← Book details Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 24

Sashe 22

Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zai tafi, ta ce to me zata yi miki a gidan ba shi ita
kawai ya tafi da ita, ai kawaici yayi miki kin ga kumnà
ki sata ta bishi da kanki yafi ace shi ne ki ka kure
hakurinshi ya ce zai tafi da itan.
Ko ba zai iya yin hakan ba ne? na ce zai iya
wanda yafi wannan a ta ce to kin gani.
Duk da bana son tafiyar tasu tare na daure nayi
abinda Innan ta ce in yi.
Dadi yayi matukar kaa shi sai dai ya daure ya
hadiye ya biyo ni dakina yana muzurai, to tunda kin
ce dole sai an tafi da wannan yarínyar ai sai kije ki ga
shirin nata wannan wani shiri zata iya? Na ce mishi
to.
Duk da ni na ce ayi tafiyar tare da ita bayan
tafiyarsu kuka nayi tayi, to ina ga in da shi ne kawai
ya zartar da hakan? Bayan tafiyar tasu ne Innan tayi
min waya don jin lafiyata, na ce mata sun tafi Inna
amma nayi kuka.
Tayi murmushi ta ce share hawayenki ki
wastsake babu wani abinda zai je ya yi har ya kusa da
kusan-kusan abinda yayi miki, ko yake yi miki a
yanzu. Na ce Inna kenan, ta ce eh ai gaskiya ce kawai
mai ita kuma yana iya yiwa kanshi hukunci.
Sai mutum bai cin zamaninshi ya hana wani cin
nashi zamanin, ai kin ci naki Maman Umahmah kina
a kai tunda me akai da maza? Don haka itarna barta
taci irn nata saboda naki zamanin vavi tsawo ya

142
kuma yi karko mai kyau.
Amma menene? Me zai je yayi sabo? Wane dare
ne jemage bai gani ba? Ai sai na ranar mutuwarsa ke
ce fa aka bashi ke yana da shekaru talatin kina da
shatara, kin san muhimmancin shekaru talatin wurin
da namiji kuwa shekaru ne na kamala da cikar
halittarsa.
Shekaru ne na ganiyar karfi, shekaru ne na
abubuwa masu yawa da ba zai yiwu in yi ta lissafo
miki su ba, sannan a wancan lokacin bai da wani
nauyi kece ke kadai, bai da wani uzuri sai naki, bai
da wata bukata sai taki, bai da wani abinda yake so
sai ke gaba daya lokacinshi naki ne, gabba daya
hidimarsa taki ce.
Ba yanzu da ya riga ya gama mallakar
hankalinshi nauyin Jama'a da kuma abubuwa masu
yawa suka hau kanshi ban da haka kina ma da wasu
darajojin a wurinshi ke kadai ce zai yi surukata da
uwarki irin surukutar da yake yi dani ba zai sake
yiwa uwar wata hakan ba.
Saboda ya riga ya girma sannan ban da
wadannan duka sai kuma ki ka yi sa'a ki ka zama
kece ki ka zamo mishi uwar Umahmah, ki ka sake
zuwa ki ka haifan mishi Baba Yahya.
Ko wadannan biyun kawai ki ka tsaya akai ai kin
san kin haifi abin da yake so, to balle gasu Zainab, ga
Khadija ga Fatima, don haka kar ki yarda ki mance

143
ni' imomin da aka yi miki kije kina sa ido kan abin da
bai taka kara ya karya ba.
Kullum ki tasa al'amarin ya'yanki a gaba kar ki
zalunci dan kowa balle sakaiya ta taba miki yayanki,
nayi aza na ce to Inna.
Kullum kalaman Inna suna kwantar min da
hankali su sanyaya min zuciyata su kara min son
ya'yana da ganin darajar su, ba.wai son 'ya'ya irin
na rashin kwaba ba, a'a son 'ya'ya irin na hakura da
abinda ka ke so ko yin abin da baka so saboda su
saboda rayuwarsu ta gaba ta inganta.
Kalaman nna ne suka kara sanya ni na yarda na
gane na kara hakuri na kara kyautatawa mijinam, ita
kuwa matarshi na maida ita tanfar yar uwa bani da
wata ita balle in je ina sha'awar zaluntarta,
musamman kuma da yake nafi kowa sanin mijin
nawa Dr. Ado Sulaiman zai yi min kawaici ya ji
kunyata ne ya kuma yi ta girmamani kan abin da
yaga ina yi na adalci, amma ba zai taba yarda da
zalunci ba.
Rannan da daddare muna hira da Inna a waya
saboda hirar tamu ta zama ka'ida yanzu kullum sai
mun yi, na ce mata ai dazu na fita Inna.
Tayi maza ta tambaye ni, ina ki ka je? Na ce
robar nan naje na cire, Inna tayi dariya ta ce kishi dai
ya motsa kenan, na ce ba kishi ba ne Inna, na dai gaji
ne kawai, ta ce ai shi din ne dai.

144

Na numfasa na co mata ni wanne yafi ne cikin
biyun nan Inna? Tunda ke su duka biyun kin san
yanda suke kin zo kin samu an kuma zo an same ki?
Tayi murmushyi ta ce, ni kam a wurina ai dace ne
kawai.
Tunda ita rayuwar gaba dayanta sa'a ne, na tuna
mata da kalaman Mama a da cewar da take yi
'ya'yanta ba za suje gidan kowa ba zuwa za'ayi á
same su, tayi dariya ta ce ba gashi ba, kuma da aka zo
aka same sun sai aka kore su
Saboia sun kasa yin hakuri? Na ce haka ne, ta ce
ai babu mai cin ribar rayuwa sai yayi hakuri, na sake
cewa haka ne.
Mama tayi ta zuba ido tana kasa kunne ko zata ji
wate rigima ta tashi tsakanina da Ado, shiru babu
wata matsala, saboda yona matukar jin kunyata da
ganin girmana a dalilin na yarda da shawarar da ya
bani na in dan yi mishi kawaici da kuma kara.
Sai kuma hankalinta yayi matukar tashi ta rinka
fadin maganganu wannan aure da aka yi ai ba aure ba
ne an kawo 'yar mutane an ajiye a gida ana cutar ta.
Rannan ina daga falona na ganta ta fito kan
keken guragunta, tana tura tayoyinshi da hannunta
kofar dakin amarya taie ta tsaya saboda ba za ta iya
tura shi yı shiga ba. Ni yarinyar nan ana baki abinci
kuwa?
Ban ji abinda BilkisD ta ce mata ba na dai ga

145

kawai ta gyada kai ta ce au to, ta juya ta tafi. Ban san
yanda aka yi ba, daga tsayuwar bakin kofa tayi
magana sai kuma abu ya dawo in ta zo bakin kofar ta
tsaya sia ta kira Balkin ta tura ta su shiga ciki.
Ni kam ko a jikina saboda da na gaya wa Inna
ma abin da Maman take yi dariya tayi ta ce ai babu
abu mai dadi a rayuwa irin ka rayu kana addini kana
kuma yarda da kaddara na ce haka ne Inna.
Rannan sai kawai aka yi kacibis tsakanin Mama
da Ado a dakin amarya, shi zai shiga ita kuma z ata
fito ina jin shi yana fadin a'a-a'a Mama, ai kin ji
sauki tunda ki ka iya fitowa daga dakin ki ki ka zo
har nan ai shi kenan magana ta kare.
Mama tayi maza ta ce, a'a wane sauki? In ban da
karfin hali don in zo in duba wannan yarinyar abincin
da ake bata ne nake ganin kamar ba ya isanta, ya ce
eh wannan duk ai alamar samun lafiyarki nce tunda
gashi har kina iya shiga harkar da ba taki ba ce.
Don haka sai ki shirya za ki koma dakinki,
Mama ta soma kuka tana bashi hakuri, ya ce a'a aiu
ba za ki kasa zaman lafiya a naki gidan ki zo nima ki
bata min nawa ba.
Dama kwanaki an kira ni a gidan su aka yi min
wasu maganganun da nayi zaton da hannunkii a ciki,
tun a lokacin na gaya wa Mallam Haruna cewar ni
ban saba da irin wadannan maganganun ba.
Ban iya yin irin wannan surutun ba na kuma

146
gayawa ita Balkin cewar in aka sake kirana a gidan
Su kan wasu maganganun da ban san da su ba zata
koma gidansu. To ashe kece Mama, don haka zan
kira Baba an jima in gaya mishi yasa ayi miki fentin
dakinki ga ki nan zuwa, ai ba rabuwa ku ka yi ba.
Na dai kyale ki a nan din ne kawai don na gane
ba kya son zaman can din amma ba zai zama dalilin
da kuma za ki nemi kulla min fitina a cikin iyalina
ba.
Mama tayi kuka har ta gaji ta bai wa Ado hakuri,
har taji babu dadi ya ce a'a Mama ki koma dakinki
kawai ita mace ai bata da wani wurin da ya fiye mata
dakin mijinta daraja in kina da matsala kawai ga
sabuwar waya nan na saya miki ki kira ni ki gaya
min, nima kullum zan rinka kiranki muna gaisawa.
A haka Ado ya kammala mata shiri ya kuma sani
wai ni da yara muyi mata rakiya na ce mishi to, muka
je muka kwana muka dawo. Sai bayan dawowan
nawa ne naji labarin wa duk wanda yazo sai ta gaya
mishi cewar ni nasa Ado ya kore ta.
Bayan kuma ita din ita ce tayi sanadin aurena da
shi, amma a yau na shiga tsakaninta da dan uwanta
na raba su.
Ni kam tunda nayi sa'a Mama ta yi wa dan
uwanta abinda ya tattara ta ya maida ita inda dama
mazauninta yake, sai naji sakat na samu sa' ida, na
gane ashe ba kishiya ce ma babbar matsalata ba, ta

147

rayuwa Mamace to na rabu da ita shi kenan zance ya
kare.
Chapter 22 · 0% Book details