← Book details Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 24

Sashe 5

Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

32
Gaba daya mun suke muna hira har Habiba tana
tambayata mace fa kema ki ka haifa ko? Nayi
murmushi ban yi magana ba, sai kawai naji Babana
yana cewa uh'uh hun, rabin da suka iya kenan, su sami
abin dadi su rufan mishi su rinka ci suna zare ido
suna gwalo.
Amma su su zauna ana su' dakunan auren sun
kasa mugun halin da aka koya musu ya hana su, gaba
daya zaman aure ya gagaresu, sun dawo min gida
sun z0 Sun zama min da:wasu munanan ya'yansu
masu kama da "ya'yan tanda.
Duk ku watse a nan ku bani wuri, yan jakar uba.
Gaba daya su da ya'yan nasu suka watse da gudu,
yuu suka shige dakin Mamna.
Ni kam duk da na sani da wuya kwarai in ga
Mama cikin wani hali da zai bani tausayi cikin sauri,
halin da ya'yanta ke ciki na kasa zaman 'aure da
yanda suka lalace suka zama tanfar ba su ne
wadannan yan gatan ba-da suke sha'aninsu irin
yanda suka ga dama.
Su daura zani irin wanda suke so komai suka yi
shi ne daidai, ra'ayinsu kua shi ne abin dauka, a bar
nà kowa ya bani tausayi bana kuma jin dadin irin
tsana da tsangwàmar da Babanmu ke nuna musu a
zahir nafi sha'awar da sai ya bar abin tsakaninshi da
uwarsu, tunda ita ce tayi sanadin komai.
Wanda duk yasan Mama, ya santa yasan halinta,

33
yagar hain da ita da 'ya'yanta suke ciki a yau, kalma
guda daya da zai iya furtawa cikir sauri ita ce, laifin
uwarsu ne.
Watsewar da aka yi aka bar mu dagani sai Baba
atsakar gida, yasa shi kallons cikii tnuroushi ya ce
min ba za ki sa a kwashe kayan da ki ka zo da su a
kaiwa innarku ta raba ba?
Nayi murmushi na ce ai sai ta.raberwa danginta
Babe namu dangin basu samu bą. Babana yayi
dariyar jin dądi a dalilin jin da yayi na tsame kaina
daga cikin dangin Innata.
Na ce, ai kai ne za ka raba sai kowa ya samu
tunda kowa naka ne. Wani dadin ya sake kama shi,
na ce amma kar ka manta da mutanen giyade, yayi
dariya mai karfi.
To in yi rabo kuma in manta da mutanen giyade
Humaira? Rabo na gaskiya Babana ya yi yanayi ina
tuna mishi wadanda ya manta da śsu.
Makwabta yan uwa, abokan tare ta kowane
bangare ya bayar, don ko ta bangaren Zubaida ya
bata turmi biyu ya ce na mahaifiyarta da kanwarta,
sabulai da omo na mutanen gidansu.
Mama kuwa kaya masu yawa ita da duk wanda
tasa zata ba har ma nata kason yafi na lnnarta yawa,
yana kallona ya ce bamu yi wa Gabo kwauron nata
ba ko? Nayi murmushi na ce, in bai ishe ta ba sai ta
sayà da kudinta ta kara, ya ce to haka.

34

Mun kammala komai ne muka shiga falon
Babana ni da shi muka sake. gaisawae na isar da
gaisuwar Ado a gare shi. Wai shi har yanzu yana
fushi dani ne ko?
Nayi maza na ce mishi a'a Baba, ya zubo min ido
yana kallona, nan take kuma ya zubo min
hannayenshi alamar dakwa.
"Kul ki ka kawo min iya shege, in ba fushi yake
yi dani ba don me tunda ya tafi bai sake waiwayowa
ba, ko a waya bai taða nemana ba'?"
Cikin natsuwa da nuna ladabi na ce, ba zai yi
fushi da kai ba Baba, to shi a wa ma da zai ce zai yi
fushi da kai? Shi din kullum a cikin fadar alherinka
yake.
Yana kuma gaya nin cewar ya karu da ilimi iri-
iri a wurinka na darasin rayuwa, yasha gaya min
cewar kai ne mafi alherin mutuIIn da yasa ni wanda
bai taba kyashin na kasa dashi ya samu alheri a tare
dashi ba.
"Bai yi fushi da kai ba Baba, sai dai kuma zai ji
nauyin kiranka a waya,. watakila so yake ya samu
damar da zai zo gabanka ya roke ka gafara kan
kuskuren da ya aikata maka."
To wane kuskure ya aikata min Humaira? Da ya
rike min ke? Shi mijinki tun kafin ya aure ki ai ni da
na dauke shi to balle kuma da yake aurenki yake
kuma rike min da ke cikin rufin asiri a yanzu."

35
Dadi ya kämä ni na ce to zan gaya mishi ya daina
tsoron kiranka Baba zai. kuma kira ka, to to to gaya
mishi.
Bayan wannan hirar nabi sai na isar da sakon
Ado gare shi na ce, amma ya ce kar in gaya mata sai
in kai din ka yarda ka aminoe, don haka sai in ka
yarda ne zata ji Baba.
Yarda? Yarda kai Humaira in da ina da hali
kamar da da bara ban biya mata ba? To bani da hali,
komai da ki ka sani babu shi, babu shi Baba? Nayi
mishi tambayar a firgice, ya ce ai babu ba I gani ba?
Ina ki ka ga ina zuwa? Nayi salati na ce yaya aka yi
Baba? Na shiga hankaling sosai don jin äbin da ya
same shi.
Sai kawai. naji ya ce min Baba da lorahi, hannu
biyu na saka na dafe kai3a, cikin tsananin kaduwa.
Bayan tafiyar mijinki sai wannan ja'irar matar
muguwa ta tasa i a gaba akan in maida su makwafin
mijinki a kasuwa.
Ta tasa ni a gaba da fitintinu iri-iri sai da na kái
su kasuwar, ba aje ko ina ba sai na gane kasuwar
tawa ba za ta juri ta'adin da ako yi mata ba don haka
sai na rufe ido nayi ta maza na kore su na kuma
haramta musu zuwa kasuwa.
Ni da uwarsu muka shiga wani Irali na babu dadi,
ga can kasuwar ma babu dadi, tunda na riga na samu
matsala, abokaina duk sun yi gaba sun bar ni, don

36

haka sai na ce to wadannan gidaje da mijinki ya
dawo min dasu tunda dama ban san da su ba, bari in
sanya su a kasuwa in karbi kudinsu in kara jari don
in koma harkar sosai.
An kawo min kudin gidajennan da kwana biyu
don mutum daya ne ya saye su, barayi suka zo min
gidan nan da daddare suka shigo min nan.
Kin ga kin gani ya nuna min wani shafcecen tabo
a keyarshi wanda na tabbatar ban san shi dashi ba ya
ce su suka buga in karfen da suka zo dashi suka
bincike min daki suka dauki kudi suka bar ni nan a
kwance a sume.
Sai daga baya sai da asiri ya tonu aka samu aka
kama guda daya, sai ya ce wai su Ibrahim da Baba ne
suka turo su zo suyi min satar.
Ni kam kuka sosai na kama yi saboda bakin ciki
da tausayin Babana, tabbas Mama ta cuci Baba na,
don kuwa ita tayi mishi sanadin lalacewar 'ya' yanshi.
yayan da kowa yasan babu abinda bai yi akan su ba,
don su zama mutanen kirki.
Bata aike shi ba, bata kuma bar shi yayi shi
kadai ba, kullum gini yake yi tana rusawa share
hawayenki kiyi shiru, Humairah ai ya wuce.
Ya wuce, kana zaune baka komai Baba? Yayi
murmushi ya ce to ba gani a raye ba? Da sun yi
nasarar kashe ni ko nakasa ni a wani wuri fa? Na
sake fashewa da wani sabon kukan.

37
Baba Yahya ne ya iso saboda kiran da Babana
yayi mishi, matar Sarkin Noma ne ta iso, nayi
murmushi na soa gaishe shi ai tunda naga tsaraba na
ce to ta Dabai ta iso kenan?
Babana ya kyalkyale dadariya, ya ce ai sunan da
ka sanya mata kenan? Baba Yahya ai ni sunanta
kenan a wurina tunda dai ta ki zama cikin mu ta
koma cikin danginta, to ba zan kirata da wani suna
ba, sai wannan ina ta ke?
Babana ya daga murya ya kira Zubaida da ke
goye da ita ta kawowa Baba Yahya ita ya karbe ta
cikin farin ciki yana fadin ka gani ba, wannan da
ganinta ai kasan gidan noma ta fito, taci hatsi ta
koshi.
Baba ashe abinda ya faru kenan mu ba mu sani
ba? Na tanbayi Baba Yahya cikin natsuwa don in yi
mishi jaje, sai ya ce min kece ba ki sani ba Aisham,
amma ko sanda muka je wurinku, ni da Mallam ai
mijinki ya yi mana jajen al'amarin ya ce min Innarku
ce ta gaya mishi.
Mamakin Ado yayi matukar kama ni, me yake
nufi da wannan abin da yayi bai gaya min ba, bai
kuma yi wa Babana jaje ko a waya ba?
Maganar tafiyar Inna da ya soma yi wa Baba ya
katse tunanin nawa, ni kam in ban da alheri Ado ya
yi wa Innata ai da na karbe kudin na mayar mishi
dasu, ban ji dadin yanda yayi ko in kula da abin da ya

38
Chapter 5 · 0% Book details