← Book details Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 24

Sashe 20

Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

129
kasafai ka ke ganinta a waje ba.
Taro ya tashi, Jama'a sai iatiya suke tayi saura
wadanda suka rage saura kadan Hajiya Kubra ta
shigo wurina tana murmushi, yau uwarki har da
goggoro ta daura.
Nayi maza na tambaye ta wacce a cikin iyayen
nawa? Ta ce wacce uwa ke gare ki da ta wuce
Mama? Na tsuke fuska na ce Mama kuma Hajiya?
Tayi maza ta ce eh, ita uwarki ce kar kuma ki yarda
ki biye mata akan komai.
Kiyi hidimarki kawai, wannan yarinyar kuma kar
ki yarda kuruciyarta tasa ki zalunceta, shi kuma
mijinki ki kara mutunta shi don ki karawa kanki
girma da daraja albarkar 'ya'yanku ma ta karu, na ce
to Hajiya na gode.
Dare yayi babu kowa a gidan, ina kivance kan
gadona tun bayan fitar Ado daga dakin da yazo yayi
min sai da safe, ban iya motsawa na tashi naje na
kulle kofar tawa ba, sai kallon agogo kawai nake yi
ina lissafin cikin zuciyata a sanin halin Ado da nayi
yanzu ya gama kaya ne yana yin kaza.
Ina cikin haka ne kawai naga yarinya ta fado min
daki da gudu a firgice kwarai take, tayi matukar
tsorata da abinda ta gani, tsallake ni tayi ta wuce can
bayana ta makure wuri daya.
Na waiwaya na kalle ta, 6ari take yi kar-kar-kar
daga ita sai yar wata lalatacciyar shimi ne a jikinta,

130
ga nonuwanta nan ba suma karasa fitowa sosai ba,
Yarinya ce 'yar karama da ba ta wuce shekara sha
hudu zuwa biyar ba.
Kamar dai ace sa'ar Umahmah, kyakkyawar
yarinye don kuwa zafin kishinta bai iya rufe min ido
ya hana'ni ganin kyan nata ba. Na tuna sanda dima.
nawa nonuwan suke kamar nata..
Cikin zuciyata na co, kai lalle Ado! Ado nabaiji
ne, yau ne na gane me yake nufi da yawan ambaton
kanshi namiji da yake yi, sai gashi ya shigo yana
daure da rigar baccin da ke jikinshi da belt
Muna hada ido dashi ya sakar min wani lallausan
murmush, a zuciyata na ce shi ma yasan ya cuce ni,
ya gama de ni.
To zomarna Humaira, ya juya ya fita ban yi
jayayya da shi ba na bi bayanshi zuwa tsakar gida
dan fito min da yarinyar nan sai ki auro kofarki, ki
kulle, ai dare yayi me ki ke yi har yezu idenki biyú?
Na harare shi na çe, kai vie ka,ke yi? Yayi.
murmushi ya ce to naji fito mii da ita don kin ga na
riga nayi niyya zan shiga dakinta. Na ce toai bani na
kawo ta ba, ka shiga ka dauke ta mana.
Cikin natsuwa ya ce ina jin kunyarki ba zan iya
ba, shi yasa nake so kiyi in adalci ki bani ita. Na
wuce shi naje nayi kwanciyata gabana sai faduwă
yake yi, kar dai Adó ya shigo min dakin nan ya ce zai
fitar da yarinyar nan don ban san abinda zai faru ba.

131

Sai aka yi sa'a har gari ya waye bai shigo ba, sai
dai kuma in bata jin zirga-zirgar, shi nayi zaton ko
lemon tsami yake nema da jar kanwa bai samu ba.
Washegari da safe na kammala abin da zan yi na
sallah da jan carbina na mike zan fita don shiryawa
yara abin karyawa da tafiyarsu makaranta.
Sai na kalli Bilkisu na ce mata ke je ki đakinki
kin ji, yanzu ba zai zo miki ba balle ya taba ki tunda
gari ya waye ta ce min to.
Tuni su Nusaiba suna kicin suna kokarin
kammala komai, don sallamar kannensu kafin suma
su sallami kansu, saboda sun riga sun saba ko ban
fito ba ba za su yi komai don haka ina shiga akan
kammala suka gama suka tafi.
Suna fita suka bar gidannan sai kawai na hango
wucewar Ado zuwa dakin yarinyar nan kan kace
meye wamnan sai kawai na jiwo ihunta akidime.
Jikina ya rinka rawa nayi matukar kidia na gigice
na rinka jin tanfar wani abu yana yi min yawo a jiki,
ya rasa hanyar fita, waiyo! Wayyo!! Wayyo!!! Abin
da kawai nake fadi kenanz uwa can nayi sa'a wani
tunani yazo min na bar waiyo na koma 'lahaulah'.
Ban san tsawon lokacin da na dauka ina cikin
wannan kidimar ba, sai kawai na ji ni jike sharkafda
gumi, na mike naje nayi wanka na yiwo alwala nayi
nafila raka'a hudu nayi addu'o'i na shafa na zauna
gaban madubi ina shafa mai ina kallon kaina a

132
madubin.
Ko da bani da nonuwa a tsaitsaye i din kuma ba
zai yiwu ace Ado zai yi wuju-wuju dani ba, a cikin
ganiyar kuruciyata nake na kuma riga na zaina mace
mai daraja wato dai mata irin na zsmani da kana
ganinsu ba sai an tsaya yi maka bayani ba.
Don baka na tsayarwa raina da cewar da wuni in
wani ya ce bai sonka to lokacin ne wani kuma zai ce
shi da kwana yake kaunarka, don haka ba zan
lamunci irin wannan matsanancin bakin cikin ba
daga gare shi, don zai iya nukurkusani ya karya min
zuciyata.
Kwalliya sosai na tsaya nayi ba don komai ba, ba
kuma don kowa ba sai don in tabbatar wa kaina
cewar kuruciyar da nake kirawa kan nawa tana nan.
Daga ido nayi na kalli agogo da nufin in ga
lokaci don fitar da nake son yi in bar gidan ya gama
abin da yake a dakin ya fito bai same ni ba, sai kawai
naji gabana ya fadi
Sha daya da rabi ne lokacin dora abincin ranar
gidan yayi, gashi mai girkin bata zo ba, na ce tay1
hutun kwana biyu don ta huta wahalar hidimar da aka
yi kenan, in har ban tsaya ni nayi girkin ba yara za su
dawo gida basu samu abin da suka ci ba.
Kan haka na fito na shiga kicin na soma aikina
abincin gidana bakina da zuciyata basu daina
ambaton lahaula' ba.

133
Duk da ban shiga kicin din don kowa ba sai don
yaran da nake gudun kar su dawo gida basu samu
abincin da zasu ci ba, ban kuma iya yin girkin yaran
kawai na fita na bar sauran mutanen gida ba.
Don ban saba ba, ba kuma zan iya barin iyalin
gidana da yunwa ba, don haka sai kawai na shiga
aikin girkin sosai, gefe daya ina yin dafaduka mai
hade-haden kayan lambu gami da naman rago a ciki.
Daya gefen tuwon shinkafa ne miyar agushi,
wanda nima shi nake sa ran zan ci don in rage
matsananciyar ramar da nayi a kwanakin maganar
aurennan zan ci abincin girki na kwana biyu.
Na sake yin farfesun kayan ciki da na yi wa hadi
sosai na kuma yi na kaji saboda Balkisu, a dalilin
nanata min da zuciyata take yi cewar ita yarinyar bata
yi min komai ba, bata da wani laifi a wurina, ba ita ta
kawo kanta ba, ba ita taga mijina ta ce tana so ba.
Sannan kwata-kwatanta bata wuce Umahmah ba,
ashe kuwa ko don Umahmah ta samu wadanda zasu
yi mata adalci a rayuwa zan yi wa Bilkisu.
Na hangi fitowar Ado daga dakin ban san sanda
bakina ya ce mishi dan iska ba, sai da na tuna mijina
ne nayi maza nayi tayin istigfari.
Yara suka shigo da gudu suna murnar ganina a
kicin din su, na shiga zuba musu ina mika musu da
kananan na fara kafin na is kan nmanyan.
Ado ya shigo ya same ni ina magana da su

134

Umahmah dukansu saboda na lura in ba yi nayi da
gaske ba shiga za su yi cikin lamarin da ba nasu ba
ne, suyi kane-kane.
Babu wani zumudin bukin da suka yi sai ma da
Sa'adatu tayi musu kaca-kaca ne suka je suka yi
kwalliya.
v Nusaiba ai kun san Babanku yayi aure ko? Hindu
ta ce eh Goggo, amma ai mun girmeta ma, na rage
fara'ata na ce uwarku ce, ko kun girme ta zaku
girmamata don matar Babanku ce, balle ma ba ku
girme ta ba, za dai kuyi sa'anni ne kawai.
a Ina maganar ina zuzzuba musu farfesun a
kwanuka daban-daban ina ajiyewa, ga kuma abincin
shima duk na zuba musu shi na sake bude oven na
dauko wata katuwar kaza da na yi wa gashi na
musamman na hada na sake jawo flask na cika da
ruwan tea mai citta na ce ku diba kuje ku same ta
bakuwa ce ku sata taci abinci ta kuma sha tea suka ce
to, suka diba suka tafi.
Ado ya matso kusa dani, nawa abincin fa? Ban
iya yi mishi magana ba, na dauki na Mama na tafi
wurinta sai da nayi sallama sau biyu bata amsa ba,
nasa kai na shiga tunda nasan tana ji na.
Sannu Mama, ta ce yauwa sannu kadai, ta bude
ido sosai tana kallon irin kwalliyar da nayi, na zauna
ina bata abinci, Ado ya biyo ni yana tambayata ina
abincin shi? Kan in yi magana Mama ta ce mishi har

135
Chapter 20 · 0% Book details