← Book details Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 24

Sashe 2

Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kulawa dani ki bani lokacinki?
Na kalle shi cikin natsuwa, sannu a hankali na
sakar mishi lallausan murmushi, don in samu damar
isar da sakon da nake son isarwa zuciyarshi, don
kuwa na nga na yi niyyar rike mijina a hannuna.
Na sani babu abin da zai farantawa Mama rai irin
ta ganni a gida babu auren Ado a kaina, ace mata
yan uwanshi ma'ana dangin ubanshi nc suka yi
nasarar raba ni da shi.
Yan uwanmu ne dukanmu kawu, ba 'yan
uwanka ba ne kai kadai, don sunyi mana wani abin
da bai yi daidai ba ba zai hana ka samun lokacina ba,
kai mijina ne.
Kai ne kuma mafi darajar mutancn yanzu a
wurina, ina kuma sonka. Ban taba furtawa Ado irin
wadannan kalaman ba, ban taba kallon idonshi na
furta mishi wata kala ta nuna kauna ko mihimmancin
a wurina haka ba.
Don haka maganar ta shige shi da kyau, abin da
kuma dama nake son gani kenan.
Humaira! ya fadi sunan cikin wani yanayi, yaja
bakinshi yayi shiru, wata kila saboda ya rasa kalmar
da zai gaya min, ina sonka kawu, na sake furta mishi
kalmar.
Jikin Ado ya dauki rawa, tanfar dai wani irin
tsimi aka bashi, nayi amfani da damar da na samu
wajen yi mishi abinda ya dace in yi saboda in kara

12
mallake abinda yake dama nawa ne.
Lokaci mai tsawo muka dauka ni dashi cikin
wani irin yanayin da ba zai yiwu in kwatanta shi ba,
sannu a hankali ya yi gyaran murya bayan ya samu
natsuwar da ta dace da shi, a hankali ya soma yi min
magana.
Zan sallame ki gobe in muna raye kije gida kiyi
bakuntarki, duk da ba a haka naso kiyi tafiyar ba, ba
kuma a goben na shirya ki tafin ba.
To amma kuma ba zan iya barinki a gidan a
yanzu ba don ina bukatar kwanciyar hankali da zan
yi wasu abubuwa kan abubuwan da suke 2aruwa.
Wani irin sanyi ya sauka cikin raina, ina fata za
ki je ki dawo ba tare da kin gayawa inna wannan
damuwar ba? Nayi maza na ce mishi ko, kadan, to
gaya min in ji ke da kanki don in ji irin adalcin da za
ki yi min, kwana nawa zaki yi?
Cikin zuciyata naji tanfar in ce mmshi to in yi
wata biyu? Sai naji tsoro kar ya ce ya tasa, na ce
mishi da dai kai da kanka ne ka gaya nin da yai.
Yana makale dani a jikinshi yayin da kurma nake
bai wa yarinya nono, ya ce a'a ai ni nace ki fada sai
dai a duk wani hukunci da za ki zartar a tsakanina da
ke, na roke ki kar ki so kanki a kaina, komai za ki yi
kiyi adalci a tsakaninmu.
Ki sani ba a yau ki ka fara ji na ina furta kaimar
ina sonki ba, nayi hakan yafi a kirga. A yau kua ina

13
so in kara jaddada miki ina sonki fiye da duk yanda
ki ke tunani, gaba daya fatana da burina kuma bai
wuce in samu wata dama da zan nuna miki halaccina
ba, in dai nuna miki cewar ni din namiji ne.
Na ce to in yi...ban san yanda aka yi ba, sai naji
bakina ya ce mishi, kwana goma? Yayi murmushi
alamar ya ji dadin hakan da na fada, za ki iya yin har
sati biyu babu damuwa. Na ce mishi to na gode.
Gari na wayewa na soma shirye-shiryen yin
tafiyar da Adon ya ce zan yi a ranar yayin da shi
kuma ya ce min zai je wani wuri ya dawo, na ce
mishi to.
Yana fita kuma ya toro min Bala, wai yazo in ba
shi ayyukan da zai taimake ni da su, na kuma san har
da tsaro yasa ya turo shi.
Yana taya ni aikin yana ta murna, Mallam ya ce
zai yi min rakiya zuwa gidanmu, kai Innarku da kirki
take Anti Humaira, na ce ko? Yayi ta rantsuwa, na ce
ai na yarda Bala huta da rantsuwar taka haka.
Tunda Ado ya bar gida wajen shidan safe bai
dawo ba, sai wajen sha biyun rana. Kan nan kuwa
babu abinda ban yi ba har miyar da na saba yi mishi
wacce yake tafiya da ita Danja tun bayan rikicin da
muka yi kan zamanshi a can na soma yi ishi.
Ki gama dai ko? Na ce mishi eh, ya ce ina
Umahmah? Na ce tana wurin Goggo Ayalle. Ya zuba
min ido, nayi mishi bayani na gyarata naje na kai

14
mata ita.
Ba zai yiwu ace zan dauki mataki akanta ba,
suma mutanen gidan duk naje na gaishe su, amma
ban yi musu maganar tafiyar ba, tunda baka gaya min
ba.
To kin kyauta, bari in je in gaya musu, na ce to.
Ya fita bai dade ba ya dawo, kai Bala jeka kayi shiri
kazo ka fitar da kayan nan ga motar da zaku yi tafiyar
da ita can a waje, yayi maza ya fita sai washe baki
yake yi.
Na zubo abinci naje na kai mishi na zauna yana
ci shi kuma yana yi min bayani, na dan yi miki
sayayyar tsaraba, sai dai bata da yawa tana bayan
mota nayi godiya tare da yi mishi addu'a bayan naa
tabbatar mishi da cewar ta ishen.
Ya turo min wani dan kunshi wanda ya nadc
cikin leda, ya kuma yi rafin din soletep ya nadu
sosai, nasa hannu na dauki kunshin ina dan jinjina
shi a hannuna, bai kalle ni ba ya ce min kudi ne a
ciki, ki kaiwa Baba ki ce mishi na roke shi ya biyawa
Inna kujera taje ta sauke faralinta.
Ban san san'da nayi jifa da sunkin kudin nan ba
na kankame Ado don farin ciki, in kin je gida ki ce
ina gaishe su na ce mishi to.
Sallama nayi da kowa a gidan cikin wani yanayi
da bazan iya kwatanta farin cikina ba, ina fitowa daga
wurin Ruwailah ina jin ta tana cewa yar hirarta ai

15
una nan da ita sai ya nuna mata cewar shi din da
namiji ne.
Na shiga wurin Goggo Ayalle nayi mata sallama
nasa hannu na dauki Umahmah na rungume a kafada
maimakon in bari a biyo ni da ita saboda gaskiyar
magana ita ce girma da kunyarta da nake ji sun yi
matukar raguwa don ta riga ta bar ni na gane in da ta
dosa.
A cikin motar ni da Ado ne a baya saboda wai
zai sauka ne a mararrabar Danja ya tafi Danjan mnu
kuma sai mu nufi Kudan zuwa Makarfi, daga nan mu
isa Kano mu dauki hanayr Bauchi, shi kuma Bala da
direba suna gaba.
Kwalliya sosai Ado yayi yana rungume da
yarinyar a cinyarshi, na kalle shi naji dadi mijina ai
cikar halitta ne mai kuma tsabta ga kwarjini ga zati
kalaman Baba Tanimu suka fado cikin raina na yaje
ya duba wasu 'yanmata.
A hankali cikin natsuwa na tambaye shi, amma ai
ba za ka fara zuwa tadi a bayana ba ko? Bai juyo ya
kaile ni ba murmushi yayi ba tare da ya daga shi daga
kallon 'yan yatsun hannun Umahnah ba a hankali ya
ce min kina tsoro ne?
Na dan matsa kusa dashi na kwantar da kaina a
gefen kafadarshi nayi mishi magana a hankali ba
tsoro nake ji ba ina dai son mijina ne kawai, shiru
yayi bai ce min komai ba.

16
A mararrabar Danja ya miko min yarinya na
karbe ta ina shirin sallama dashi yasa hannu a kui6in
wandonshi ya ciro kudin da ban san adadinşu ba, ya
jawo jakata ya sanya a ciki ya zuge zib din ya fita,
bayan yasa bannu ya dauki food flaks din miyarshi
Suka yi sallama da direba da kuma Bala ya
tsallaka in da zai hau mota mu ma muka mika muka
kama tafiya.
Tafiyace ta fara mikawa sosai kewar mijina taci
gaba da karuwa a gare ni ina kara nesa dashi kewa da
kaunarshi suna karuwa cikin zuciyata.
Ban san yanda aka yi ba sai kawai naji zuciyar
tawa ta kama yin nazari da tunani cikin al'amarin
aurena da Ado wanda aka faro shi watanni ashirin da
daya da suka wUce, watanni ukun farko muka yi su a
gidan Babana, kusa da yan uwana da iyayena da
dangina watanni goma sha takwas din bayan nan
kuma tare da na shi dangin.
Tunani na sosai nayi har kafin zuciyar tawa ta
kawo ga tunanin bali da kuma irin sallamar da nayi
da kowane bangare, na rabu da Ado ne bayan ya
tabbatar min da cewar fatan shi da burinshi bai wuce
nuna min halaccinshi ba, ta hanyar tabbatar min da
cewar shi din da namiji ne.
Yayin da ita kuma Ruwaila da nata mukarraban
suma suke yi min fata da barin muna nan tare daşu
shi Adon ya nuna min cewar shi din da namijin ne.

17
To wai wancne da namiji? Ko kuma me kalar da
na miji ke nufi? Wannan ita ce tambayar da ta zo min
cikin zuciyata.
Namiji ni a sanina shi ne suna mafi daraja da
Ado ke yi wa kanshi lakabi ko kuma in ce kirari
dashi.
Sannan duk da ban taba yi mishi tambaya yayi
min bayanin abinda yake nufi da kiran kanshi da
wannan sunan ba, ni, a fahitata kalmar Namiji' a
wurin Ado yana nufin suna na cikakken mutum
jarumi mai iya fuskantar kowane irin al'amari da
zärfin zuciyarshi.
Mai tsayawa kan abinda ya sanya a gabanshi,
mai iya tsayawa ya fuskanci kowane irin wahala da
jaruntakar shi don ya zamo kariya ga na kasa dashi,
mai sanin ya kamata wanda yake iya saka alheri da
alheri.
To amma a wurin mutane kamar su Ruwailah da
masu fahita irin nata, ina ganin shi 'namiji' ba kowa
ba ne a tasu fahimtar face jarumin da ke iya danne na
ƙasa dashi.
Jarumin da bai kamata mace ta bashí amana ba
saboda bai da alkibla guda daya, yana iya canzawa a
kowane lokaci, ya manta da farko ya saka aheri da
mummuna tunda shi din kanshi kadai ya sani.
Bai kuma damu da rayuwar kowa ba sai tashi,
tunda a bakunansu dai kusan kullum sai ka ji su suna

18
Chapter 2 · 0% Book details