← Book details My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 44

Sashe 26

My Bestie's Husband Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wani tuquqi ne ya tasowa Ni'imah tayi kan Rafi'ah da sauri ta miqe tace “sorry I call you later" Dora wayar tayi saman TV stand ta jirayi qarasowarta tana zuwa ta kawo Mata duka ta kauce tana dariya tace “ni haba yarinya ai bazakiyi dani ba" wayarta ta Zara ta haye sama tana cewa idan kin gama ki rufemin na gaji bacci nake buqata" binta tayi da zagi tana wani Harbin iska batako waiwayo ba ta shige dakinta ta fada gado ta kwanta tana murmushi tana Jinjina haukan Ni'imah wai akan namiji take haukannan namiji ma irin Ja'afar Wanda a zaman da ta danyi dashi na kwana biyu ta fahimci shi ba mutum ne da ake burgeshi ba abinda yaga dama shi yakeyi.
Duk irin bugu da zage zagen da Ni'imah takeyi Rafi'ah bata tankata ba kuma bata bude ba dakanta ta gaji ta tafi tana kwance taji ya sake kiranta ta daga yace “meye ya hadaki da Ni'imah kikaje har part dinta kika zageta?" Abin ne ya daure Mata Kai tace “ni Kuma nida tunda ka tafi Ina kwance ko qasa ban sauka ba saida naji kamar ana tabamin qofa nace maka zan kiraka anjima" numfashi yaja kawai sai ta Kama shassheqar kuka abinda ya tashi hankalinsa kenan yace “to meye Kuma daga tambaya sai kuka" jan zuciya tayi tace “ni bansan meye ta tarewa duk wani wanda ya shafeka ba da baya sona nima fah bason aurennan nakeyi ba qarfa qarfa akayimin...."
Katseta yayi da cewa “kinga naji Ni dama tunda ta fada ban yarda ba kawai na kiraki ne don na gasqata ai daga yanayinki ma ansan ke bame fitina bace" jan zuciya tayi tace “to nidai banaso kajawa matarka kunne kada ta qara qoqarin hadani dakai idan wani abu takeji akaina tazo ta sameni zan iya sammata lkc a cikin lkcnka inka yarda" dariya yayi yace “bama na buqatar kowa ya shiga lkcna ya tsaya iyakar nawa ni daya"

Kashe wayar sukayi tayi murmushi tace “salon wasan zai canza dama aunty Bushira ta fadamin saina sawa idona kwallin rashin mutunci zanyi miki illah idan kika matsa Ni'imah badon mijin ba saidon ki gane kowa yanada tasa baiwar" tayi bacci sosai sannan ta  tashi  ta shiga kitchen ta fara shirya dinner ta bata lkc matuqa wajen shirya musu abincin lkcn data gama biyar saura ta fada bathroom ta dauki wankan susuta megida ta harde a parlourn tana kallo tana chat bai shigo gdanba sai bayan magrib ya jima akanta kafin ta ankara shima Saida ya zare wayarta a hannunta ta dago suka hada ido da Ni'imah dake shigowa bakinnan kamar cokali kawai saita qara fadada murmushinta ta miqe ta rungumeshi tare da lalubo bakinsa ta hada da nata ya tallafo bayanta yana sakin wani nishi me qarfi mutuwar tsaye Ni'imah tayi saboda abin yazo Mata a bazata kallonta Rafi'ah tayi ta daganta gira tare da janyewa daga jikinsa ta shafa sajensa tace “yau na yini da kewarka sai nakejina kamar marainiya ka tafi ka manta damu..."
Rufe Mata baki yayi yace “ah haba kiyi istigfari wlh kina Raina munje anguwa da Mai martaba ne dana dawo Kuma sai na wucce sama mana Visa me kika tanadar min?" Rufe idonta tayi tana yar qaramar dariyar kirsa tace “a..bin...da...ka...fis...." A rarrabe tayi mgnr ya kwashe da dariya yace “wayyoh dadi matata kina shagwabani wai dama haka kike wow! Allah na gde mak...."

Muryar Ni'imah yaji ta rushe da kuka tana cewa “Allah ya isana wlh Allah ya isana kirana kayi don ka wulaqantani a gaban wannan yar iskar matar tak..." Tsawa ya daka Mata yace “keyyyy ki iya bakinki...." Rufe masa baki Rafi'ah tayi tace “Haba ranka ya dade saurin fushi ai ba naka bane ay rarrashi take buqata" sakinsa tayi ta nufeta ta kamota tace “kekuwa rabin jiki kiyi hqr mana ai bamusan dakeba idona rufewa yake idan Ina tare da mijina shine sanyin ruhina salamar rayuwata am sorry please iso muyi dinner yau abinda nasan kinaso fiye da komai shi nayi mana kowa favorite dinki zaici yau a gdannan"Fusge hannunta tayi ta hankade Rafi'ah tace “dake da favorite din na hadaku naci bura ubanku ni zakiyiwa bariki kina kallona kina wani qara rungumarmin miji kina tsotsar bakinsa har kina dagamin gira kice wani baki ganni ba kaikuma kwallon munafiki sullutu sallamamme da aka wanke wani guri aka bashi ya shanye har wani qara shigewa kake jikinta to ka hadiyeta mana qarewar so da kewa munafiki mara adal...."

Hannu ya daga zai kwada Mata mari Rafi'ah tayi saurin riqe Hannunsa tace “Don Allah ka rinqa tausasa zuciyarka mijina ai namijin gaske baa sansa da fushi a gidaba idan kana fushi meye sauqinmu ne muda zamu rayu a qarqashinka please yi Mata uzurin nan daka saba da wankama nakeso na tayaka kayi nasan ka gaji Amma naga tumbinka ya sauka ba haka na saba ganinsa ba muje na ciyar dakai yanda zaifimin dadin shafawa" ta qarasa tana shafa tunbinsa murmushi yayi ya dagata cak ya direta a kujerar dinning din takaici ne da baqin cikin abinda bata taba tunani ba yasa Ni'imah juyawa zata fice har takai bakin qofa yace “dokace ba umarni ba kin saba taka dokata Ina qyaleki wannan bazanyi uzuri ga kowa ba"

Sumsum ta dawo taja kujera ta zauna Rafi'ah tai murmushi ta hadawa kowa abincin ta turawa kowa gabansa ta diba a cokali zatakai bakinta ya riqe tasan me yake nufi ta matso da kujerarta ta rinqa bashi tuwon Cous-Cous ne da miyar kubewa da yaji bandar kifi sai fatan doya da yaji hanta babu kunya Ni'imah da ganda tasata yiwa kanta horon yunwa ta zage ciki ta nadi tuwon tasha hadin lemon da Rafi'ah tayi musu na kankana ta miqe ta Kama hanya zata tafi Ja'afar yace “ki jira na gama na rakaki tunda cikinki ya dauka a qa'ida ma fah ba ita zatake girki ba ke zakikeyi mana tunda ita sabon hannu ce da wanne zataji saboda haka daga gobe zaki fara aikinki zuwa sati" ta hadiya iyakar hadiya wai tayi musu girki suci tab aikuwa zaayi zaman yunwa a gdan to ita da wanda zataci ma batason girkawa itace zata girkawa qarata biyu abinci tab zaayi bala'i kuwa" a tsaye ta tsaya taqi zama shima Kuma yaqi tashi saijan Rafi'ah yakeyi da hira itace taga tsaiwar tayi yawa tace “am dare yayi zata gaji da tsaiwa ka tashi ka rakata" juyowa yayi ya dubeta ta kumbura fuska yayi murmushi yace “wlh na manta dake a tsaye sorry muje na rakaki" miqewa yayi itama Rafi'ah ta miqe ta rakasu har bakin qofa tace “asuba ta gari Best...."
Wata uwar harara da yayi Mata tasata juyawa da sauri ta fara harhade kayanta sake gyara parlourn tayi ta kunna turaren wuta a burner ta haura saman shima ta sake Masa sabon gyara tayi alwalar isha tara harta wucce tayi isha tayi shirinta na kwanciya gabanta na faduwa batason nacinsa cikin saa daya shigo din shima bai wani takura Mata ba sukayi baccinsu salamun salamun washegari litinin ta roqeshi alfarmar zataje tayi C.A a school da farko cewa yayi bata isa fara yawo ba Saida yaga ta marairaice masa zatayi kuka sannan yace ta shirya yakaita suna fitowa Ni'imah ma tana fitowa da alamun fita zatayi iyakar son tuno abinda ya wucce dinsa yakasa tuna sanda ta tambayeshi fita Koda yake dama tunda aka fara mgnr aurensa da Rafi'ah bata tambayarsa zuwa unguwa saidai ya dawo ya tarar batanan.

Ya shirya Mata mugunta saboda haka ya nufeta da sauri yana zaro kudi a aljihunsa yace “Au na manta yau zanyi baqi daga Gombe ki bawa Yahaya kudi gasu ya siyo kifi nasan babushi a kitchen dinki wancan kin barsa ya lalace kiyi mana farfesu sannan kiyi mana tuwon alkama miyar kalkashi ki tabbatar kin gama kafin azahar zankai Rafi'ah makaranta May be tare zamu dawo da baqin"
Bai jira cewarta ba ya juya yana murmushi ya shige motarsa yaja har suka fita takasa motsawa tashin hankalinta yanda zatayi wannan wahalallan girkin daya sata ita tunda take a gidansu bata taba ganin anyi tuwon alkama ba Amma wai yau ita zatayisa harma da tagomashin miyar kalkashi ga gyaran kifi da kullum ta gyara sai yace bata iyaba gdanta yana qarni, zubewa tayi a gurin ta dora hannu aka tanaso ta zunduma ihu Amma ta kasa daqyar ta miqe kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta koma ciki ta rinqa zagaye parlourn tana tunanin ta inda zata fara kiran Hajiya Sahura ne ya shigo ta daga da sauri tace “ya munata jiranki boka yace dole sai kinzo aiki zaiyi yadda akeso ke Kuma kina bata Mana lkc" sai yanzu ta samu damar fashewa da kuka tace “Mom wannan dan gadon masifar ne ya hadani da aiki wai baqi zaiyi shine yace nayi masa tuwon alkama miyar kalkashi sannan nayi masa farfesun kifi harda cewa saina hada masa lemo don Allah ki turomin Marawiyyah nasan ta iya tunda girkinsu ne na yan qauye wlh idan banyi ba akwai matsala" Hajiya Fatsum ce ta karba tace
Chapter 26 · 0% Book details