← Book details Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 24

Sashe 21

Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ka fito daga dakin amaryar ne?
Shima bai amsa ba balle ni, to kaima kenan ana
jin haushinka ba a baka abinci ba to balle kuma ita
wannan aure ai fata dai kawai Ubangiji yasa ba asarar
dukiya aka yi ba, tunda ban ga alamar yayi wani
tasiri ba.
Na fito daga dakin Mama na dawo nawa nayi
maza na dauki gyalena zan fita, sai ga Ado ya shigo
ina za ki Humaira? Maimakon in tsaya gaya mishi
inda zanin sai kawai na soma yi mishi kuka.
Kuka kuwa mai tsananin gaske, saboda bakin
cikia shi ya ishe ni, kiyi hakuri, hakuri yake ta bani
sai da ya ga na dan natsu sai ya ce min ban fa yi miki
wani aibu ba Humairah, ban kursa zalunce ki ba, ba
kuma zan zalunce ki ha.
Saboda ban yi aure don na gundura da ke ko kin
ishe ni ba, nayi ne don ina son karawa yin hakan
kuma ba laifi ba ne, gode ni'imar da aka yi min nayi
Na roi alfuoarki ki ba ni mu zauna lafiya kar kiyi
min abin da k: ka san úa car ba kya yi min.
Kar ki fita ba da izinina va, zan hakura da komai
amma ban da wannan, in ki ka dan yi hakuri da ni
kadan nayi miki alkawarin zan yi mai yawa da ke.
In ki ka dan kawar min da kai ki ka yi min
kawaici na miki alkawarin zan ji kunyarki, in kuma
yi ta girmamaki, saboda ke din dama kina da girma a
wurina. Yanzu muje ki bani abinci yunwa nake ji,

136

nace ai ya kare, ya sake kallona cikin natsuwa kafin
ya ce min Humairah kenan.
Kina ganin idan ki ka azabtar dani da yunwa da
akwai wata riba da hakan zai kawo miki? Ai yanda ki
ka shirya abin da ya dace ki ka tura wa Balkisu tare
da yara sa'o'inta don su debe mata kewar zaman
gidan su saboda kin yarda bata yi miki laifin komai
ba, ba ita ta kawo kanta bani naje na kawo ta.
Haka ya kamata ki yarda nima da na kawo ta ba
laifi nayi ba, Humairah. Sannan ko da nake ni na
ajiye ku dukanku kin fi kowa sanin ina gudun bacin
ranki, ina tsoron ganin fushin ki.
Ina yin komai ko barin komai don neman zaman
lafiya dake, to na roke ki kar kiyi amfani da damar da
ki ke da ita a kaina don ki kuntata min ki hana ni
morar halal din da aka halalta min.
Kalaman nashi suka dan sani natsuwa, naje na
dauko daya kazar da na bari a cikin oven din na kai
mishi falonshi tare da ruwan matsattsen lemo, to
zauna mana na ce mishi IRa zuwa na dawo wurina ina
shiga wayata na dauka saboda rurin da take yi.
Gabana ya fadi kar dai wani laifin aka je aka
cewa Inna nayi take nemana? Jikina a sanyaye na
Soma amsa wayar tata, sai naji ta ce min, taro ya tashi
lafiya? Na ce lafiya Inna.
Ta ce, to Ubangiji yayi miki albarka, ke da
zuriyarki, ya saka miki da alheri, ya kuma baki

137
hakuri da juriyar rike girmanki, na ce to amin Inna.
Muka dan fara hira da ita har na dan saki jiki na
gaya mata wulakanci da cin mutuncin da Ado yayi
min, na shiga dakin matarshi da rana tsaka, sai da
tayi ajiyar zuciya kafin ta ce min.
Kar ki rinka kokarin shiga tsakaninshi da ita,
babu ruwanki kamar da ido kawai kan al'amarin nasu
kamar yanzu ne kawai sai ki ka zafin shi yana ta
raguwa a zuciyarki.
Yafi Yafi ace za ki rinka damywa da su ku rinkka
samun matsala ke dashi har ita yarinyar tayi wayon
da zata gane kina da damuwa a kanta, sai ta raina ki.
Kin ga abu ya baci kenan, aa ce haka ne Inna.
Muka dan yi shiru kadan sia naji ta nişa ta ce ai
kishiya zafi ne da ita, sai kayi hakuri in ba haka ba
sia ki ga ka gudu ka bar ladanka.
Na ce ai aima dazu ji nayi kamar in gudun, tayi
aza ta ce kar ki fara ai gidanki ne kiyi mata adalci,
kawai Ubangiji zai hore miki zama da ita na ce to.
Dama Inna ta bani sosai na in saki jiki in yi magana
da ita.
Magana kuma ba irin ta uwa da 'ya ba kawai, a'a
har da zancen kawa da kawa aminan juna tana yi min
magana in muka soma gaisuwa zata sako min
maganar kishi'.
Watakila don tasan shi ne babbar matsalata ta
lokacin ni kuma da yake na riga na kidime bana iya

138

boye mata zafin da nake ji, in yi tá gaya mata abinda
nake ji da yanda zuciyata take tafarfasa in fadi
maganganu masu zafi a kanshi.
Rannan ma dai da'yake na riga na tunzura da
yawa saboda abin da nake ganin yanayi da tayi min
wayar ce mata nayi, kai ni kam Inna to me zan sake
yi da Kawu ne kuma? Me zai sake yi min in ga ya
burge ni kuma a rayuwar nan Inna?
Ai ni kwata-kwata gaba daya ya riga ya fita
kaina babu abinda na tsana irin in ga wulgawarsu ko
in ji maganarshi balle in gan shi ya shigo in da nake,
sai in ji kamar in mike kawai in rufe shi da duka in yi
ta duka.
Dariyar da tayi ne yasa na katse zancen nawa,
nayi shiru, me yayi miki da zafi ne haka Baban
Umahman? Na dan yi murmushi saboda jin sunan da
ta kira shin na ce bare-barenshi ne yayi yawa Inna.
Ba ki ga irin rawar jikin da yake yi akan yarinar
nan ba, shi yasa ma na ce ni kam ko ya sake dawowa
wurina ba zan sake sauraronshi ba, tunda dai abin
nashi haka ne na hakura dashi na bar mata shi na
yafe, suje can su karata kawai
To in ki ka yi hakd ai ba kiyi mana adalci ba,
nayi maza na ce kamar ya ya Inna har da ke a ciki?
Tayi murmushi ta ce, dani kai tsundum a ciki, ke din
ai tanfar uwa ki ke a gare ni a yau, zaman lafiyarki da
kwanciyar hankalinki a gidan aurenki yana nufin

139

al'amura masu yawa a gare ni, don nasan shi ne
kwanciyar hankalin 'ya'yanki.
Ni nasan babu wani bare-baren da rawar jikin da
zai yi akanta da har zai tsole miki ido, in ba kin bar
abin da yake gabanki kin maida hankalinki a gare su
ba. Me zai mata ya kai wanda ya yi miki?
Ai babu shi, maganganu masu dadi tayi ta yi min
har dai na ahkura na yarda da cewar wai duk abin da
yake yin bai kai wanda ya yi min ba, amma ni kam in
ban da Innan ce ta gaya min haka da ban yarda ba.
Don gani nake tanfar babu ma in da aka taba yin
irin abin da shi yake yi din. A haka sai gashi ya dawo
dakin nawa, kashedin da 'Inna tayi min na cewar
matukar ba-shi ne ya kawar da kai daga gare ni ba, to
kar in bijire mishi dashi nake shirin yin aiki.
Don haka nake ta fatan shi din da kanshi ya fita
hanyata tunda ni kam a yanzu nafi so ya bar ni kawai.
Zo nan kiji Maman Umahmah cikin zuciyata na
ce wani,wayon zai yi min don kuma ya kan kira ni
Maman Umahmah ne a irin lokutan da yake-ganin
tanfar al'amura suna shirin cabe mishi a tsakaninmu.
Ai babu wata amaryar da zata yi irin amarcin da
ki ka yi a hannuna, Humairah ke ce fa, ya. soma
lissafo min alarmura masu dadi da suka gudana
tsakanina da shi a lokacin amarcin da muka yi
sannan ya kalle ni ya ce to a yanzu wanne nake iyawa
a ciki?

140

Sannan ke ce Humairah da na kamu da sonki sai
na iya tsayawa na nunawa kowa har da wadanda bai
kamata in yi musu wannan tsaurin idon ba, cewar ke
din ke kadai nake so, ke kadai nake bukata.
Zan kuma iya barin kowa saboda ke a yanzu wa
zai sani in yi irin hakan? Ado ya soma lissafo min
al'amura da tun ina jin shi ne kawai har ya soma sani
murmushi har ya sani na hakura na fidda komai çikin
raina nasa hannu biyu na karbi al'amarin aurena.
Shi da kanshi Ado ya fahinta tare da sanin cewar
Inna tayi tasiri mai yawa a cikin harkar
zamantakewar rayuwar aurena dashi da kuma
amaryar da yayi, don haka kullum a cikin girmamata
yake, kullum kara ganin mutuncinta yake yi.
A kullum kuma in ya bude baki zai fadi wani abu
game da ita, to alherinta da karemcinta gami da
adalcinta ga suruki shi ne abinda yake bayar daa
labarinta akai.
Rannan na wuni cikin farin ciki da zumudi
saboda Ado ya gaya min zai tafi Abuja gobe, a dalilin
hutun da ya dauko ya kare, dadi ya kama ni a
Zuciyata na ce zan dan huta da ganin mu'amallarshi
da 'yar yarinyar nan da ko kunyar tubewa a gabanta
ba yayi, duk da karancin shekarunt.
Tsananin farin cikin nawa ne yasa na yi wa Inna
waya nake bata labarin da zai yi, sai ta ce min ba da
ita zai tafi ba kenan? Nayi maza na ce, a'a shi kadai

141
Chapter 21 · 0% Book details