Sashe 4
Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
25
lokacin sallar tayi.
Ina idar da sallah su Atika da sauran yan uwa
suka soa kiran wayar Inna suna yi min sannu da zuwa
tare da fadin ga sunan zuwa, don haka na mike naje
nayi wanka da ruwa mai dui na watsake, nazo na
zauna ina shafa. Sa'adatu ma tana sanyawa
Umahmah kayanta, suma wankan suka yi.
Kai Anti, kin iya sayen rigunan yara, na ce bani
ba ce Sa'a kai ji wannan ma, wanne zan sa mata? Ji
wata ma, kai ga wata. Inna ta ce, da dai kin hakura
kin sa mata guda daya yau da gobe sai ki ga kin
sanya mata sauran ma, kin gansu a jikinta.
Kwalliya sosai nayi, wata super na sake daukowa
gara ta jiya da nazo da ita ma na taba daurata,
wannan sabuwa ce dal, Sa'a ta kalle ni tayi dariya ta
ce "Anti ai ke har kin fi ma matan masu kudin daura
zannuwa.
Nayi murmushi na ce, "Wannan shi ne iya shege
matar me kudi bata daura zani ta daura gwal ta hau
mota me numfashi ba me tayi?
Inna tayi murmushi ta kalli Sa'adatu ta ce mata,
kawo yarinyar ki kawo mata ajiyarta, ta kawo mata
ita ta wuce cikin dakin Inma, wata 'yar leda ta kawo
min wacce da gani na sani daga Saudi take, ga kuma
alamarta, ga yan akwatina a ciki har guda uku.
Daga ina wannan Inna? Ina bude su ina tambaya,
sarkokinki ne da ki ka tafi ki ka bari na baiwa Mama
26
sanda za su tafi aikin hajji da Aliya, na ce ayi ciko a
canzo miki sarkoki ne guda biyu babba da karama,
ga kuma warawarai guda hudu da zobuna biyu,
wanda ni su suka fi daukan hankalina ma.
Don nan take na zuba su a hannayena ta kuma sa
zobunan, in ban da Inna ta ce in sanya karamar
sarkar ma ni ka da hakan ma ya ishe ni. Godiya mai
yawa nayi mata.
Na tashi na fito tsakar gida saboda jin da nayi
Babana yana tambayar wai ni Aisha bata tashi ba ne?
nayi maza na ce ai ban ma kwanta ba Baba, wanka
nayi.
Akan katuwar shifidaddiyar tabarma na same shi
a tsakar gida yana zaune wanda wannan-ba wani abin
mamaki ba ne, dabi'ar gidan ne yin hakan, abin
maakin dai shi ne, yau shi kadai na ganshi zaune
akai, ban ga Miama ba, ban ma ji motsin fitowarta
wajen ba tunda gari ya waye ban ma ji wo muryarta
ba ko da daga cikin dakin ne, shiru.
Sai Zubaida da ke ta faman kai-kawo tsakanin
kicin da tabarmar Babanmu.
Kai Antin Sa'adatu kin yi kwalliya kin kuma yi
kyau ba an ce min garin naku kauye ne ba? Na kalli
Zubaida nayi murmushi na ce, Anti kenan. Karo na
farko da bakina ya yarda ya kirata Anti, ba akan an
tilasta mishi ba.
Babana yayi tsaki ya ce, ka ji wani zance wurin
27
yarinyar nan, to harkar yau aljihunka ba shi ne
birninka ba? Kana zaune a birni ba ka da ko kwabo ai
ka zama dan Rauye, sai dan kauye ya ci duniya in
yana da kudinshi kai baka ci ba.
Tayi maza ta ce, haka ne kam, itama bin atanfar
tawa take yi da ido, a zuciyata na ce itama ta koya
wurin Mama, zuwa can kuma sai naji ta ce mu ma fa
atamfofin da ya aiko mnana super ne, ban tanka mata
ba
Na kalli Babana wanda shia dadin ganina ya
kama shi, ga kwalliya mai kyau mai kuma tsada, na
ce mishi Baba bari in je in gaida Mama, ya ce to kar
ki dade, don yanzu zamu karya. Me ki ke so ki karya
da shi?
Na ce duk abin da Anti Zubaida tayi dashi zan
karya. Yana murmushin jin dadin ganin mu'amallata
da Amaryar tashi, Sa'adatu ta kawo mishi Umaimah
daidai zan shiga dakin Mama.
Sau biyu nayi sallama katin ta amsa, bayan tana
ganina ina ganinta, na ce mata sannu Mama, ta ce
yauwa sannu kadai, muka sake gaisawa ba tare da ta
tambayeni Ado ba, balle 'yarshi.
Ni kuwa na bararraje na zauna mata a daki sosai,
cikin zuciyata ina fadin abinda ka shuka shi ka ke
girba, komai na dakin yayi dikin-dikin alamar datti
ya kama shi saboda ba ta shi ake ba, ba a da lokacin
shi balle a samu zarafin gyara shi.
28
Wai Mama da Babana suna hade a gida amma
babu mai kula wani, kowa harkar gabanshi kawai
yake yi, in da wani abin da ban taba zaton zai faru
ina raye ba ai shi ne wannan.
Ni 'yanjakar ubannan sun ma zo sun gaishe ki
kuwa? Daga waje Babana ya daga murya yayi min
wannan tambayar, nayi kamar ban gane su waye ba,
tunda ina jin motsin mutane a dakın Mama, na kuma
san su Suwaiba ne sun ki fitowa ne kawai don kar
muyi ido hudu da su.
Watakila suna tunanin kwana daya ko biyu zan
yi, su waye kenan Baba? Cikin natsuwa da murmushi
mai yawa don dai ma Mama ta kara sanin mun shirya
da Baban nawa, nayi mishi tambayar.
"Wadannan 'yanjakar uban mana." Ya sake yin
zagin, mamaki ya kama ni ban san Babana da yawan
zagi ba, watakila itama Mama abin ya dame ta, don
wani mummunan tsaki naji taja kafin naji ta ce.
"Kai Allah kenan, rayuwa dai bata yi ba tunda an
kare da zage-zage. Da sauri na kalli Mama saboda
jin maganar tata dan kirin ya rage in kyalkyale da
dariya, saboda yanda ta tsuke fuska ga ta kuma dama
ta zama 'yar karama.
Wadannan yan jakar uban Mama su Habiba
masu gadon mugun abu ai suna nan a ciki."
Gabana ya yanke ya fadi, cikin tsoro da kunyar
masu gadon mugun abin da yake fada nayi maza na
29
ce, a'a Baba, ai ma ba laifinsu ba ne nawa ne, da na
yi wa gidan shigowar dare.
Da sauri na mike na nufi can cikin dakin na
Mama na barta tana tsaki tare da fadin wannan yaron
ai wahala ta same shi, tunda ya gamu da mutane
marasa Imani, balle tausayi." Ko a jikina.
Ashe kuna ciki? Nayi tambayar daidai na daga
labulen kofar wanda ya zama tanfar ba na Mama ba
don datti. Abinda na ganin yayi matukar kadani,
tukunyar alala akan risho a bayan kofar Mama yana
tafasa, ga Anti Sha'awa da Habiba suna kwance kan
katifar da ke yashe a kasa sun tasa 'ya'yansu a gaba
suna basu non.
Suwaiba ce a gaban tukunyar tana rantsuwar ita
da kanta zata raba don ba za ta yarda ta bar musu ba
su kwashe su baiwa 'ya'yansu, su bar mutane da
yunwa.
Na kalli 'ya'yan sun kai biyar ban da masu shan
nonon, sun takura waje daya gaba dayansu ya'yan
Anti Sha'awa ne. na ce, kai su Buhari ne haka? Suka
zubo min ido alamar a cikin doka suke.
Muka gaisa da Sha'awa da Habiba har na karasa
shiga na yi wa 'ya'yan da suke shayarwa wasa,
Suwaiba ta sunkuyar da kai kasa tayi kamar bata
ganni ba, nima na wuce na fito ban tanka mata ba.
Na kama hanya zan fita saboda jin muryar
Salisusu da nayi, na kalli Mama nayi murmushi na ce
30
Kawu fa ya ce a gaishe kir da kyau-da-kyau, ta ce
madailah.
A tsakar gida Salisusu yana tsugune suna
gaisawa da Babana, ga katuwar kula a gefenshi
alamar shi yazo da ita, sannu da zuwa Yaya, ya dago
ya kalle ni cikin murmushi, Anti ashe kun iso? Na ce
eh.
Ina Baban ba ka zo min da shi ba? Yayi
murmushi, suna nan zuwa. Muka gaisa sosai, cikin
yanayin suruka kafin ya mike ya shiga wurin Inna.
Babana ya kalle ni ya ce min, ga abin karyawa nan
daga wajen Atika.
Nayi murmushi na ce, an gaishe su, amma sai
naci na gida na Anti kafin in ci na wani, dadi ya sake
kama Babana.
Muna cikin haka sai ga su Buhari a guje Suwaiba
ta biyo su tana duka, wai ta ce kar suyi warwaso sun
yi, Baba ya daka musu tsawa kai ku min shiru ku
koma dakinku ku zauna kar kuzo nan ku cika min
kunne da ihu, 'yan jakar uba kawai marasa da'a masuu
abin tsiya. To an koya musu.
Cikin zuciyata na ce, oh oh, Baba kuma sarar da
ya samu kenan? Ko da yake dai ba laifin shi ba ne,
Maman ce ta koya ishi komai yaro yayi, ta ce mishi
wai uwarshi ta koya mishi.
To gashi abin yazo kanta, a wancan lokacin da
take sha'aninta kuwa bata taba tsammanin abin zai
31
koma mata ba.
Salisusu ya yi wa Babana sallama ya tafi, sai
kuma ga dan aika daga gidan Hajiya Aliya, da
manyan kuloli itama abin karyawan ta aiko dashi, ga
kuma na Zubaida shima ya kammala.
Na kalli Babana a hankali cikin natsuwa na ce
mishi, bari in kira su Habiba mu karya tare Baba. Ya
yi maza ya yautsa fuska, kar. ki kira in wadannan
yan jakar uban yaran.
Na sake bashi hakuri kafin na dauko wata
katuwar tabarmar na shifida na leka falon Mama na
ce "Habibah ku fito nan mu karya. Buhai ku ma
kuzo dukkanku.
Na koma sabuwar tabarmar don mu zauna dasu,
tunda sun kasa zuwa kusa da Baba, na ce 'rai dai' wai
in ji kuda, Mowowin Baba wadanda suke komai suka
yi daidai ne, sune yau suka zama babu wata
mu'amalla a tsakani sai na zare ido da mmuzurai.
Na kira Zubaida na nuna mata abin da Atika da
Aliya suka aiko dashi, na ce mata samo wuri ki diban
wa Baba nashi da na Mama da Inna da naki ta ce to,
nayi zaton Mama zata ce ba ta so sai naga tasa hannu ta karba.
Mu ma na Zuzzuba mana har yaran nasa musu
nasa kuci a natse in baku koshi ba sai a kara muku,
suka ce to ita ma Suwaiba na aike mata na kira Sa'a
na ce mata ta kawo mana kunun gyadan da inna tayi.