← Book details Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 24

Sashe 16

Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

101
ba kya iya yi wa kanki komai amma kin ajiye sanda
don dukan wadanda ki ke son duka?
Ya dago ya kalli Umahmah ya ce, Umahnmah,
tayi maza ta ce na'am Baba, ya ce daga yau na sauke
miki nauyin kulawa da Mama da maganinta da motsa
jikinta, duk ba naki ba ne.
Zai zamo na Mamanki bari ke in dora miki
nauyin kulawa da Maman naki kin san irin abincin da
na canza mata don gyara min jikinta? Tayi maza ta ce
eh Baba.
Ya ce to ki rinka shirya mata shi kina bata ita
zata kula min da Mama.
Umahmah tayi dariya cikin tsananin farin cikin
canjin da ta samun ta ce mishi sau goma zan rinka
bata ko sau ashirin Baba?
Ya ce, a'a Umahmah ai rage kiba da rage teba
nake so tayi ba karawa ba, don haka sau uku kadai za
ki bata, ta ce mishi to. Tana murna tana tsalle don
dadi, tasa kai ta fita. Tun daga nan bai wa Mama
magani da motsa mata jiki ya dawo kaina.
Gaskiya ne, tunda Ado ya tilasta ni janyewa daga
cin abinci mai nauyi irin namu na dafawa na janye
daga cin nama mai yawa, na koma cin irin
ganyayyakin da ake nomawa a gonar Humaira
Farm'.
Nayi matuka zabge jikina, tebar da na ajiye tayi
matukar sauka na rasa nauyi mai yawa a tare dani

102

daga kilo sittin da biyar zuwa saba' in na dawo
arba in da bakwai zuwa hamsin.
Na kurma tsaya akan motsa jikina safe da yamma,
don in kara gyara jikin nawa ta yanda mai gidan zai
samu yanda yake so.
Masani da motsa jikin Mama na gama na dawo
nazo na samu Umahmah tana zaune tana jiran zuwan
nawa, wai abincina ta shiryo ta kawo min, kin san
Goggo nasa miki 'Asparagus' sanda daya Brocooti
daya ganyen celery danyen dankalin turawa guda
uku, cherry tomatu biyu, Beef tumatu biyu, cabbage
dan madaidaici, kwai dafaffe biyu
Na ce to na gode Umahmah bari in yi wanka
tukuna in fito ta ce min to, har nayi wankan nazo na
gama ci tana jirana in kawo miki madarar shanu na
dafa miki?
Na ce kawo min taje ta kawo min a kofi ina
karba na kafa kai na kwankwade, ta zuba min ido
tana kallona tayi murmushi ta ce, Goggo ke kam
kwankwadar madara ki ke yi nace eh, Umahamah kin
san mu komai addininmu ya koya mana yanda zamu
yi shi.
Don haka madara kwankwada muke yi, ruwa
musha a hankali, sai zuma kuma mu lasa, kin gane?
Tayi maza ta ce min eh.
A wannan lokacin ba Ado ba da dama kullum
jikina abin jin dadin shi ne kowane lokaci kuma cikin

103

tattalin jikin nawa yake don ya kara jiyar dashi dadin
da yake nema.
Ni da kaina ina jin dadin jikin nawa, ya yi min
warai-wasai, bana tare da wani nauyi, kullum
kuruciyata kara bayyana take, kwalliyar da na dama
nake yi saboda ina daukar kowane iri.
A daidai irin wannan yanayin ne da lokacin wani
irin lokacin da nake ganin tanfar ban taba samun
wata dama ta mallakar mijina kamar shi ba.
Ado ya dawo daga tafiya zuwa kasar Thailand in
da ya tafi taron kärawa juna ilimi kan noman Rania
kasashe masu tasowa, saboda a wannan lokacin ya
shiga kungiyoyin manoma daban-daban cikin kasa da
waje.
Kwalliyar mini siket da wata 'yar shirmanmiyar
riga nayi mishi, shi ne kuma ya taho min dasu in na
tsaya cewa nayi kyau ma nayi shirme.
Kallona Ado yake yi yana karawa, watakila ji
yake tanfar ya kama ni yayi ta lashewa tun lokacin
yin hakan bai yi ba.
Ban fa bai wa Mama maganinta ba, fuskarshi ta
dan yannutse alamar ba ta maganin ya somma shiga
mishi cikin harkokin rayuwarshi.
Bari dai zan nemi wacce zata rinka yi min
wannan aikin ina biyanta, don na riga na fara gundura
da yanda hakan yake shiga lokataina.
Nayi murmushi na ce, ai ba wani dadewa ma ake

104

yi ba, minti arba'in da biyar ne kawai. Ya kalli
agogon hannunshi kafin ya sake kallona, ai ba zan
iya jiranki minti arba'in da biyar ba, sai in ga kamar
awa arba'in da biyar din ki ka yiwo, muje in raka ki.
Na mike tsaye da nufin zuwa dauko alkyabbata
da gyalenta in sanya in rufe kwalliyar tawa, tunda
nasan ba zai yiwu in iya shiga wurin Mama a haka
ba.
Hannu ya saka ya jawo ni na fada jikinshi,
Humairah kina kallon yanda ki ka zama kuwa a
madubi? Ko ban kalla ba ai kana gaya min kuma in
dai nayi maka ka gamsu to ai shi kenan ya ishe ni.
Kin yi min na gamsu Humairah, kin zama tanfar wata
yar yarinya mai shekaru ashirin da biyar.
Nayi dariya na ce, goma fa ka rage min Kawu, ya
ce uh ba ki i ashirin da biyar din ba, babu mai
ganinki ya ce kin wuce hakan, don haka bar gonman
kawai a gefe in kin ga dama ma ki dora min a kaina
tunda ni kam ni ne...
Nasa hanu a bakinshi na ce na ce baka yi ba
kawu, ganinka nake tanfar yau ne nmuka faro komai in
don wannan tebar taka ne bata yi maka komai ba in
ban da mutunci da kwarjini da ta kara maka.
Ado ya kyalkyale da dariya ya ce, muje ki bata
magani mu dawo na sanya alkyabbata na rufe kaina
da gyalanta muka fita muka nufi dakin Mama, tana
ganinmu ta rushe da kuka.

105

Ni kam nasan ganin da tayi mana tare ne yasa ta
kukan gashi kuma na dan makara kan lokacin da na
saba zuwa bata maganin, amma Ado da bai gane
hakan ba rarrashi ya rinka yi yana bata hakuri tare da
tambayarta damuwarta.
Wani abu ke miki ciwo Mama? Tayi jagwale ta.
kara maida kanta ta kara zama abin tausayi, ta girgiza
kai uh'uh wasu hawayen suna kara zubowa, to
menene?
Kiyi magana mana Mama, ganin kidimewar tashi
a kanta ya kara bata dama ta sake rushewa da wani
sabon kukan.
Cikin kukan naji tana cewa, wai burinta ne kawai
ta gane ba zai cika ba a kanshi har ta mutu, da sauri
Ado ya zaro ido yana kallonta cikin kidima tare da
tambayarta menene burin nata?
To ba Ado ba, ko ni da ba wani damuwa nayi da
lamarinta ba, mu'amallah kawai nake yi da ita don ta
zame min dole, 6oyewa kawai nake yi nake kuma kin
yardan wa zuciyata dauke ta ita din damuwa ta ce
tunda nasan damuwarta a kaina tafi wacce nake da ita
a kanta yawa.
Kasake nayi ina kallon Mama tare da sauraron
abin da zai fito daga bakin nata a matsayin shi ne
burin nata, sai kawai naji ta kekkebe baki ta ce, wai
in ganka da mata biyu, kadan ya rage in yi subutan
hannu in buge bakin Mama da abin da nake rike da

106
shi na gwajin jininta.
Sai na daure kawai cikin zuciyata dai gaya mata
nayi ai ke da burinki za ki mutu Mama, Ado kuwa
shiru yayi na wani lokaci mai tsawo, cikin wani
yanayi da yafi kama da tausayinta ne yafi komai
kama shi.
Zuwa can sai naji ya bude baki ya ce mata kiyi
hakuri Mama in har na samu yanda zan yi to ba zan
bar ki har ki mutu da wannan burin ba, zan cika miki
shi nan ba da dadewa ba, in har muna raye dukkan
mu, kiyi hakuri.
Cikin yanayin shagwaba ta ce mishi, to. Hannu
yasa ya karbe abubuwan da na zo dasu din na
amfanin nata yayi mata komai saboda jikina ya riga
yayi min sanyi, na riga na gane wannan burin na
Mama na son ganina da kishiya.
In ba wata kaddarar ba zai cika a kaina, don
kuwa kalaman da yayi amfani da su wajen bata
hakurin sun sha bamban sosai da wadanda na saba
jin shi yana yi mata a duk lokacin da tayi mishi
magana kan ya kara auren.
Mafi yawancin lokaci murmushi yake yi ya ce
Mama kenan, ba wai bana son yin auren ba ne, ko
kuma na kasa yin shi lokacin yin nashin ne kawai bai
yi ba, don haka kiyi hakuri.
Ita kuma tayi ta zuga tana kokarin tunzura shi
kan wai ya kasa ne, sai ya ce to Mama in na kasa ma

107

ai ba wani abu ba ne dama karawan ba na kowa da
kowa ba ne na wanda yaga zai iya adalci ne, in ba za
ka iya ba sai ka zauna da guda dayarka kawai.
Ni da in yi biyun in zo ina zaluntar wata ko ana
zaluntarta ina kallo na rasa yanda zan yi ai gara min
in yi ta zamana a haka. Sai taja tsaki ta ce ai kuwa da
ka ji kunya.
To yau ba haka aka yi ba cewa yayi in har ya
samu yanda yake so nan ba da dadewa ba zai yi
sanadin cikan burin nata. kenan yayi nufin yi shi
kuma mutum ne mai yin aiki da abinda ya fada.
Tashi muje Humairah, kalmarshi da naji kenan
na dawo cikin natsuwata na fahimci ya gama yi mata
abinda ya kawo mu din. Sai dai duk da na gane
abinda yake shirin yin ban muna mishi wani canji ba.
Iyaka dai bayan ya samu bacci ya dauke shi,
maimakon nima in yi nawa baccin don in samu hutun
da ya dace da jikin nawa tsunduma nayi cikin tunani
mai yawa, in saka wannan in kwanče, in saka
wanca.
Mama zata yi min sanadin kishiya a daidai
lokacin da ni da mijina muka dunkule muka zama
abu guda daya, ya zama ni a zama shi. Zata sa shi
kawo min wata cikin gidana don ta samu hanyar
wargaza min gidan, tayi min sanadin fitina, tayi
dalilin da nima zan kasa zaman gidan mijina kamar
yanda itama nata gidan mijin ya gagare ta.

108
Chapter 16 · 0% Book details