Sashe 12
Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
75
tsoron kar yayi abinda za a ce yayi laifin kora tunda
maganar tana gaban Baba, ba zan iya jayayya da shi
ba.
Kwanaki kadan da ya yi yana tsare a gida sai da
jikinshi ya canza ya soma yin kyau.
Rannan ne nemi Yaya Ibrahim na rasa, ban gan
shi ba baya cikin gida ba kuma lokacin Sallah ba ne
balle in ce yana masallaci.
aNa kesa buda bakina in tambayi wani shi, don
kar ya yada maganar cewar ba a gan shi ba har Ado
ko. Baba suji, don haka naja bakina nayi shiru nayi ta
leke-leke ko zan hango shi har dai na hakura.
Ina zaune tsakar gida sai gashi ya shigo layi yake
yi nayi salati mai karfi ya waiwayo ya kalle ni "Anti
Humairahhh ki shouumn kawai kin gane? Ki rabu da
wannan mugun mutumin muuu dah yah zan...
Nayi maza na tura shi dakinshi na tura mishi
abincin shi wanda sakwara ne da miyar taushen da
aka yi da kayan ciki da busasshen kifi naja kofar na
rufe shi a ciki ina ta addu'ar kar Ado ya dawo ya ce
ina yake?
Washegari da Asuba Ado yana fita Masallaci da
yake yana fita da wuri tun kafin kiran Assalatu nayi
maza na tashi naje na shiga dakin Yaya Tbrahim.
A kwance shame-shame na same shi, yayi filo da
sakwarar da na mika mishi, ko loma daya bai yi ba, a
tsorace na tashe shi ya wastsake na nuna mishi
76
abinda yayi, shima ya tsorata.
Na sa shi yayi wanka kafin ya fita Masallaci aka
yi sallar Asuba dashi ya shigo gida ya gyara dakin
nashi.
A haka ina zaune da Yaya Ibrahim kullum ina
kab-kab-kab ina kuma addu'a har nayi sa'a zaman
nau ya mike ya soma wastsakewa daga abubuwa
masu yawa.
Natsuwa ta soma zuwa mishi, har dai daga baya
ya yarda ya koma makarantar addini da ta boko.
Ado ya yarda da zamanshi a gida, ya saki jiki
dashi ya soma jan shi zuwa gona da ma wuraren
harkokinshi, har ma daga baya yake iya tura shi ya
wakilce shi kan al'amura masu yawa.
Shekaru goma cif sun cika daga wannan ranar ta
daidaituwar al'amuran Yaya Ibrahim.
Shekaru goma sha biyar kuma kenan na aurena
da Ado, auren da kaddara da rabo na abubuwa masu
yawa suka tilastawa Mama yin sanadin shi.
A yau ni din mahaifiyar 'ya'ya biyar ne cif na
Kawu Ado, cikinsu akwai namiji guda daya Baba
Yahya, sai kyawawan 'yan mata guda hudu,
Umahmah ita ce ta farko, sai Baba Yahya bayanshi
ne kuma muka samu Zainab da Khadija da Fadima.
Wadanda mahaifinsu ya zaban musu Sunayen
nasu saboda kaunar da yake yi wa yayarsu
Umahmah, don haka ya ce to tunda a tarihin da ya
77
karanta na Umahmah Zainab yar Annabin Rahama
ce mahaifiyarta ita kurma Zainab kowa yasan 'yar
Nana Khadija ce.
Sannan ita Nana Fadima sonta da take yi wa
Umahmah ne ya sanya ta bar wa mijinta wasiyyar
auren Umahmah bayanta, to bari ya jera mana
Sunayen.
Haka don neman albarkar masu sunan na ce
mishi to Kawu don haka Ado bai taba yiwa kowa
takwara ba tun bayan wanda yayi wa Baba Yahya.
Duk kuma da wadannan 'ya'ya biyar din da ke
gare ni shekaru kusan biyar ne kuma yau rabona da
haihuwa a dalilin son miji da neman gindin zama a
wurinshi ya sanya ni shiga harka ta bin tsarin iyali.
Mahaifar tawa a daure take, watakila in ban dá
haka da yanzu an wuce biyar an kai shida ko bakwai
ko ma takwas ko da yake dai ina da sani da kuma
Imani na cewar babu wani wanda ya isa ya hana wani
zuwa duniya a lokacin da kaddarar zuwanshi tazo.
Don haka na yarda nayi hakan tunda abin da
maigidan yake so in yi kenan ni kuma kullum a kan
bin ra'ayinshi nake matukar dai bai zamo sabo ba
tunda nasan ni din ni kadai ke gare shi a gida ko a
waje ba mai leke-leke ba ne.
Yanda na zamo mahaifiyar ya'ya biyar a cikin
gida, to a waje shima mai gidan al'amura masu yawa
ya sanya a gaba farko dai a yau shi din shi ne 'Dr.
78
Ado Sulaiman', don kuwa digiri uku ne da shi.
A yanzu yana aiki ne tare da hukumar inganta
ilimin makarantun primary ta kasa. Shi ne kuma
mamallakin shahararriyar gonar nan ta "HUMAIRAH
FARM'.
Wacce ita ce kadai gonar da a nan kurkusa tayi
fice wajen bayar da kayayyakin amfani irin na lambu
rani da damina, irin su (Brocooli, Beetroot,
Asparagus, Aborigine, Cabbage, Kore ja, ko na
Chinese, carrot, ganyen celery, cucumber, lettuce, da
abubuwa masu yawa da suka danganci lambu, ga
kuma 'ya'yan bishiya irin su gwanda, abarba, lemo,
gwaiba, da makamantansu, wadanda duka ana' tafiyar
dasu ne bisa tsarin nomna irin na zamani.
Haka nan wannan babbar gona ko kusa harkarta
da dawainiyarta bai fitar da Ado daga cikin harka ta
noma damina ba, wanda da shi dama ya fara.
A yanzu shi din manya-manyan gonaki ya
mallaka na noman masara, dawa, wake, ga kuma
fadamun noman shinkafa da rake wadanda mutane da
yawa suke taimakon shi tafiyarwa.
Amintattun yaran da ya rike irinsu Bala wanda
bayan kammala hada haddar Alkur'aninshi, Ado ya
trua shi ya dan karanci Boko har ya zamo ya mallakii
ilimin digiri akan aikin gona da kuma wasu yaran da
anbatonsu zai y yawa...
Ina zaune cikin katafaren gidan da sanda na yi
79
wa Ado rakiya zuwa kasar Singapore ne na dauko
sanfurinshi bana komai na aikin hukuma bayan
kanmaluwar karatuna na N.C.C. nayi aikin
karantarwa a makaran tar primary ta Dabai na tsawon
shekaru bakwai.
Ado ya bani umarnin' ajiye aikin don in zauna a
gida in yi aikin da yati kowanne dacewa da ni, wanda
yafi kowanne zamo min dole don shi ne in ban bayar
dashi baza a tambaye ni.
Shi ne aikin tarbiya, tarbiyar 'ya'yan da ke gare
mu wadanda ba biyar din da na ambatan wa kaina ne
kawai tarbiyarsu ta hau kan nawa ba, manyan
yanmata kadai guda hudu ne da ni ga Umahmah ga
Hindatu ga Nusaiba ga 'yar gidan Furerah da ta haifa
bayan haihuwarsu da shekara daya har tayi min
takwara da ita.
Da zan taso duk na hada su muka dawo a maza
kuma ga Usman sai Baba Yahya sai kuma wasu
yaran da Adon ne ya kawo su gidan to ga kuma su
Nana.
Bisa wannan dalilin ne maigidan ya zaunar dani
yayi min gamsasshen bayanin da ya sanya ni
gamsuwa da barin aikin nawa na zauna a gida nake sa
mana ido kan al'amarin tarbiyar ya'yanmu.
Ganin da yayi na hakura da albashin nawa da
nake samu wanda yasan amfaninshi wurina yana da
yawa, tunda yasan ina da iyaye da 'yan uwa da dangi
80
wadanda nake tafiyar da al'amuran da ke tsakanina
da su na zumunci ba tare da shi1 yasan yanda aka yi
ba.
Sai yaga na hakura na bari na kuma ja bakina
nayi shiru, ban taba tanbayarshi yaya za ayi ba? Ya
sanya shi yi min tukuici da gonar HUMAIRAH
FARM.
Ina zaune a falona ina karatun littafin (Riyadus-
salihin) babin godiya kan ni'imomi nake karantawa,
Baba Yahya ya shigo da gudu, can bayana ya tsallaka
ya wuce ya buya.
Sai ga Umahmah ta biyo shi a fusace, ga dukkan
alamu tsokanarta yayi, ta bude baki da nufin yin
magana fushin nata yayi tsanani, na daga ido na
kalle ta cikin natsuwa na ce mata.
"Umahmah sau nawa zan gaya miki cewar
Ubangiji yana son masu hadiye fushinsu, nan da nan
ta 'sauka, ta kalle ni cikin ladabi ta ce na hadiye
Goggo, na ce to ai kin san kuma yana son masu
yafiya, ta ce na yafe mishi.
Na ce to kuma har ila yau yana son masu
kyautatawa na kasa da su, tayi murmushi ta ce to
Goggo ya biyo ni yazo ya karba.
Tana barin dakin na kamo Baba Yahya na jawo
shi gabana, kumnenshi na kama na rike da hannuna
ina ja yana bin hannun nawa yana fadin kiyi hakuri
Goggo, na zaro ido ina kallon shi sau nawa nake gaya
81
maka ba sa'o'inka ba ne?
Sau nawa nake gaya maka da Hindu da
Umahmah da Nusaiba shekaru uku-ukı suka baka?
Don haka ka daina tsokanarsu, ka daina yi musu
rashin kunya."
Jin da ya yi na ce da jan kunnen nashi ya sanya
shi tunanin da dokar da yasan an kafa min, cikin
natsuwa ya ce Goggo Babana ya hana ki kama min
kunne saboda yana min ciwo.
Na saki kunnen nashi cikin sauri na ce, to ama ba
zai hana in saka, in saka tsallen kwado ba ai, tunda
kai baka son a tsokane ka amma ka iya tsokana. Sun
ce maka superdi ka gaya mishi ya ce kar a sake.
Sannan sun ce maka Tanko ka sake gaya mishi
ya hana, to zan gaya mishi ni da kaina ba ka da aiki
in ka zauna a gida sai tsokanar yayunka kawai kake
yi, don haka ya zabi abinda za'a rinka yi maka cikin
biyu, ko dai ya bari in rinka sa Yaya Bala yana tafiya
da kai gona ko kuma a gida Yaya Usman ya rinka
horar da kai yana saka tsallen kwado.
Cikin natsuwa ya kalle ni ya ce, kiyi hakuri
wahala zan sha in an sani tsallen kwado, nayi nauyi
da yawa, na ce to bi bayan 'yar uwarka kaje ka bata
hakuri, ya ce min to. Ya tashi ya fita.
Yana fita ya bar dakin, na amsa wayar Yaya
Ibrahim daga Kaduna, Anti Humaira ina kwana?
Nayi murushi na ce lafiya Yaya Ibrahim, ya ya gida?
82