← Book details My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 44

Sashe 19

My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Numfashi taja yace “Inasonki fiye da rayuwata My Bestie ki kasance cikin aminci 1:30am ki kwanta ki huta akwai ranar rashin baccin batazoba tukunna" kashe wayar yayi taja fasali tana jujjuya tata wayar a hannunta maganganunsa sunata yawo a kwanyarta lumshe idonta tayi tare da dauke qwallar idonta da kalamansa dana matarsa sune suka hadu suka saukar Mata da ciwon Kai ta miqe ta dauro alwala tayi sallar nafila raka'a hudu tayi addu'a me tsayi tana roqon Allah alkhairin wannan aure tace “Allah Kai kace mu roqeka zaka amsa mana tabbas baiwarka ta kasance me kawo duk wani damuwarta gareka Allah na nemi zabin miji a gurinka ka zabamin mijin aminiyata Allah Kai kace Aljannar wadanda sukayi soyayya dominka ma  dabance tabbas naso Ni'imah dominka nayi Mata duk wani Abu dominka, Allah Kaine masanin sirrin fili dana boye Kaine kadai kasan dalilin zabamin mijinta a matsayin mijina Ina roqonka ka haskamin alkhairin abin Allah ka ragemin qinsa a zuciyata idan kabarni naci gaba da qinsa bazanyi masa biyayya ba idan banyi Masa biyayya ba bazan hadu dakai cikin aminci ba"
Ta Jima tana hawaye tana fadawa Allah buqatunta tana cikin addu'ar ya kirata bata dagaba daya sake kiranta ta daga jin muryarta wasai yasashi jin dadi yace “kinyimin addu'a?" Shiru tayi yaja fasali yace “ina buqatar addu'arki matata ki roqamin Allah yabani ikon adalci tsakaninku kinji matata?" Jinjina Kai tayi tace “saida safe" wani dadi ya lullubeshi suka aje wayar ta cire rigar da tayi sallah da ita tasa na bacci ta haye gadon tare da addu'ar ta kwanta.

Washegari tunda ta tashi bata sauko qasan ba kuma bata bude wayarta ba har azahar tana sama dake litinin cema azumi takeyi sai a lkcn ta bude wayarta text din Ja'afar kusan biyar bata duba ba kiransa ya shigo kamar karta daga tadai danni zuciyarta ta daga suka gaisa ya tambayeta lfyrta  ta amsa yace “ina jiranki a waje" kashe wayarsa yayi tabi wayar da kallo tafi 20 minutes a zaune ya sake kiranta yace “sauri fah nakeyi kina batamin lkc"
A hassale tace “to ka tafi uzurinka mana ko na nemeka ne?" Ransa ne ya baci Ja'afar akwai baqar zuciya yace “ok" kawai ya kashe wayarsa ya juya motarsa ya fice zuciyarsa na tafasa unguwa zashi Amma wannan abinda tayi masa yasashi juyawa ya nufi Fam house nasu tun daga shigowarsa Hajiya fatsum take kallonsa yayi parking ya fito a fusace ya shiga bangaren nata domin tun safe tace tanason ganinsa bai samu fitowa ba sai yanzu yana shiga ta daukesa da mari ya tsaya cak tare da dago kansa a kasalce ya zuba Mata ido yana cije lebansa.
Shaqarsa tayi tace “nice na mareka magaji ko zaka ramane dan iska maci Amana kaikam kayi asara meye laifin yarinyar nan Ni'imah daga aurenku ko wata uku baku cikaba zakayi Mata kishiya kishiyarma aminiyarta wannan debabbiyar yarinyar yar gdan Haj Amina sangartacciya lalatacciya aini bansan lalacewarta takai haka ba wlh da ko zaka mutu bazaka aureta ba..."

Ji yayi daga bayansu an cafe da cewa “wlh Barebari fadawa kowa Shahararriyar yar iskace ta gaban kwatance duk ATBU babu Wanda bansanta ba ke qarewa ma fah Prettyn Lecturori akece mata duk wani lecture daya kwana ya tashi a ATBU yasanta ansha kamata da lectures......" Rintse idonsa yayi cikin qaraji yace “qaryane Dijah wlh qaryane Rafi'ah ba haka takeba Kuma ku tambayi Ni'imah tafi kowa sanin halinta....." Duka Haj Fatsum takaiwa bakinsa tace “Ni'iman ubanka da uban waye ya fadi wannan din tun jiya ta kirani ta fadamin na tashi jakada yaje yayomin bincike akai aka tabbatarmin saboda haka tun kafin ka gurbata zuri'arka ka sawwaqe Mata kowa ya Kama gabansa

Komawa yayi ya zauna jikinsa yana rawa sai huci yakeyi tsawa Hajiya fatsum ta daka masa tace “Mgn fah nake maka Magaji" iska ya furzar ya miqe yace “bazan iyaba" yana fadin haka ya fice da sauri suka bisa da kallo yana fita mota ya shiga ya nufi gdansa inda Salma da Dijah suka kalli mahaifiyarsu sukace “kinji fah Hajiya ai dama Hajiya Sahura ta fada sun tsafaceshi a kishi irin nasa wlh da qalau yàke da sai yayi abinda kikace kigafa yanda yake dakama mana tsawa dan tsoron nakima ya daina an cire mishi wlh idan kika sake rabaki zatayi dashi gabadaya kamar yanda ta rabashi da matarsa"
Dunqule hannu Hajiya Fatsum tayi ta daki tafin dayan hannunta tace “aa Basu isaba wlh Kaltume ma da take tsafi ta qyaleni ballesu dole ma su barmin dana ba mace na haifawa ba kaina na haifawa" mayafi ta figa tace “ku biyoni"  miqewa sukayi suka bita mota suka shiga driver yajasu suka fice Kai tsaye sukayiwa gdan Alh Nuhu tsinke lkcn Rafi'ah ta sauko tana kwance a parlourn saboda azumin baqar wahala yake bata Ammi tana gefenta tanayi Mata tsifar baqin dogon gashinta saiji sukayi an shigo ana dure duren ashariya da sauri Rafi'ah ta wuntsulo cikinsu babu Wanda ta sani har garama Dijah suna yanayi da Ja'afar saidai ita baqace a sanyaye ta dubesu tace “haba bayin Allah yada shigowa babu sallama kamar ba musulmi ba....."

Dauketa Hajiya Fatsum tayi da mari tace “kaji sabuwar mara kunya Koda yake kyayi ai nasamu lbrnki dana uwarki me daure miki gindin iskanci da bin maza an fake da karatun likitanci ana karuwanci ruwan jiki ya qare an sihircemin dana an liqa masa to bamaso bamason irin tsiya irin jaraba wannan kyaun dan macijin shine yake dada rudarsa to wlh bazamu kwashi jarfaba"
Rafi'ah sai jikinta ya dauki rawa ta rinqa ja da baya suka rinqa tujararsu da zage zage babu Wanda ya tankansu sun jima sunayi itadai sai tsumar jiki takeyi data zuci Wai karuwa an fake da karatun likitanci ana karuwanci wannan kalma ta girgizata tunda take bayan Ja'afar babu namijin daya taba riqe ko hannunta Amma gashi uwarsa tana kiranta karuwa, Ammi ma kalmomin sunyi Mata ciwo Amma bazata biye musu ba tasan duk sharrin Sahura ne miqewa tayi ta Kama hannun Rafi'ah tajata suka haye sama suka barsu a tsaye sai lkcn Aunty Raziqa ta miqe tace “ashe yan iskan da yawa kema kin haifi dan iska domin kuwa babu yanda zaayi idan shi nutsattse ne yayi sha'awar auren karuwa..." Aunty Murja ce ta katseta da cewa “wai dama wannan itace uwar Ja'afar din kayy Amma albasa batayi halin ruwa ba dan bai tsotsa a nonon uwaba karuwa kuwa saidai ki gani a dakinki" Suma ficewa sukayi daga parlourn suka barsu tsaye kamar dashe sun jima suna rarraba idanu sosai suka Raina kansu ashe Suma iyayen Rafi'ah ba faqirai bane sunma fi na Ni'imah Koda yake ita dama Haj Fatsum tasani baqin cikine ya hanata tunawa wani gwauron numfashi ta sauke tayi qwafa ta fice tana cewa “kunyi da yar halak indai nice na haifi Magaji wlh bazai zauna da wannan makirar mara kunyar yarinyar ba matarsa yar arziqi daya tilo ta isheshi..."

Tunda su Ammi suka shiga ciki take aikin rarrashin Rafi'ah ta sake botsarewa tanata kuka tana cewa wlh bazata zauna da Ja'afar ba ita bazata iya masifa ba kowansa masifaffe shima masifaffe ita bazata iya masifa ba bata sababa, duk yanda ammi take tunanin shawo kanta taqi shawuwa saima qara botsarewa da takeyi tana maimata “Wai nice karuwa Ammi wlh bazan iyaba ni bazan iya masifa ba"
Shikuwa gogan gdansa ya shiga yana shiga yaci karo da Ni'imah duk ta fashe komai na parlourn hatta show glass dinta bata bariba baiko saurareta ba ya haura saman ya bude wani daki dake kulle ya debo takardunsa ya fito har yaje bakin qofa ya tsaya yace “sannu da aiki Allah ya qara lfy" Bai jira cewarta ba ya zaro raffers na 100k ya ajiye Mata yayi gaba abinsa ya fice ya tare adaidaita ya fada masa inda zashi airport ya nufa ya hau jirgi sai birnin tarayyah gabadaya Bauchi tayi masa zafi.

Haka kwanaki suketa turawa a bangare ukun duka babu kwanciyar hankali hauka sosai Ni'imah takeyi duk wani Abu me amfani na gdanta ta lalatashi Yusrah ce tazo gdan taga yanda ta mayar dashi take ta fadawa Hajiya Sahura aikuwa tayo tattaki tazo ita da Hajiya Fatsum nan suka hauta da fada suna nuna Mata illar haukanta Hajiya Fatsum tace “ina mijin naku kwana bakwai banganshi ba?" Hawaye ta share tace “nima kwana bakwai bansashi a idona ba nikadai naketa haukana" murmushi Sahura tayi tace “ya hadaki da hawan ruwa ya tsallake ya tafi yabarki garama ki canza salon kishi wannan haukan bazaisa ki samu abinda kikeso ba"
Hajiya Fatsum taja numfashi tace “ni bantaba ganin jaraba irinta Magaji ba ita kanta Rafi'an ba son auren takeyi ba jiya Muhseen yakemin bayani ni saitama bani tausayi tun ranar da mukaje mukaci mutuncinta da iyayenta tanacan ana bala'i da ita akan ita saiya saketa bazata zauna dashi ba gashi Yama kashe wayoyinsa gabadaya duk neman duniya an kasa samunsa balle asan inda yake" hararar Hajiya Fatsum Ni'imah tayi tace “qarya takeyi munafukace wlh tanasonsa ni nasanta fiye da yanda uwarta tasanta inda batajin sonsa aranta da bai isama ya rabeta ba ranar fa da aka daura aurensu fah da ya dawo yayimin hawan qawara bayan ya gama cemin yayi itace ta tada masa da sha'awa wlh idanda batasonsa ko ystsanta bazai riqeba tujararriyace ta masifa akan abinda takeqi"
Chapter 19 · 0% Book details