← Book details Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 24

Sashe 17

Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda a yanzu din nan a yanda najin zuciyata, ai
ba zan iya zama da wata kishiya ba, bai yi min ita
tuntuni ba sai yanzu da na gama mike kafafuna, ya ce
in nade hanyoyi iri-iri kawai nayi ta tunanowa na
yanda zan yi in hana Ado yin auren saboda in ga
burin na Mama bai kai ga ci ba.
Sai dai tayi ta zama dashi yana cinta ita kadai a
ranta, tayi ta fama dashi tuni Ruwailah ta fado cikin
raina, kiranta zan yi in yi mata maganar tunda ni da
ita yanzu a dunkule muke, ta kuma san hanyoyin
shiga da fita iri-iri, bari dai ya kuskura ya ce min
yana neman aure, zai ga abin mamaki.
Mun soma zama da Ado a cikin wani yanayi da
shi bai san me nake ciki ba nasa ido da 'yan rahoton
da na kewaye shi da su akan dan kiris in suka ji to
suzo su gaya min sai kawai aka yi waya da daddare
kan cewar mai babban allo bai da lafiya.
Babana ne kuma yayi wayar, jikina ya dauki
rawa nan take na soma yin kuka duk da ina jin
Babana yana gaya mishi cewar a'a da sauki gashi nan
ma ita Binta tana ba shi kunu ina jin dai jikin girma
ne kawai ya yi addu'ar Ubangiji ya ba shi lafiya.
Ya juyo ya kalle ni. Mallam mai babban allo kar
yayi ciwo? In ban da mai babban allo an yi mishi kira
mai kyau gashi ya rayu cikin addini ga kuma gatan
ya'ya da jikoki a kewaye dashi an ce miki kananan
shekaru ne dashi?

109

Ya fa haura tamanin da dadewa, ban daina kukan
ba tunda a kam nasan komai tsufan mai babban alle
ina son shi ina kuma son rayuwarshi kullum fatana da
addu'ata Ubangiji ya kara mishi lafiya ne.
Miko annunshi yayi yana share min hawaye
tare da fadin sai ki himmatu muyi sammako da
sassafe muje mu dubo shi, in yaso ai daga can sai in
wuce tunda ina da tafiya a gabana.
Ke kuma in ki ka kwana sai ki dawo na ce mishi
to, amma ai gara muje da yara koda su Nusaiba ne
kawai tunda kana jin irin fadan da yayi min wancan
karon na kar in sake zuwa mishi gida ban kai mishi
yara ya gansu ba. Koda bai da lafiya in ya gansu zai
ji dadi, ya ce min to.
Kan ayi sallar Asuba mun gama komai, suma
yaran da za'ayi tafiyar dasu sun gama, Mama kuwa
naje na gaya mata na kuma ce mata ko zamu tafi tare
ta ce ina? Ba za ta ko ina ba da wannan jikin nata na
ce to.
Nayi mata addu'ar samun karin lafiya na bar wa
masu aikina guda biyu Sadiya da Tabawa sallahun
kula da Mama da sauran yaran da ke gidan, muka
Idar da sallar Asuba muka tashi.
Computer Hiace Bus mai cin mutum goma ne
muke tafiyar a ciki, dama kuma Adon ya sai min ita
ne saboda tafiya gida da yaran, ni da shi da Baba
Yahya ne a baya sai yan matan su hudu a tsakiya, sai

10
kuma Usman da dircba a gaba.
Ni kam dama tunda muka taso ban saki jiki nayi
wata magana ba in dai ba wata tambaya aka yi min
ba, lazimina kawai nake yi.
Ado yana ta amsa wayoyinshi daga wurare
daban-daban, kamar yanda dama al'adarshi take
saboda yanayin mu'amallar shi da Jama'a.
Ana cikin haka naga ya amsa wata waya da naji
ya ce ikon Allah! To muna nan akan ya na daga ido
na kalle shi banga wnai abu ba sai naji ya sake yin
wata wayar, kai Bala ka bar abin da ka ke yi kaje
gida ka dauki motata ta hawa ka debo min sauran
yaran nan kuzo ku same ni a Bauchi.
Ban yi mamakin umanin da ya yi wa Balan ba,
don nasan tsakaninsu ya wuce duk yanda ake zato,
mu'amallah yake yi dashi irin na da da uba, tunda
takai ma ya gaya min ya gayawa Umahmah cewar
Bala shi ne mijin da zai bata in har lokacin auren
yazo muna raye.
Na daga ido na kalle shi cikin natsuwa, na
tambaye shi wani abu ya faru ne? ya ce me ki ka
gani? Na ce uh'uh nayi shiru naci gaba da abinda
nake yi, shima ya kashe wayoyin nashi ya kara
gyarawa Baba Yahya jinginon da yayi a jikinshi yana
bacci wai don ya kara jin dadi.
Jimawa can sai naji ya ce min ke a rayuwari ai
ke 'yar gata ce Humairah nayi maza na ce mishi da

111

aka yi me? ya ce to kin rayu tare da uwa da uba da
Kakanni na bangaren uwa da uba.
Ki duba kiga Hajiyar Giyade irin yawan ran da
baiwar Allahn nan tayi, bara ne fa ta rasu. Nayi maza
na ce mishi eh, ai daga rasuwar tata ne ma na kara
tsorata da rashin lafiyar Mallam.
Ya kalle ni cikin natsuwa ya cc min, to ki kara
tsorata Humairah, Mallam zai yi ta zama a duniya ne,
jikokinshi na farko-farkon fa sa'o'in Inna ne,
mutumin da yayi irin wannan yawan ran ya bar
zuriya mai albarka irin ta Malla ya'ya da jikoki da
ya'yan jikoki ba a san yawansu ba.
Su Nusaiba nan duk ba yawan ranne yasa suka
san shi ba, ke kina zama kiyi nazari da tunani kan
ya' yan da suka rayu rayuwa irin tawa Humairah?
Nayi maza na daga ido na kalle shi ya ce, ni kam ai
maraya ne Humaira, tunda ban san mahaifiyata ba.
Babana ya rasu tun ban isa komai ba, a haka na
taso a tsakanin gidajen 'yan uwa da makwabta babu
wanitsayayyen da za ka gani a tsaye akan
al'amarinka, haka nayi ta dibi-dibin da nayi karatun
primary da secondary a lalace.
Saboda ina ganin wasu yaran unguwar yan
kadan suna zuwa a irin wannan lokacin ne fa Mama
tazo ta tafi dani, kafin zuwana hannun Mama ban
taba dandanar wani abu mai sunan dadi ba.
To ke fa? A cikin gatanki ki ka rayu mutanen da

112
suke sonki suna kewaye dake, don haka kar muje
gida ki samu jikinshi yayi tsanani kice zaki yi ta
rusa kuka wannan al'ada ce ta jahiliyya wacce
kuma aka hanata.
Cikin natsuwa da sanyin jiki na kalle shi na ce
jikin nashi yayi tsanani kenan ko? Bai yi musu ba
ya ce ch, gaba daya muka kama bakunanmu mnuka
yi shiru, sai addu'a kawai muke yi.
Mun isa Bauchi wajen sha daya da rabi ne na
safe saboda samnmakon da muka yi, ga kuma mota
lafiyayya uwa uba kuma shi ne mun godewa
Ubangiji ya tsare mana hanyar.
Tun daga karya kwanan layin runfuna ne a
kakkafe, Jama'aa ciccike har lokacin kuma Jama'a
isowa suke tayi, jikina ya dauki rawa kar-kar-kar.
Ado ya kama ni ya rike a jikinshi.
Kiyi hakuri Humairah, tun a hanya an gaya min
Mallam lokacin shi ya yi, ban gaya miki ba ne don
kar tafiyar ta zamo mana mai tsanani da yawa, kiyi
kuka ta hanyar zubar da hawaye ba laifi ba ne,
amma kar kiyi wani abinda ya sabawa Shari'a.
Tunda kullum a cikin karatu ki ke, karatu na
addini. To shi karatu da ki ke ganinshi yanda duk
ya kai da yawa to bai da wani amfani matukar mai
shi din ba zai yi aiki da abinda ya sani ba.
Shi yasa ma sai aka ce mana babu wani sani sai

113
wanda aka yi aiki dashi. Ade yana yi min
wadanan bayanan tuni ni kam awaye da majina
zuba kawai suke yi min.
Jama'a suka tartaso don ganin isowar Ado,
suna yi mishi sannu da zuwa Alhaji, barka da
isowa, abin da suke fada mishi kenan yana
amsawa, amma hankalinshi yana kaina, na yanda
zan yi in wuce cincirindon Jama'ar da ke zaune in
shiga gida.
Rike Mamanku Nusaiba, tayi maza ta kama ni
ta rike ungo jakar nan Hindatu, itama ta karba, to
maza Umahmah kuje. Haka muke wuce in na wuuce
inda maza suke 'yan uwana suka atre ni don an riga
an ji isowata.
Muna shiga gida na saka kuka sosai sai dai ban
yi ihu ko wani abin da ya saba ba, na riga na sani
ihu ko sabo ba zai dawo min dashi ba, ba zai
amfanar da mu da komai ba šai dai ma ya zame
mana wani sanadi.
Ubangiji ya gafarta mana.
"Sannu da zuwa Hajiya." Mafi yawan mutane
abinda suke fadi kenan, ina amsawa. Manya kuma
da suka fi kowa sanin abinda ke tsakanina da mai
babban allo suna ganina cewa suke yi.
Uh uhun, sai hakuri Humairah, yau kin rasa
Mallam, wannan maganar ita ce tafi komai Rara

114
tayar min da hankali ia karyar min da zuciya gaba
daya gidan a cike yKe har tsakar gida babu masaka
tsinke.
Tabarmi ake ta shisshimfidawa saboda iyali
sun riga sun hadu. amma kowa yana cikin
natsuwarshi babu koke-koke, babu maganganu a
koma gefe ana ta hira ana ba da labari a gidan
mutuwa.
Kowa cikin natsuwarshi yake, in ma yana
istigifari ko salatin Manzo ko kuma yana zaune
cikin jimami saboda yasan tilas watarana shima
zata zo kanshi.
Dakin Hajiya 'yar dubu na fara shiga can kusa
da ita naje na zauna saboda tana hango ni ta shiga
kokarin samar min wurin zama a kusa da ita din,
kama ni tayi ta rungume a jikinta tana fadin sai
hakuri, sai hakuri sai hakuri. Bar kukan haka kuyi
tayi mishi addu'a,.
Ina share hawaye ina ce mata ban gan shi ba ne
Hajiya da na ganshi wata kila da ya gaya min wani
abu, ta ce da kin ganshin ma maganar guda daya
ce, ita yayi ta nanatawa kuyi hakuri da gidajen
aurenku, kuyi bakuri da zumuncinku, bai fadi
komai ba bayan wannan.
Ranar da mijinki yazo kuwa lafiyar shi kałau
sun kai awa biyu a falon shi su biyu ya hana a shiga
Chapter 17 · 0% Book details