← Book details My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 44

Sashe 41

My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shikam Alh Hashim gidansa ya nufa cike da fargaba yayi parking ya fito ya nufi cikin gidan rungume da Mahir a qirjinsa hadiman gdan sai kallonsa sukeyi da tsananin mamakin inda ubangidan nasu ya samo danyen jariri kafin ya Isa ciki har saqo ya ishe Hajiya Bari'ah cewar ga mijinta Nan dauke da abin al-ajabi hakan yasata saukowa daga saman ta zauna a qasa ya bude qofar ya shigo ya mayar ya rufe ya juyo sukayi ido hudu ta miqe da sauri qirjinta nabada wani daram.
Ya lura da yanayin data shiga shikuma sai yayi Mata murmushi ya zauna a kusa da ita ya bude fuskar Mahir ya dago ya dubeta yace “uwargida bani ruwa do Allah" jikinta a sanyaye ta nufi freezer ta bude ta sauko ruwa me Sanyi ya taba yace “yayi sanyi mara sanyi nakeso Mahir zanyiwa addu'a" batayi gardama ba ta sake daukowa da qaramin cup na glass ta rusuna ta bashi yaja ajiyar zuciya yayiwa yaron addu'a ya dago kansa ya guntsi ruwan a bakinsa ya hada Dana yaron ya rinqa basa a hankali Bai cire bakinsa ana yaron ba saida yaga ya shanye yayi hamdala yace “kinga wani kyakkyawan babe Bari'ah Yana burgeni sosai" numfashi tayi ta zauna qirjinta na dokawa tace “ina ka sameshi?" Murmushi yayi yace “ina ranar da naje Dambam karbo Miki magani to ranar Allah ya hadani da uwar yaron nan cikin wani mawuyacin hali abin tausayi da alamun sihiri akayi Mata aka kadota daga gdan mijin kinsanni da tausayi saina daukota muka taho nan har Nan gidan mun shigo fah nace ta fito kawai sai ta riqe ciki Ashe aiki akayi Mata aka cire wannan babien a cikinta Kuma aka samu azzaluman da suka haukatata hauka fah tuburan, so shine na dauketa muka tafi Gombe General Hospital anan aka rinqa kula da ita nikuma nasa malamai suka rinqa yimata addu'a har Ubangiji ya kawo sauqi yau yanzu haka ta farfado cikin hayyaci saidai fah ta manta kowa da komai sai danta kadai Babu abinda zata iya fada daya faru a baya"

Zuba Masa ido tayi ta kalleshi ta kalli yaron zuciyarta bata yarda da abinda ya fada Amma batason sanya Masa tuhuma da kanta zata tabbatar da abinda qawarta Rahila ta sanar da ita tagani a asibiti shirun nata ne yabashi damar cewa ki tsayar da zuciyarki Bari'ah bazan cutar dake ba kuma bantaba munafurtarki ba Am Baiwar Allan nan zatazo gidannan ta zauna kafin binciken da nasa akeyimin ya bincikomin inda danginta suke na sadasu da ita so ki nutsu don Allah ki taimaka Mata wajen kula da yaron nan ta dalilin taimakonta sai muma kiga Allah ya bamu namu"
Jinjina Kai tayi tana qara kallon Mahir zuciyarta na Bata cewa Raina Mata hankali Hashim yakeyi fah yaje yayiwa yar mutanen ciki ta haihu iyayenta sun koreta ya dauko zai kawo Mata gidanta ko Kuma auranta yayi a boye yayi Mata ciki shine yanzu yakeson hadasu saboda idanunta daya rufe har Kama taga Mahir da Hisham sunayiMiqewa tayi ta shigewarta dakinta ya bita da sauri yana kiranta don dama ya hasaso faruwan hakan Kiran duniya ta bude taqi budewa bayason Bata Mata saboda itadin amanarsa ce Amma akan wannan jahadin saidai tayi duk abinda zatayi Allah shine zai fitar dashi.

Ya Jima cikin tunanin abinda ya dace kafin ya juya ya sake ficewa ya koma asibitin lkcn Rafi'ah ta samu bacci ya zubanta ido yana kallonta a ransa yanajin ninkin tausayin ta damuwar loosing memories ai ba qaramin abu bane dole tana buqatar kulawa ta musamman sake fita yayi ya samu likitan ya nema Mata sallama suka sallamesu tare da dorata akan magunguna sannan ya koma da Nusaiba aka had a kayan suka tafi yanata zuba mata sannu suka shiga gidan tanata bin gdan da kallo tana son tuna tasan wani Abu kwatankwacinsa Amma ta kasa Kama hannunta yayi har cikin gdan bangaren da yass aka gyara Nan ya kaita ya kwantar da Mahir yace “ki huta sosai sosai zuwa anjima sai nazo nabaki magungunanki" zama tayi ya juya ya fice ita Kuma ta kwanta bacci ya sake dauketa har yanzu akwai baccin gajiya akanta.
Ranar kwana sukayi shida Bari'ah suna rigima kuka takeyi sosai wai yaci amanarta Babu wani taimako matarsa ce Rafi'ah saboda yaga Bata haihu ba shine yayi Mata wannan sakayyar yaso fahimtar da ita Amma taqi ganewa shikam da yaji haushi ya dawo parlour yayi kwanciyarrsa cikin dare yaji Mahir na kuka yaso ya qyaleshi amma yaji bazai iyaba saboda qaunar yaron yakeyi da gaske ya miqe ya bude qofar bangaren a parlour ya tarar da Rafi'ah tasa yaron a gaba itama sai kuka takeyi.

Mamaki ya kamashi yayi dariya shi baitaba ganin wannan rigima ba ki haifi da a cikinki Yana kuka maimakon ki rarrasheshi Wai sai kema kisashi a gaba ki Kama kuka karbarsa yayi ya zauna yana hura Masa kunne har yayi shiru ya koma bacci ita Kuma Bari'ah ta fitto ta nemansa bata gansa ba zuciya tabata yana dayan bangaren ta nufa a fusace ta bude ta shiga sai tayi turus ganinsa kwance a parlourn farko Mahir na qirjinsa suna baccinsu cikin kwanciyar hankali qwafa tayi ta juya ta fice ta kwana zaune tana kuka Wai ya tsallaketa ya tafi gurin shegen dansa.
Da asuba ya farka ya miqe ya kwankwasa dakin Rafi'ah da take zaune tana lazumi ta miqe ta bude ta karbi yaron tare da jinjinawa alamun godiya yayi Mata murmushi ya fice, yana fita masallaci ya nufa lkcn daya dawo ya tarar da Bari'ah ta hade kayanta a akwatu tanata kukan Wai anaci Mata mutunci duk yanda yake tunanin shawo kanta ta dadi ya kasa qarshe yace idan ta fita bai yafeba dole tayi hqr bata fitan ba Amma ko abinci ta rantse bazata rinqa bawa Rafi'ah ba bai wani damu ba hakanan ya amince kullum da kansa yake shigar kitchen yakewa Rafi'ah girki tea ne zai dafa Mata ya soya Mata qwai da duk wani Abu da yasan zata buqata har tayi sati uku a gidan lkcn tayi qwari sosai ta murje Amma Babu baki sai ido yanajin dadin yanda yaga ta saki jikinta dashi abu daya dake neman wargatsa lissafinsa shine yanda take mu'amalantarsa yayi Kama da tanayi masa kallon mijinta sannan taqi karbar sunansa Hisham kullum Ja'afar take kiransa

Yayi iyakar yinsa yaga ta gane ta kasa ganewa inda Bari'ah take qara samun hujja da yanda Rafi'ah take mu'amalantar mijin nata da Kuma irin son da yake nunawa Mahir kullum sai yayiwa Mahir shopping idan ya fita takanas Bari'ah da taga bashida niyyar saukowa ya sake Mata bayani tayi tattaki har gidan surukarta tana kuka ta fada Mata cewa Hisham ya kawo Mata mace gda ya ajiye Kuma harda ɗa a wata majiyar ma ance dansa ne yayi Mata ciki ta Haifa Masa shine iyayenta suka koreta shikuma ya aureta,
Sosai hankalin tsohuwar ya tashi duk da ta yarda da ingancin danta Amma mgnr Bari'ah abar dubawa ce dubanta tayi tace “kije zanzo anjima idan ya dawo" haka kuwa akayi da magariba ya dawo daga aiki yayi wanka ya zura doguwar rigarsa ya nufi bangaren da Rafi'ah take domin dauko dansa Mahir da ya qara kuɓulɓul dashi a parlour ya isheta tana sallah shikuma Mahir na kwance a kusa da ita yanata kallon sama yasa hannu ya daukesa ya zauna a kujera yana cillashi sama yaji an bude qofar an shigo ya dago da sauri sai yaga Hajiya Rakiya mahaifiyarsa ya shafa kansa tare da cewa “Ahhh Hajiya kece da daren nan?" Zubawa Rafi'ah ido tayi tana tunanin inda taso sanin fuskar yarinyar tana cewa “ashe haka ka zama Hashim dan shege a zuri'ar mu...." A gigice Rafi'ah ta dago ta dubi Hajiya Rakiya sai hawaye sharr a idanunta shima Hashim saurin kallon mahaifiyarsa yayi yace.
“Hajiya nasan cewa baki yanke hukunci da ka a mafi yawan lokuta ma baki amsar hujja saman yaqini wlh tallahi banida wata alaqa ta kusa da wannan baiwar Allan bayan taimako, Nan ya kwashe komai ya fada Mata tayi shiru tana nazarin kalamansa ita kanta Bari'ah sai jikinta yayi sanyi ya share qwallar idonsa yace “ke daga ganin nutsuwa da kamalar wannan baiwar Allan bata cancanci wofintarwa ba duk inda ahlinta suke sunanan suna haqilon nemanta jiya nabada hotonta a kafafen yada labarai da jaridu domin a cikitomin ahlinta ko Ubangiji zaisa a dace"

_Comment_
_Share_
_Vote_

*_Ummuh Hairan_*
[2/1, 7:44 PM] Real Oum Hairan: *_Mbh_*

*_Ummuh Hairan_*

*_Wattpad-realfauzahtasiu_*

*_Telegram Link_*
👇🏻
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7

*_51-52_*

_____________________________
_____________________________

Jinjina Kai Hajiya Rakiya tayi ta dubi Rafi'ah ta miqe ta Isa gabanta lkcn ta idar da sallah ta zauna kusa da ita ta Kama hannunta kuka takeyi sosai, cikin yanayi na tausayi Hajiya Rakiya tace “kiyi hqr kinji yata Allah yasan komai Kuma shine yakeda maganin komai" kwantar da kanta tayi a kafadarta ta sake rushewa da kuka cikin yanayin da batasan ya akayi ya wanzu ba ta bude bakinta da cikin watanni hudun baya iya furta komai tace.
“Wlh banida wata alaqa da Hisham a baya ne ma yakemin Kama da uban Dana Ja'afar amma yanzun ya daina...." Miqewa Hisham da bari'ah sukayi tare suka Isa gabanta yakai hannu zai tabata sai ya tuna da mgnrta uban danta Ja'afar tuni ya dawo nutsuwarsa yaja fasali yace “dama bakinki Yana mgn kikaqi yimin mgn tsayin wata hudu?" Cikin kuka tace “aa yaune naji Ina iya furta wasu kalmomin sannan inajin kamar inason tuno wani abu game Dani Amma na kasa don Allah wacece ni ya akayi nazo nan Kuma inane nan?"
Chapter 41 · 0% Book details