me miji aka shiga mota suka nufi asibitin yana riqe da hannunta suka tura qofar dakin suka shiga,
Lkcn Rafi'ah ta tashi Hajiya Innah ta hada Mata shayi tana Bata suka shigo ta dago kanta idanunta ya fada kansu babu kunyar Hajiya Innah Ni'imah qara shigesa takeyi wai ita me miji shikuma sai wani binta yake murmushi Rafi'ah tayi cikin sanyin muryarta tace “sannunku da zuwa Best Ashe tafiya kayi dazun dana farka nake tambayar Innah kana Ina...." Kafin ta rufe baki ya taso da bala'i “to zama kikeso nayi nayi gadinki saboda ga asararre mara aikinyi hakanma banyi Miki ba dana Nemo Innah ta zauna a gurinki ke wacce irin mara tunani ce daga dawowarmu kin fara cuta saboda kinibibi kada na samu lkcn iyali na ke nifa baayimin iskanci kinsan cin mutuncinki ba wahala zaimin ba ba ciki ba ko bayane dake shashasha kawai....."

_More Comments_
_More Typing_

*_Ummuh Hairan_*

*_39-40_*

_____________________________
_____________________________

Juyawa yayi fuuuu ya fice a fusace sai huci yakeyi inda suka kalli juna da Ni'imah Ni'imah tayi Mata murmushin mugunta tabi bayansa da sauri a jikin mota ta tarar dashi yanata huci ya bude Mata ta shiga shima ya shiga yaja suka fice daga asibitin sukabae Rafi'ah da sanyin jiki da faduwar gaba, sunan Allah ta rinqa ambato a hankali taji Hajiya Innah ta dafata tace.
“Ina mamakin zafin zuciyar Baban Innah shi komai nashi na fada ne ko meye abin bacin rai cikin kalaman ki sai naga kulawa ce da nuna damuwa da abokin rayuwa tasa kika damu da rashin nasa a kusa Koda yake wani abun sai anayiwa rayuwa uzuri kiyi hqr iya wuya kedin dai kece"
Sosai ta rinqa rarrashinta murmushi tayi tace “karki damu Hajiya nasan halinsa yanzu haka wani abun ne ya bata masa rai nasan fushinsa baya jimawa zuwa anjima zai sauko" ajiyar zuciya Hajiya Innah tayi sukaci gaba da tattaunawa saida tasan yanda tayi taga Rafi'ah batabar damuwar abin a ranta ba ranar a asibitin suka kwana saboda jinin da akasa Mata da magrib bai qare ba sai cikin dare.

Washegari har Tara baizoba aka sallamesu Hajiya Innah ta dauki waya ta kirasa ya daga suka gaisa ya tambayeta me jiki tace “da sauqi dama sàllamarmu akayi shine mukace ko zakazo ka daukemu" Shiru yayi na dan lkc sannan ya dago yace “aa Hajiya kawai bari na turo driver yazo ya daukeku ku wucce can fada kawai ni na danje unguwa ne idan na dawo zanzo" bataja mgnr ba ta kashe wayar ta miqe ta fara hada kayan lkcn da drivern yazo ta gama hadawa suka fita suka tafi suna Isa yana shigowa gidan ya tsaya jikin motarsa suka fito duk munafukai suna jira suka abinda zai faru qarasowa yayi ya rusuna suka gaisa da Hajiya Innah ya dago ya zuba idonsa akanta tayi wani haske ta qara ramewa yaja numfashi ya dubeta yace “ya jikin naki?"
Sunkuyar da Kai tayi tace “da sauqi" fasali ya sake ja yace ”nasa an qara gyara can bangaren muje na rakaki" kallon Hajiya Innah tayi idonta ya ciko da ruwa tayi saurin girgiza Mata Kai dole tasa ta hadiye kukan, taimako daya da Allah yayi mata tsakaninsu da Hajiya Innah babu nisa hakan tasa suka taka da qafa ya bude qofar shiga part din ya shiga itama ta shiga da Bismillah tana qarewa bangaren kallo tun daga waje zakasan ya kashe mazan kudi wajen gyarashi.
Yana tafe tana biye dashi a baya har suka shiga ya bude qofar parlourn ya shiga itama ta shiga ya mayar da qofar ya rufe ya juyo ya zubanta ido itanma shi take kallo fuskarsa a daure take sosai hakan ya tabbatar mata da babu wargi, rabashi tayi zata wucce ya riqo hannunta ta tsaya cik matsowa yayi ya riqo qugunta yana jan numfashi ya matsota sosai yace “meye yake damunki ne?" Dagowa tayi da mamaki so take tayi mgn Saidai yanda ya kafeta da ido yasa ta kasa furta komai sakinta yayi ya sanya hannu a aljihunsa ya zaro kudi masu kauri ya miqa mata yace “ki riqe saboda tsaro ki kula da kanki"

Juyawa yayi ya fice tabisa da kallo yaja Mata qofar ya rufe itakuma ta taka taje ta murda Mata key ta nufi step din shiga dakin ba bene bane Amma an daga dakunan sun danyi sama sabanin babban parlourn da take a qasa nan din ma akwai parlour Amma baida girma sosai kujera daya ce doguwa sai wani qaton kilishi 24 pillow sai TV da dispenser sai manyan flowers da aka qara qawata parlourn dashi gefe Kuma akwai qaramin dinning table me kujera biyu.
Tsarin wannan parlour yayiwa Rafi'ah tayi ajiyar zuciya ta bude daki daki daya ta shiga shima an gyarashi sosai gadone na alfarma aka saka komai yaji taja fasali ta zube kudin daya Bata ta fara rage kayanta ta fada wanka ta jima tana wankan tanajin dadin ruwan kafin ta fito ta shafa mai ta bude wardrobe din kayanta ne jere reras ta dauko wasu masu sauqin nauyi tasa ta kwanta tana hutawa ta Jima a kwance tana tunanin abubuwa da yawa sannan taji ana taba qofar ta miqe a gajiye ta fito parlourn tana tambayar waye.

Amsa Mata akayi da cewa “nice Rafi'ah Ashe kun dawo to sannu kinji" jin an ambaci sunanta yasata budewa batasanta a zahiri ba domin bata taba ganinta ba ko lkcn da aka kaita bangaren fuskarta a rufe take, Hajiya Kaltume ce ta kawar da shirun da shiga parlourn tace “tubarkallah Masha Allah guri yayi kyau to ai haka yafi Amma da duk ya debeku ya tareku guri guda don shirme musamman ma ke da kike buqatar kulawa yanzu sannu kinji"
Sunkuyar dakai tayi ta durqushe da niyyar gaisheta tayi saurin Dagota da cewa “subhanallah kula kada kiyi barna haba yarnan keda ba lfy ta isheki ba ai bakya tsugunna ba zauna abinki ni uwarki ce banason ki takurawa kanki da jikana" tana mgnr tana zaunar da ita a kujera tace “to ya jikin jiya munji mugun labari Koda yake Allah ya taqaita wahala

A kunyace ta amsa Hajiya Kursum ta rinqa janta da Hira harda guzurin agwalumarta ta kawo Mata ta miqa Mata tace “kinsan abinki da me wannan Abu da son tsami tsami shiyasa na bayar aka siyo miki" kamar tayiwa Rafi'ah kyautar aljanna haka taji sukayita yar hirarsu tanata nuna kulawarta tare da bata shawarwari kamar gaske, shigowar Hajiya Innah ne yasata miqewa suka kalli juna Hajiya Kaltume ta harari Hajiya Innah tace “to Rafi'ah ki kula da kanki kinsan gdan namu gidan yawa bakasan cikin wani biyune ba saiya lashe maka kurwa" itadai bata tanka ba Hajiya Innah ta zauna tace “Allah ya kyauta" Shiru ce ta dan ratsa kafin Hajiya Innah ta bude kular da tazo da ita tace “dambu nayi Miki da fatan yakuwa ko Zaki iyaci naga duk kin fige wannan jika yana wahalarmin dake"
Kunyace ta kamata tayi murmushi tace “bantaba ganin yar da take kunyar uwata ba saike tashi kici abinci" xuba Mata tayi ta zage taci dambun sosai don ta dade tanason sa tunda ta samu ciki dashi da tuwo bata taba daina kwadayinsu ba sosai taci sauran ta ajiye tace taci da dare a kalamai baa bayyane ba Hajiya Innah take nunawa Rafi'ah tayi hankali da mutanen gdan fada gidan makirci ne kowa da abinda yake zuciyarsa, sosai ta shiga taitayinta ta qara Mata da cewa idan kadaici ya dameta tana gama abinda take ta taho bangarenta, Jinjina Kai tayi ta qara da cewa mutane da yawa sunayi maka dariya Amma basa qaunarka munafikinka yafi maqiyinka illa domin maqiyi baya zama kusa dakai balle ya samu damar cutar dakai Koda kuwa zai cuta maka saidai yabi ta gurin munafikinka da hausawa kance gadon bacciñka so kibi a sannu dariya ba so bace wata dariyar tafi sukar wuqa ciwo"
Maganganun sun shigeta ta nutsu kuwa tana nazarinsu lkcn da sukayi sallama tace “ki kulle bangarenki kiyi kwanciyarki ki huta surukarki batanan tace Damagaran balle kice zakije gaisheta" tana fita ta kulle part din ta shiga kitchen ta ajiye kayan abincin ta dawo ta dan gyara gurin data zauna
Chapter 33 · 0% Book details