← Book details Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 24

Sashe 15

Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ke tafi can ni ki bani wuri da fitinarki ta tsiya,
ke yanzu ai na riga na gane ki gaba daya burinki bai
wuce kiyi min abin da hawän jinina zai tashi ba ya
karasa ni in mutu, in yaso burin uwarki ya cika a
kaina.
Na kalli Mama nayi murmushi na ce lnnata ai
bata da sauran buri akan ki Mama, tunda gidan da ki
ke yi mata gadara a kanshi kina fadin naki ne ya
zama nata, mijin da ki ka kwace mata gashi can kin
baro mata shi saboda ya gagare ki.
Nan kurna da aka dawo aka zauna nawa ne, tunda
mai kishiyoyi da 'ya'yan miji ma takan nishadi in ta
samu wuri ta ce gida da mnijin nata ne ita kadai balle
ni da ni kadai din ce.
Mama ta kama kuka, Suwaiba kuma ta kama
maganganu ba dai ita kadai ce a gidan ba wooo! Na
ce ai ita bata dame ta ba, ba kin san gidan ba? Ai kin
san bata kishi da ita.
Ai Inna bata da sauran kishiya, dama Mama ce
matsalarta, tun kuma daga ranar da tayi kuskuren kin
jin kashedin da masoyanta suka rinka yi mata, ta
dauki Ado ta danka min shi a hannuna da nufin
zaluntar uwata, nayi wuf na kama shi na dunkule shi
wuri daya na dankawa Innata shi bata sake zamowa
matsalarta ba.
Na wuce su nayi tafiyata cikin zuciyata ina fadin
Mama dai kam yau na zage ta duk abinda Ado zai yi

96

kuma sai yayi kawai mu gani.
Ban dade da fitowa daga dakin nasu ba sai ga
Suwaiban tazo ta wuce ni ta fita nayi waya na ce wa
maigadi ya kulle gidan kar wanda ya sake shigowa
kowane ne sai an gaya min, ya ce min to.
Sai da aka yi sallar magariba Suwaiba ta dawo
maigadi ya ki bude mata kofa tayi juyin duniya ya
ki, Mama ta turo keken ta na guragu don bata riga
tayi karfi ba tukuna, tazo ta same shi ka bude mata na
ce.
Cikin stawa take ba shi umarnin, ya ce Goggo ce
ta ce kar a bude, tayi-tayi abin ya gagara sai ga ta a
kofar dakina na ce kisa a bude wa Suwaiba gida ko?
Cikin tsawa tayi maganar na ce to, ba ta kuma
zaci to din zance ba na kali Hindu na ce mata jeki ki
ce wa solori ya bude mata kofar, tana gaya mishi ya
bude, Suwaiban ta shigo.
Muna nan a haka Suwaiba bata sake fita ba don
tasan taná fita zan sa a kulie har Ado ya dawo,
shigowar dare yayi na kuma riga na shiryawa zuwan
nashi, don sabuwar kaza ce a jikina.
Kwanaki uku kuma kenan tunda naci ka riga ta
jika a kidime kwarai ranar ya kwana, Humaira, na ce
mishi naam ya kara matsowa jikina va kankae kina
da wani sirri a tare da ke Humairah da wani lokaci ki
ke kidiar da ni, ki rinka sanya ni ina jin tanfar dai ke
din budurwa ce.

97

Shiru nayi ban tanka mishi ba.
Washegari da safe sai da na slirya mishi abin
karyawanshi ya gama komai ya yi wanka ya kintsa
aiken Mama biyu ta waya wai tana son ganinshi,
amma bai samu fita daga dakin nawa ba sai gab da
azahar.
Don haka sai da yaje yayi Sallah ya dawo sannan
ya shiga wurin nata, ya dan dade kafin yayi waya wai
in je.
A dakin na same su ranshi a 6ace kwarai da
alamar ya ji maganganu iri-iri, amma duk da haka ya
kalle ni saboda kwalliyar da nayin yasan táshi ce.
Meke faruwa ne Hurmaira? Cikin natsuwa na ce
mishi kamar me? ya ce ina nufin mc ya hada ki da
Mama? Nayi maza na ce babu komai.
Mama tayi maza ia ce ba ki zagen ba za ki ce
mishi babu komai? Suwaiba ta ce wai ita ga
mu...Ado ya yi maza ya katse ta in ki ka zage ta a
gabana ranki zai 6aci, na kalle shi cikin natsuwa na
ce mishi.
Ni babu abin da ya hada ni da Mama tunda ba
abokiyar magana ta ba ce, uwata ce kai ne ka ce in
wani abu ya faru tsakanina da Suwaiba in daina gaya
maka, in kawo kara wurinta zata tsawatar mata.
Ya ce haka ne, na ce to karar na kawo sai
Suwaiba tayi min rashin kunya a gabanta nayi mishi
bayanin komai har kawo kan abin da ya faru duka,

98

sai dai na ki yarda da cewar ni maganganu da Mama
nake yi na ce da Suwaiba ne.
Ado yayi shiru na lokaci mai tsawo saboda
ranshi ya 6aci kwarai, don kwa ko ban amsa da
Mama nake yi ba ai shi ya ji abinda na fadan sai dai
kuma nasan zai san ita Mama ita ta fara tsokanata.
Shiru yayi cikin matsanancin tunani, yayin da ni
kuma nayi shiru cikin natsuwa ina sauraron abinda
zai ce, sai Mama ta fara yi mishi bayani, ita
Humairah bata gane ba ne ita so take duk wanda zai
zauna a gidan nan sai ya yarda ta maida shi talolo
kamar yanda ta maida wannan yaron.
Ado ya daga kai ya kalle ta ya ce wa Ibrahim?
Tayi maza ta ce ebh, shi to ita kuma Suwaiba ba za ta
yarda da hakan ba, don ita ba sakarya ba ce irin shi,
-ba ruwinta tazo ba ba don ita tazo ba.
Tunda gidan nan ba nata ba ne ita da yan
dakinsu da zata ce sai ita da su ne za su zauna a ciki,
gida ai naka ne amma take bugun kirgin nata ne yayi
maza ya katseta ba bugun kirjin bane nata ne kuma
tunda suwaiba tace ba wurinta tazo ba.
Kema kin fada ba wurinta tazo ba, to ta bar mata
gidanta kawai, azo a zauna a gida ace ba wurin matar
gida aka zo ba wurina aka zo'ni mazaunin gida ne?
Humairah ai bata adawa da 'yan uwanta, Mama
da ke take yi shi yasa da ta samu damar gaya mii
magana ta gayaa miki, ba kuma zan kyale ta kan

99

rashin kunyar da tayi miki ba.
Ai ta zauna da Ibrahi babu abinda bata yi mishi
ba, ta kuma zauna da Kaltume da ya'yanta tsawon
wata goma bata ji ko ganin wani abu mara dadi ba,
saboda bata da matsala dayan uwanta. Don hakka
Suwaiba suna da gidan uba ta koma can ta zauna.
Mama ta ce uhun, za ka kore mu dai kawai tunda
kasan hakanne zai fi yi mata daidai, ai kaima kasan
ba zan zauna a in da Suwaiba ba za ta zauna ba in dai
ka ce ta tafi to tare zamu tafi.
Ya ce to shi kenan Mama, in kun ga hakan yafi
miki sai ki bita ni dai nasan ban ce ke ba amma
Suwaiba kam a gabana ta amsa ta ce ba wurin
Humairah tazo ba, to in wurina ne ni bani da gida
zaman nata ya isa haka ta tafi kawai.
A ranar Suwaiba ta tafi, ina jin Mama tana gaya
mata inda zata, wai kar ta ce gidanmu ban san yanda
aka yi ba sai kuma gata ta gama bin dangi ta gaji ta
koma gidan namu.
Ta bude dakin Maman ta shiga ta zauna ita
kadai, Innar tawa kuma ita ce dai mai daukar
dawainiyartata.
Barin Suwaiba gida sai Ado ya dorawa diyarshi
dawainiyar baiwa Mama magani da safe da yamma
tunda da rana kam bata nan tana makaranta, sai ni in
je in bata.
Tunda Ado ya dorawa Umahmah wannan

100

dawainiyar ya hadata da aiki saboda kullum taje
baiwa Mama magani tunda ba maganin ba ne kawai
sai ta motsa mata jiki, to bata fitowa sai da kuka.
Tunda ba za ta gama ba sai ta jawo wata sanda da
ta sunne a gefen gadon nata ta rafke ta dashi wai tayi
mata mugunta.
Kullum tazo ta gaya min zante mata to kiyi
hakuri Umahmah ai kin san bani na saki wannan
aikin ba ko? Ta ce min eh.
Rannan ina dakin Ado da rana saboda yazo gida
week end na kalli agogo na ce mishi bari in je in
baiwa Mama magani lokaci ya yi, ya ce a'a babu inda
za ki yanzu Umahmah taje ta bata na ce ishi to.
Sai ga Umahmah ta dawo tana kuka da iyakacin
Rarfinta, sallama biyu tayi kafin Ado ya bani izinin
amsawa da bata umarnin shiga inda muke din.
Durkusawa tayi a kasa tana cewa, Baba ka
taimake ni ka ce ni da Hindu da Nusaiba ne zamu
rinka baiwa Mama magani da motsa jiki, kowa sau
daya a wuni tunda su ba ta dukansu. Amma ni
kullum sai ta buge ni.
Da sauri ya ce duka Umahmah? Ta ce ch, ka
gani? Yanzu ma ta buga min sanda a dan yatsana
yayi maza ya kama hannun nata yana dubawa ban
san abin da ya tuna ba sai kawai naga ya yi
murmUshi.
Ya ce, Mama kenan, ba kya iya tashi kiyi komai
Chapter 15 · 0% Book details