Sashe 18
Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
115
bayan tafiyar nashi ne ya soma kukan ciwon kai
ashe tafiya ce tazo ban cewa Hajiya 'yar dubu ban
san Ado yazo wurin mai babban allo ba, shiru
kawai nayi.
Yan uwa suka yi ta baro in da suke suna zuwa
yi min ta'aziyya da na natsa nima sai na mike naje
na yi wa wadanda suke gaba dani lokacin ne naga
inda su Nusaiba suka yi masauki, wurin Hajiya
Kubrah.
Anyi zaman makoki kwana uku amma Jama'a
sai tururuwa suke yi suna ta isowa a cikin gida ana
ganin kamar za a kara zuwa bakwai sai kawai
Alhaji Maikudi ya shigo ya kara gaida Janma'a ya
ce to yau kowacce ta shirya ta tafi dakinta ya isa
haka.
Duk inda muke ba zamu fasa yi wa Mallam
addu'a ba, har sai ranar da tamu tazo ta same mu,
muka ce haka ne.
Muka tashi daga gidan rasuwa muka bi Inna
zuwa gidanmu, can ma gida yayi matukar cika
saboda su Bala da yara sun iso har iyayen Balan ma
Sun zowa Ado ta'aziyya, ga Yaya Ibrahim da
iyalanshi gaba daya, ga su Ruwailah har da su Baba
Tanimu.
Ga mutanen arziki kawayena da a yanzu nake
mu'amallah dasu matan abokan Ado, Babana va
116
shiga dawainiya da Jama'a, Zubaida ma haka, tun
da ita kam Sa'a can dakinta ma ta sauka gaba daya.
Shigowa nayi wurin Inna na samu Kawu Ado
da abokinshi na tuntuni, Mallam Umar wanda
yanzu shi da Inna babu wanda yasan tsakaninsu,
saboda mu'amallar dukiyar da suke yi.
Suna zaune kan shimfida a kasa su biyun ita
kuma Inna tana daga can cikin daki kusa da bakin
kofar dakin tana rike da labulen don ta rinka
hangen su don suji dadin maganar da suke yi.
To mutuwa kam ba an riga an yi ta ba, Mallam
Umar sai yasa a fasa abin da aka sa a gaba? Ya ce
a'a Inna a dai bar shi a hakan kawai na juya na fita
na basu wuri cikin zuciyata dai ina mamakin abinda
aka sanya a gabad a ya sanya Inna fadin mutuwar
Mallam ba za ta bana ayi ba.
Nasan lalle yana da muhimmancia wurinta.
Kwananu biyu a gida na kwashe iyalina muka
koma gida muka je muka samu Mama wacce ba sai
na tsaya fadin mutuwar Mallam tayi matukar
faranta mata rai ba, a zuciyata na ce uhun murnar
mutuwa kam ma ai murnar banza ce, tunda kai ma
mai murnar ba ka tsira ba, wani naka ma bai tsira
ba.
Kwananmu biyu da komawa, Ado yayi
tafiyarshi wacce dama zai yi rasuwar Mallam tasa
117
ya daga, ni kam ina gida tare da iyalina tunda
Mallam ya rasu na kara maida komai ba komai ba.
Kullum sai na tuna shi, na tuna kalamanshi
musamman nasihohinshi da mafi yawancin lokaci
yake yawan nanatawa, wannan duniyar ai ba komai
ba ne, dan dadinta kuma takaitacce ne.
sAl' amuran cikinta kuwa in har kana da hankali
to na tsoratarwa ne, ina iyayenmu suke? Ai muna
kallonsu suka kare ba mu yi komai ba don ba mu
da ikon yin to haka randa tazo kanmu to gashi
kuwa tazo din yau baya nan.
Duk yawan iyalinshi kuma taruwa kawai muka
yi muka yi kuka muka tashi wannan kadai ya ishi
bawa tsoro.
Sati biyu da tafiyar Ado ya dawo ya kwana a
gida gari ya waye daga ni har shi ga dukkan alamu
muna cikin jimami don 'yan abubuwan da suka
gudana a tsakaninmu duka babu wani matsanancin
nishadi a ciki.
Tun kwanaki fa naso muyi wata yar magana
da ke rasuwar da aka yi ne yasa na dakatar da
al'amuran zuwa wannan lokacin.
Na zuba mishi ido ina kallonshi cikin natsuwa
da sauraro. Sai naji ya ce min kin san abokina na
ruwan bungo da matanshi da iyalinshi duka na ce
mishi eh, ya ce ke da kanki ne kike gaya min cewar
118
suna da kokari wajen kula da tarbiyar 'ya'yansu, na
ce haka ne.
Ya sake kallona cikin natsuwa ya ce min, to tun
kwanakin baya kamar sati shida da suka wuce nayi
mishi waya na ce mishi in akwai yarinya budurwa a
gidanshi ina so.
Abinda naji a zuciyata yafi karfin a kira shi
faduwar gaba, na dai daure kawai na zuba mishi
ido ina kallonshi cikin wani yanayi da ban tabbatar
ba a-farke nake ko a mafarki nake oho?
Ni da ke muna da fahintar juna, kanmu a hade
yake bamu da wata matsala a tsakaninmu, yarinyar
da zan kawo ba wata yarinya ba ce da ba ki san
tarbiyarta ba, kin san iyayenta kin san komai dinsu.
Har ma kuna mutunci ke da su.
Yar wajen Hannatu ce, bana so ki dauki wani
abu da tsanani ko kiyi tunanin saboda wani zan yi
musamman da yake na sha gaya miki cewar ina son
mata biyu amma ba zan yi ba, sai adaidai lokacin
da ke da kanki za ki shaida cewar nayi miki adalci.
Ban san yanda aka yi ba, sai kawai na tambayi
Ado to adalcin me kayi min a yau da zaka kawo
min ita? Ban san shi ba in kuma akwai shi nuna
min shi.
Shiru yayi yana kallona, bai tanka ba, tuni naji,
wani abu yana motsi cikin Jikina daya sani
119
shure mishi abin karyawan nashi da kafata na mike
tsaye ina fadin, ai tuni nasan abutarka da Mallam
Haruna in ba sa'a nayi ba tsiya zata zame min.
Baka da hira sai ta ya yanshi ni ina nasan su
balle in san wata tarbiyar su da ka ke cewa na gaya
maka? Ina ruwana da su, Mama ce ta saka kayi
aure don burinta ya cika ba kuma zai cikan ba a
haka zata mutu.
Kar ki zagi Mama Humairah, saboda bana so
kiyi sanadin da maganar zata lalace a tsakaninmu,
kar ki neme ni da fitina tunda ni ba ita nake nema
da ke ba.
Ki bari mu tafiyar da al'amuranmu yanda muka
saba yi saboda yaran nan sun riga sun fara wayo
bana so su shaida wani sabani a tsakaninmu.
Na mulmulo wani irin mahaukacin ashar irin
wanda ban taba ba na antakawa yaran na ce su
sheda komai, saboda ka shirya cutata wannan
mutuwar tsohuwar tasa ka kayi aure mugu...caraf
yayi ya kama min baki ya rike, yana sakin bakin
kuma ya faska mishi mari.
Kafin ta sa ni auren wata ai ta sani aurenki,.
kenan ba yau na fara yi mata biyayya akan aure ba.
Hannu biyu na saka na kama rigar Ado na rike
na ce to a saken kawai tunda ai bayan umarnin
aurena ta baka umarnin sakina sake ni kawai a yau
120
kowa ya huta.
Kama hannayená nayi yá tattara su wuri daya
ya hada su a jikina, ya hankada ni nayi tsalle na
kife can gefe. Ya kama hanya yayi tafiyarshi
Ana cikin haka sai ga su Ruwailah sun iso da
su Furerah, Jama'ar cikin gida gaba daya sai 'yan
kadanne ba su zo ba, gaba daya labarin auren Ado
ya bazu ko'ina.
Don haka suka zo su jajanta min al'amarin
tunda su din a yau nawa ne a bangarena suke.
Muna zazzaune jungum-jungum gaba daya mun
buga uban tagumi, kowa da lissafin da zuciyarshi
take yi, na hanyoyin da zamu bi auren ya wargaje
kafin ranar daura shi.
Sai da Sa'adatu ta iso tana rike da hannun
danta sun sha kwalliya sai walkiya suke yi. Hajiya
sannu da zuwa, suka soma gaishe ta tana amsawa a
lalace, a wulakance na zuba mata ido ina kallonta.
A zuciyata ina tambayar kaina dama yarinyar
nan ta iya yi wa mutane irin wannan wulakancin r
ni ban sani ba? Wai ita matar me kudi ko? To bari
Ana gama gaisuwar ta mike ta nufî can cikin
daki ta bar mu, don haka muka ci gaba da tattauna
al'amuranmu irin masoya sai gata ta sake fitowva
fuskarta a murtuke kai duk ku watse ku bar gidan
nan ko kuma in kira Yaya Ado in gaya mishi
121
abinda naji kuna tattaunawa a kai.
A fusace na ce mata, ke Sa'a za ki ci mutuncin
mutanena ne a gabana? Kina hauka ne? za ki kawo
min iskanci ne da rashin kunya? Nan da nan ta
kama kuka haba Anti, kishiya musiba ce? Da in
za' ayi miki ita sai ki birkice ki fita hankalinki ki
tara mutanen da zasu yi miki karya?
Su wacece bata da kishiya a cikinsu? In kura
tana maganin zawo tayi wa kanta mana, kin san ki
ga yawa wani gaskiya ya ji amma in gaskiyar tazo
kanki ba za ki iya aiki da ita ba?
Na wanke Sa'a da mari mai kyau saboda
maganganun nata sun zama rashin kunya a wurina.
A'a-a'a to mu kam barî mu tafi, su Ruwailah
suka soma zare jiki suna shiga suna gaida Mama
daga can kuma sai su wuce, ta sake kallona cikin
natsuwa ta ce min.
Sai dai kiyi hakuri Anti, ko kuma ki mike kiyi
ta dukana amma zan gaya miki cewar wannan
kishin naki bai dace da ke ba, don kuwa yafi kama
da kishi irin na jahilan mata, ba matan da suka
karanta addini suka san shi ba.
Ita kaddara yarda da ita ai sharadi ne na cikar
Imani, kaddarar kuma wacce ka ke so ne da wacce
ba ka so, kan ayi miki kishiya ai Anti Aliya aka
fara yi wa ba kya nan ne lokacin yasa baki ga bukin
122